Skip to content
Part 26 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

“Ba zan iya ci gaba da zama da Hafsa ba Maman Walid. Zuciyata ta gaza jurewa, da kowata bugawar zuciyata tsoro da fargaba ke tunkarar zuciyata.

Ina jin tsoron kalar fitinar da zata iya ratsowa daga bakinta, ina jin tsoron mitar da ta ke sauƙewa a kaina da kuma ƙananun maganarta waɗanda basa ƙarewa. Na gaji, na gaji fiye da yadda kalmar ke fitowa a cikin bakina.” Adda Halima ta faɗa a lokacin da ta ke fuskantar Maman Walid ɗin.

Tun shigowarta gidan a firgice da yadda take nanata kalmar Hafsa ta zame mata fitina da kuma gansheƙar kukan da take, Maman Walid bata dakatar da ita ba har zuwa lokacin da ta gama sauƙe duk wani abu da ke zuciyarta.

“Yanzu Halima duk da sanin wace ce Hafsa, da kuka gargaɗinki da ƴan uwanki suke a kanta. Amma kika toshe kunnenki kika barta a tare da ke?”

Tambayar da ta yi tasan ba zata samu amsa ba, hakan yasa ta miƙe tsaye a kan ƙafafuwanta tana yafa ƙaton mayafinta kasancewarta babbar mace mai yalwar jiki, wadda kuma haƙurinta ke da ƙaranci. Kusan zan iya cewa a duk cikin unguwar babu mace mai jikinta da kuma fusatacciyar zuciya wadda tasa a ke shakkarta.

“Tashi muje.” Ta faɗa a ba tare da ta sake bi ta kan Haliman ba ta fice tana barin Zahra ɗiyarta akan ta kammala aikin tuwon siyarwar da take yi.

Tana fitowa taga mata sun cika ƙofat gidan Haliman hayaniya nata tashi wadda bata fahimtar me ake faɗa, a kuma lokacin ne Umman Khadija itama ta fito daga gidanta tana gaida Maman Walid ɗin, da tambayar abin da ke faruwa.

“Sakarcin Halima ne ke shirin kaita gadon asibiti. Gata nan ta ɗebowa kanta masifa tana zaman zamanta.”

Juyo da kallonta ta yi ga Haliman da zuwa yanzu ta yi zuru-zuru, idanuwanta sun zurma idanuwanta sun shiga ciki, sai kuma bakinta da ya bushe kamar yadda wasu hawaye suke kwance a fiskarta da suka gama bushewa.

“Iya Haly kin kwanta ciwo ne ban sani ba?” Sautin maganar Umman Khadija ta fita a hankali cike da tausayawa.

Iya Haly wani suna ne da su matasan matan unguwar suke faɗa mata, da sunan mata alkunya da sunan ƴan gayu.

“Fiye da jinya dai ta yi Umman Khadija. Dan tana gaf da faɗawa rami a kan abin da ta siyowa kanta. Kin ganta nan ciwon ƙirji take fama da shi  sanadin masifar ƙanwarta. Bari dai na ƙarasa naji abin da waɗancan ƴan koren suke faɗa.” Umman Walid ta faɗa tana ƙara takunta da jujjuya musu gaɓɓar jikinta da yake a ƙoshe.

“Ban gane ba Iya Haly?” Bata da zaɓi bayan faɗa mata halin da take ciki.

Ji ta yi maganar ta zo mata kamar sauƙar guduma a kanta “Hafsa fa! Hafsanki, maman Bunayya! Ita ce duk ta yi waɗannan abubuwan iya Haly? Hafsa da alkhairinta da haba-habanta ke ratsa kowanne mutumin da ke unguwar nan.”

“Hafsa ta wuce da sanin mu Umman Khadija. Idan nace zan faɗi komai da ke gareta na halayyarta ina mai tabbatar miki da zan cika ƙaton littafin da za a shekara ana rubuta shi.”

“Kuma duk da kin koreta amma ta ce bazata tafi ba?”

“Haka tace Umman Khadija.”

