Skip to content
Part 25 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

Bayan Mako Biyu

“Har yanzu na gaza ganin dacewar haɗuwar ku ke da Nasir Nasar. Ina tunanin kamar kina ɓata lokacinki ne kamar yadda yake ɓata nasa a kanki.” Maganar Adda Halima ta ratsa kunnuwanta a lokacin da take zoza powder a fuskarta.

Bata juyo daga shafa powder da take ba, asalima sai jambaki da shiga zagaye tsukekken bakinta da shi. Tana haɗe bakin nata da kuma wataya ƙananun idonta a kan faffaɗan madubin da ya ke hasko mata fuskarta.

“Duk yadda zaki fante fuskarki da kuma murza launi a bakinki, ba zai ɓoye shekarun da suka taru suka wuce a kanki ba, Hafsa. Abin haushi ne a ce duk wannan kina yinsa ne saboda yaron da bai fi ƙanin ƙanin bayanki ba.”

Sai a lokacin ta juyo da kallonta ga Adda Halima, ta kalleta ta kuma shimfiɗa shu’umin murmushin da ya zama ɗabi’a a gareta, murmushin da baya ɓacewa a kan fuskarta koda ace akwai ƙuna da zafi a cikin zuciyarta.

“Dacewata da Nasir Nasar Zayyar, wannan abu ne da idanuwana kaɗai suka iya ganin hakan. Bana jin gajiyayyun idanuwa irin naki da yake a rufe sa kuma rauni na tunanin ya zan tallafi rayuwata zai hango hakan.”

Murmushi ta ƙara shimfiɗawa a fuskarta a lokacin da take feshi jikinta da turarika masu ƙamshin sanyi kala-kala.

Tana ƙara kwantar da muryarta ga Adda Halima da ta tsaya kamar kafaffen dutsen da aka fidda ido a goshinsa.

“Ba zaki taɓa ganin dacewarsa a tare da ni ba Adda Halima. Domin kin manta yadda ƙawar rayuwa da jin daɗi take, an kuma kashe miki jin daɗin rayuwarki tun da ƙuruciyarki. A yanzu na tabbata kowa ganin yaro kike masa mutuƙar bai cimma shekaru tamanin a duniya ba. Kamar yadda dai mataccen mijinki ya ɗara shekarun mahaifinki a duniya.”

Daga haka ta raɓa ta gabanta har sai da ta kai bakin ƙofar ta dakata ba tare da ta juyo ba “Ki dai tunanin ni da Nasir bamu dace ba, domin dacewar abin da ya shiga tsakanin yanayi da halayya tawa da tashi. Muna yin abin da muke so ne a lokacin da muka so, ba tare da tunanin wani zai mana shamaki da shi ba.

Zan auri, Nasir Nasar Zayyar, koda hakan bai miki ba, koda hakan bai yiwa mutane da yawa daga cikin ahalina ba.”

Daga haka ta fice a ɗakin tana barinta da buɗaɗɗen ƙamshin turarenta da ya gama cika ƙofofin hancinta. A duk kalaman Hafsa babu wadda tafi riƙewa kamar wadda ta kira mijinta da sunan kira mijinta da mataccen da zarce shekarun mahaifinsu.

Hakan na nufin iskancin Hafsa zai koma har ga mutum da ya tsaya mata a dukkanin al’amuranta, mutumin da ya ɗauketa ɗaya daga cikin yaransa, ya sota fiye da ɗiyoyin cikinta.

Shiɗin kuma yanzu take aibata haɗuwarta da shi.

“Indai zaki ci gaba da tarawa da ɗebewa a kan maganar Anty Hafsa ba zaki taɓa samun abu mai daɗi a wajenta ba.”

Muryar Aadamu ta ratsa ta cikin dodon kunnuwanta, wadda hakan ya dawo da ita daga makahon tunanin da ta lula.

“Kowata rana kina ce mana Anty Hafsa ƴar uwarki ce da baki da kamarta. Amma a tare da ita muna iya ganin ke ɗin ba komai bace a wajenta face rigar da take sawa ta cire a duk sanda ta so.”

“Aadamu!” Sautin muryar Adda Haliman ya fita da amo wadda da alamu ta tattara ƴar guntuwar jarumtar ta ne.

Miƙewa ya yi a kan ƙafafuwansa “Ki yi haƙuri Umma. Amma gaskiya ɗaya ce a duk duniya. Anty Hafsa bata miki son da kike mata, bata baki girman da ya kamata ta baki a matsayinki na babbar yayar da kike riƙeta.”

“Fita ka bani waje.” Ta yi maganar da ɗan ƙarfi wadda ya tilasta masa jan ƙafafuwansa ya fice.

