"Ba zan iya ci gaba da zama da Hafsa ba Maman Walid. Zuciyata ta gaza jurewa, da kowata bugawar zuciyata tsoro da fargaba ke tunkarar zuciyata.
Ina jin tsoron kalar fitinar da zata iya ratsowa daga bakinta, ina jin tsoron mitar da ta ke sauƙewa a kaina da kuma ƙananun maganarta waɗanda basa ƙarewa. Na gaji, na gaji fiye da yadda kalmar ke fitowa a cikin bakina." Adda Halima ta faɗa a lokacin da ta ke fuskantar Maman Walid ɗin.
Tun shigowarta gidan a firgice da yadda take nanata kalmar Hafsa ta zame mata fitina da kuma. . .