“Wannan ƙarya ne kuma. Ba zai iyu ke da gidanki amma tace bazata fita ba, idan har ba dama ta zo ne dan ta ƙarasa kashe ki ba.”

Ƙofar gidanta ta janyo ta datse da mukulli ta tafi, saboda yaranta duk sun tafi islamiyya.

“Mu je.” Ta faɗa tana harba ƙafarta zuwa ƙofar gidan Adda Haliman da ke cike taf da mutane.

Wani abu ne da zaka iya ɗaukan biki ake ko kuma dai wata ƙwarya ƙwaryar taro, domin manya da yara ne mata da yaransu ke ƙofar gidan kayan Hafsa da ke watse har a lokacin a ƙofar gida tana ƙoƙarin ɗaukansa da shigar da su cikin gidan Adda Haliman. Tana nanata kalmar ba zata tafi ta bar gidan ba.

Basu san da zuwan Adda Haliman ba sai ganin tsallenta da suka yi ta dira gaban Hafsa ta fixge jakar hannunta da wulli da ita zuwa baya.

“Wallahi koda kina yawo da Ɗan zagi a bayanki, ina tabbatar miki da cewar ba zaki koma gidana ba Hafsa. Kin gama zama a gidana har abada.” Ta yi maganar da wata irin buɗaɗɗiyar murya idanuwanta na tsaye ƙam a kan Hafsa kamar za su yi tsalle su faɗo ƙasa.

Murmushi Hafsa ta yi wadda har sautin sa ya fita “Lallai kuwa zaki yi kaffara.” Ta faɗa tana ƙoƙarin tureta.

Sai dai ga mamakinta ta ji an ruƙota zuwa baya, wadda hakan yasa ta juyo a fusace. Umman Walid ta gani idanuwanta fiƙe a kanta, kamar yadda take ɗauke da haɗaɗiyar fuskar da zaka iya cewa bata taɓa dariya ba a rayuwarta.

“Wannan al’amarin ya kamata ya tsaya a haka nan Hafsa. Tun da har a yau Halima ta yi rantsuwa ta kuma fito bainar jama’a tana cewa ba zaki zauna a gidanta ba, hakan na nufin haƙurinta ya kai ƙarshe.

Duka nan mutane ne da suka kasance maƙotan Halima, ba a taɓa jin sautin muryarta a sama ba tun bayan zuwanta, bata da abokin faɗa kowa nata ne. Idan har zata iya haƙuri da mutanen da bata haɗa jini da su ba tsawon shekara ɗaya, ya za a jiku ke da ita a abin da bai wuce watanni biyar ba kacal? Hakan na nufin kina da sababbiyar ɗabi’a da ke cutar da ita.

Dan haka ki tattara ki ta fi.”

“A matsayinki na wa kike yanke hukunci a kan abin da ya shafe ni nida ƴar uwata? Wadda  JININ MU YA TSAGA FATAR MU TA CIZA!”

“Tabbas jininku ya tsaga Hafsa. Amma kuma baki da gado ko ɗaya a gidanta.” Cewar Umman Khadija da ta ratsa a wajen.

Kafin kuma wani lokaci hayaniyar mutanen unguwar ta fara ƙaruwa wadda da yawa suna magana ne a kan Hafsa ta tafi tabar gidan Adda Haliman.

Dariya Hafsa ta yi tana kallon mutanen da bakinsu ko kaɗan bai saɓa ba, hakan yasa ta jinjina kanta tana haɗe hannayensu a jikinta, kafin ta ɗaga musu hannu “Ku yanzu duk kun yarda da abin da Adda Halima ta faɗa?

Matar da take da jirkiɗaɗɗiyar ƙwaƙwalwa wadda bata da ishasshen lafiya? A yanayin yadda take a haka ya isa ya tabbatar muku cewar akwai motsi a kanta.”

Hayaniyar mutanen ta ƙara tashi wadda yasa Adda Halima kasaƙe tana kallon Hafsa, yau ita Halima Hafsa ke cewa tana da jirkiɗaɗɗiyar ƙwaƙwalwa a bainar nasi, a gaban dubbanin mutane. Bata san lokacin da hawaye ya yi tsalle ya gangaro a fuskarta ba, sai dai ta ji lokacin da ɗuminsa ya sauƙa a kan fatar ta.