Wannan shine karo na ba a dadin da zata ce ta kori yaranta a kan sukan da suke a kan ƴar uwarta. Bata san me yasa har yanzu bata kallon abin da Hafsa ke mata a matsayin abu mai girman da zai iya zama aibu a gareta ba.

Tana zaune kamar bishiyar da aka shuka bata san lokaci ya ja ba, har sai da ta tsinkayi muryar Jiddah na cewa ta tashi zata musu shimfiɗa.

“Ƙarfe nawa yanzu?” Ta samu kanta da tamba.

“Goma da minti uku.” Jiddah ta bata amsa a lokacin da take warware ƙaton bargon da zata musu shimfiɗa.

“Har yanzu Hafsa bata dawo ba?” Ta sake jefa tambayar ga Jiddah wadda tana iya ganin yadda Jiddah ke taɓe bakinta.

“Kin manta ne sai sha ɗayan dare suke tashi a zancen.” Muryar Jiddah ta ankarar da ita wani babban kuskuren da ta sake yi a karo na biyu a rayuwarta.

“Sha ɗaya?” Ta ji maimaicin maganar na ƙwacewa a bakinta.

Wadda yasa Jiddah jinjina mata kai.

Miƙewa Adda Halima ta yi a kan ƙafafuwanta, tana zarga hijabin da ta gani a ƙofar ɗakin, babu wani tunani ta kutsa kanta zuwa waje, har gaban Motar da ta tabbatar da ta Nasir ce, tana iya hango hasken fitilar motar da ya gama haska mata fuskokinsu a lokacin da suke zance cike da walwala.

Bata ɗauka Nasir ɗin yana magana doguwa da fara’a haka ba, amma zata iya cewa tun da ta doshi wajen take hango fararen haƙoransa a ware. Tana ganin yadda zagayayyen bakinsa ke magana yana ƙara lumshe idanuwansa.

Wadda take ta tabbacin hakan na daga cikin jerin abubuwan da ya siffantu da su na yaudara.

Ƙwanƙwasa gilashin motar ta yi da hannunta wadda hakan ya ankarar da su zuwanta, wadda ba su tsammace shi ba.

Zuge gilashin motar ya yi da madannarsa yana zurma idanuwansa a na Adda Haliman da take sanya da wani cakuɗaɗɗen hijabi.

“Lafiya? Waye ba lafiya? Ko mutuwa  a ka yi na ganki haka wujuga-wujuga?”

Maganar Hafsat ta ratsa kunnenta a lokacin da take gaf da fesar mata nata tijarar.

Hakan yasa ta kalli jikinta tana duba yadda ta fita a sigar wujuga-wujuga da Hafsa ta faɗa ɗin. Sai dai a mamakinta tsaf take asalima akwai duhun da ba lallai idanuwa su fahimci a kwai shi ba.

Hakan yasa ta nisa tana jan zuciya da fasali “Ina tunanin ke ce kike gaf da mutuwar Hafsa. Kin san yanzu ƙarfe nawa kuwa?”

Bata bari ta bata amsa ba ta ci gaba da magana “Ƙarfe goma da ƴan kai, kina zaune a gaban mota kuna zancen da aka shefe awanni ana yinsa. Me za a faɗa na alkhairi da ba a faɗe shi a cikin awa ɗaya da ta wuce zuwa huɗun da suka shuɗe ba? Har sai kun mayar da idanuwan mutane kanku, an fara kafa mazaunai a zauruka ana yi da mu?

Wannan ita ce rana ta ƙarshe ta farko da zan miki, idan ba haka ba…”

“Idan ba haka ba zaki rufe ni da duka ne Umma Halima? Ko kuma zaki rufe min ƙofar shiga gidanki?” Hafsat ta datse maganar da take shirin yi da ɗorawa da ta ta maganar.

“Zan dai yi fiye da hakan.” Daga haka ta juya tana bar musu wajen. Zata iya jure komai a rayuwa amma banda abin da zai watsar mata da kimarta a wajen mutanen da suke kallon kowa watsattse ne.

Mutanen da take da tabbacin ko bacci suke idanuwansu ɗaya a buɗe yake, kamar yadda kunnesu ke buɗe da son jin abin da za su kafa majalissa da shi.

Bata shirya jin shewarsu da dariyar shaƙiyancinsu ba a kowata fitar da zata yi. Zai fi kyau ta tsayar da komai da kanta, koda ace kowa zai fahimci yadda take faɗi tashi da ƙarfi  da ya rage mata ba.

Bata kai ga ƙofar ɗakinta ba ta ji bankowar ƙofar gidan da kuma turata da ƙarfin da aka sake yi,  wadda yasa ta juyowa da sauri dan ganin wadda ya shigo gidan.

