Bayan Mako Biyu
"Har yanzu na gaza ganin dacewar haɗuwar ku ke da Nasir Nasar. Ina tunanin kamar kina ɓata lokacinki ne kamar yadda yake ɓata nasa a kanki." Maganar Adda Halima ta ratsa kunnuwanta a lokacin da take zoza powder a fuskarta.
Bata juyo daga shafa powder da take ba, asalima sai jambaki da shiga zagaye tsukekken bakinta da shi. Tana haɗe bakin nata da kuma wataya ƙananun idonta a kan faffaɗan madubin da ya ke hasko mata fuskarta.
"Duk yadda zaki fante fuskarki da kuma murza launi a bakinki, ba zai ɓoye shekarun. . .