“Kun ji ko? Kun ji ba? Hafsa kashe ni take son yi.”

“Ki yi haƙuri Adda Halima ba zan ƙara tanka kalmarki ko ɗaya ba.” Hafsa ta faɗa da jirkitattun idanuwanta hawaye na gangarowa a idanuwanta.

“Idan kika kore ni ban san ina zani ba. Ke kaɗai ce ƴar uwata da take ƙaunata, dan Allah ki yi haƙuri Adda Halima.” Ta yi maganar hawayen na silalowa a idanuwanta, tana girgiza da gunjin kuka wadda ya sa jikin mutane ƙara yin sanyi. Umman Walidi da ta zo a tafashe sai taji ƙafafuwata sun sage, tana tunanin idan har ta sanya hannu Halima ta kori ƙanwarta kamar bata yiwa rayuwa adalci ba. Sai dai kuma wani adalcin rayuwa ne ya rage tsakaninta da Haliman da ta gama kawo mata kukanta a kan ƴar uwarta a ɗan abin da bai wuce mintuna talatin ba.

Runtse ido Adda Haliman ta yi tana jin hawayen Hafsa na tasirantuwa da tsargar mata da wani abu a jikinta, wani abu mai zafi da raunin da bata san wanne iri bane. Jini ba ƙarya ba, duk inda za a zo a dawo dai Hafsa jininta ce da bata da kamarta. Bata taɓa ganin kukanta haka ba, kamar yadda bata taɓa ganin tashin hankalinta kamar wannan ba.

Kallon mutanen wajen ta yi da idanuwansu ke sauƙa a kan fuskarta da wani irin abu da basu san wane iri ba ne, amma zata iya cewa kallon tausayi ne da kuma jimami da suke musu shi.

“Ki yi haƙuri Halima. A rayuwa naka sai naka, duk inda Hafsa zata je ta dawo dole dai ita ɗin jinin ki ne. Ke ce mutum ta farko da kika san wacece ita.” Muryar Aa’i ta ratsa tsakanin shurun da wajen ya yi da kuma sautin kukan Hafsa.

Wadda hakan kamar ta buɗe ƙofar maganar mutanen ne suka fara bata haƙuri a kan abin da ya shiga tsakaninta da Hafsa, ya yin da suke ganin hakan a matsayin wani saɓani na zama da ya haɗa su a yau ɗin.

“Harshe da haƙori ma ana saɓawa Halima, ki ƙara mata uzuri da haƙuri. Babba juji ne da yake iya ɗaukan duk wani abun wuya da wahala daga na ƙasa da shi.” Muryar Usaina maƙociyarta ta kusa ta ƙara tasirantuwa zuwa kunnenta sai dai kalmar

_’Babba Jujin’_ Da ta yi amfani da shi kamar ya shafe kowata kalma da ta ji a baya. A hankali duk mutanen suke bata haƙuri a kan ta jure.
  Ta riga data gama sanin cewar kalmar ‘Haƙuri’ bata zuwa har sai an cutar da kai. Ta kuma amince da cewar zaman Hafsa da ita kamar buɗewar wata sabuwar ƙaddara ne a gareta. Ƙaddar da bata san yaushe ne zata ɓace daga gareta ba, kamar yadda bata san yaushe ne zata rabu da ita ɗin ba.

Tana gani mutanen suka shigar da Hafsa cikin gidanta da kayanta, suna kuma ƙara bata haƙuri a karo na ba adadi, amma ita ba wannan take gani ba, murmushin da Hafsa ta mata da kuma rungumetan da ta yi ne ta ƙara cakuɗa duk wani tunaninta, ya kuma sage mata gwuiwoyinta….

*****

Ban san me zaku ce da Adda Halima a yanzu ba, amma ina roƙonku da a ƙarfafa mata gwuiwa 😄😄😄

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Jini Ya Tsaga 25Jini Ya Tsaga 27 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×