Hafsa ce take tafe kamar kububuwa dan ɓacin rai, kai kace zata bangaje gini ne.

“Ai ba sai kin fita kin min gargaɗi a gabansa ba zan tabbatar da cewar ina zaune ne a gidanki a kuma ƙarƙashin kulawar macen da take zaman kanta a gandu.

Da tun farko kin sanar da ni kina son Nasir Nasar da sai na bar miki shi. Amma ba wai kije gabansa kina min gargaɗi a kan hirar da muke da shi ba.

Ba yau nasan bakya son duk wani abun da ya zama na cigaba a gare ni ba, ba yau bane rana ta farko da nasan kina adawa da duk wani abu da zai zama mai kyau a gare ni ba.

Gara da kika fito min da asalin fuskarki wadda nake ta dakon son ganinta. Gara da..”

Maganarta ta dakata ne a lokacin da taji sauƙar mari a kuncinta, marin da ya haddasa ganin gilmawar haske a kan fuskarta.

Kafin kuma ta dawo a duniyar tunaninta taji sauƙar maganarta a karo na farko a rayuwarta da taji muryarta da zafi da kuma kauri “Tabbas ina adawa da duk wani abun da ya zama ɗabi’a ne naki. Ina adawa da yadda kika zama zakka a cikin danginmu.

Sai dai zuciyata bata rufe a kan wannan adawar ba, ta karɓe ki duk da kina da baƙin fantin da ya zama abin gudu a wajen kowa. Kowan da ya zama harda iyayen da suka zama silar zuwanku duniya. Kowan da ya zama harda ƴaƴan da kika zama uwa a gare su.

Son zuciyarki da son kanki ya raba ki da komai. Komai ɗin da kike tunƙahon kina da shi. Faɗa min a yanzu me kike da shi wadda zaki kalla kice naki ne da ke tare da ke? Karki ga na miki shiru ki ga damata. Kada kawaicin da nake miki yasa ki tsallake iyakar abin da na shimfiɗa miki a yau. Kada kuma ki ɗauke ni tamkar takalmin sawarki ne.”

Da sauri su Jiddah suka fito a ɗakinsu, jin yadda Ummansu ke faɗa, tana magana sa ƙarfi, wadda su kansu basu taɓa jin irin wannan faɗan ba, basu taɓa ganin ɓacin ranta ba kamar yadda suke gani a yau ɗin.

Hannunta ta fara tafawa tana ƙoƙarin kawar da duk wani zugi da zafin maganar da Adda Halima ta jefa mata, ciki hadda zazzafan marin data watsa mata.

“Da kyau Adda Halima. Ai ban san motsin haukan naki na nan ba. Indai kina ta magana ne a kan Nasir to ko zaki mutu, ko zaki mutu sau ba adadi sai na aure shi.”

Taci gaba da faɗar magana son ranta wadda ko ci kanki Adda Haliman bata ƙara ce mata ba, sai dai tana da tabbacin a daren yau ɗin ba ita kaɗai bace bata rintsa ba, hatta maƙotanta tana da tabbacin fitinar Hafsa bata barsu sun yi baccin ranar mai kyau ba.

Har zuwa wayewar gari tana ci gaba da ƙananun magana da aibata Adda Halima wadda hakan ya tunzura Adda Halima musamman ganin yadda maƙota suka fara taruwa suna tambayarsu dalili.

Zata iya cewa wannan shine karo na huɗu da maƙota ke shigowa akan matsalarta da Hafsa.

Bata bi ta kan kowa ba ta shige Ɗakin Hafsa ta fara fito mata da kayanta tana mata watsi da su ƙofar gida.

Jikinta rawa yake tana jin zuciyarta ta kai mataki na ƙarshe a zamanta da Hafsa “Wallahi yau koda gwara muka yi muka faɗo ciki ɗaya sai kin bar min gidana.

Haƙurina ya kai maƙura ki zo ki fita min a gida da rayuwata.”

“Babu inda za ni, inda kika fita da kayan nan haka zaki dawo kin da shi.”

Hafsa ta faɗa tana tsallake kayan da shigewa gidan maƙotan da ke kallo gidan Adda Halima.

Wadda hakan yasa Adda Halima rugawa kamar mahaukaci ta finciko Hafsa tana janta, kafin ta fizge ta shige gida.

Sake durba Adda Halima ta yi a tsakiyar layin nasu ta fara ihu tana kuka, daga nan ta nausa gidan Maman Walid da take da tabbacin zata samu taimakonta dana maƙociyarta Umman Khadija. …

*****

Lallai abin da ya koro ɓera daga rami ya faɗa wuta yafi wutar zafi.

Hhhh rai fess nasan wasu…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Jini Ya Tsaga 24Jini Ya Tsaga 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×