Skip to content
Part 27 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

Ta daɗe tana jiran jin wani ya zo ya tasheta daga mummunan baccin da take mai ɗauke da munnan mafarkai. Sai dai bata ga ta yadda abin da ya faru yake kama da mafarkin ba. Domin iskar da ke busawa a jikinta da kuma bushewar da maƙoshinta ya yi shi kaɗai ya isa ya tabbatar mata da cewar ba wai bacci ne take ba.

Jingina ta yi a jikin zauren da yake nata, tana jin sautin muryoyin mutanen na ƙara bata haƙuri suna dannarta “Ki ƙara haƙuri Halima. Mu zamu tafi, idan akwai wani abu daga baya ki sanar da mu dan yiwa tufkar hanci.” Umman Walid ta faɗa tana juya.

_’Tufkar hanci!’_ Maganar ta ƙara ratsawa a kunnen Adda Halima kamar da aka ware maganar ana maimaita mata ita. Shin akwai wata tufkar da ta rage da za a samar mata da hanci bayan zaman Hafsa a gidan ta? Bata jin akwai ta gaskiya, sai dai ba zata musa da kalmar su da maganar su ba, hakan yasa ta gyaɗa kanta kamar ƙadangare, kafin kalma ɗaya ta suɓuto daga bakinta, kalmar da sai da ta ratsa mikin ciwon da ke maƙoshinta kafin ta fito.

“Na gode.” Daga haka ta juya tana jan ƙafarta da shigewa gidanta.

_’Ba zaki iya da Hafsa ba Halima. Hafsa fitina ce duk inda ta je sai ta yaɗa sharrinta.’_ Sautin muryar Yaya Ado ta ratsa kunnenta tana tunatar da ita Annobar da ke zaune a tare da ita.

Ƙafafuwanta ne suka sage a lokacin da take gaf da shiga cikin gidan, ganin Hafsa zaune tana dama kunun Ayarta hankalinta kwance kamar ba wani abu da ya faru.

Ƙara yawata idonta ta yi, ta hango Ummi kwance a kan tabarma a cikin rumfa gidan ta mata shimfiɗa da zaninta. Tsakar gidan tsaf a share kamar yadda rumfar take a share, wadda take da tabbacin Hafsa ce ta yi sharar.

“Ki shigo mana Adda Halima, kin tsaya kina ganina kamar sabuwar halitta a gabanki.” Bakinta ta ɗan taɓe tana tauna laɓɓanta.

“Hafizu ne ya kirana yana cewa ana neman kunun aya a gidan ƙanƙararsu. Kin san yau rana ta buɗe shi yasa na fara ɗaurawa.”

Ba wannan Adda Halima take da buƙatar ji ba, a yaushe ne har aka kaiwa Hafsa niƙan ayar aka kawo mata ana hayaniyar nan?

“Zo ki sha kunun Aya mai zaƙi wataƙila zuciyarki ta risina ta huce Addana!” Ta yi maganar tana kamfato kofi da ɗebo mata kunun ayar, tana murmushi da karya kanta.
Ta daɗe da sanin Hafsa ba zata sauya ba, shi yasa ta ɗaga ƙafafuwanta ta shige ɗakinta.

“Ba na kawo miki har ɗaki Addana!” Sautin muryarta na fita raɗau kamar yadda sunan Addanah ke amsa amo a kunnen Adda Haliman.

Kafin ta kintaci abin da zata yi sai ganin Hafsa ta yi shaƙe da kunun Aya a kofin silbar su.

Ta ajiye a gabanta tana ƙara kwantar da kanta “Ki sha ki danni zuciyarki, ki ƙara haƙuri a kaina. Idan kika kore ni ban san ina zani ba, kuma ina da tabbacin ba zaki so ki ganni ina yawon bariki ba. A taƙaice ni ba ni da ɗabi’ar watsattsun da ba su watse a gida ba sai bayan auren su.

Ki yi haƙuri na yi aure na ɗan lokaci, bayan nan zan barki ki sha iska fiye da yadda kike tunani.”

Daga haka ta miƙe ta tashi a kan ƙafafunta “Abin da ya faru a daren jiya zaɓinki ne Adda. Amma zaki iya gujewa sake faruwarsa a karo na biyu.” Daga haka ta ɗaga labilen da zummar barin ɗakin.

“Zo ki ɗauki abin ki bana buƙatar sa. Kin ce ke ba watsattsiya ba ce, amma ina tabbatar miki da cewar watsewar da kika yi har ta fi ta gantalallun da suke siyar da abin su a titi. Domin wataƙila su basu katange kansu da ƙirƙirar sharri ga wadda ya basu alkhairi ba. Wataƙila kuma basu yi nesa da gida dan muradin zuciyarsu ba. Wataƙila kuma basu yada yaransu na halak sun kasa bibiyarsu na, wataƙila ƙaddara ce ta sa suka yi nesa da duk wasu abubuwa ba dan suna so ba.

Nasha ji ana cewa mata dangin sheɗan ne, amma ni yanzu na tabbata ke uwa da uban sheɗan ce Hafsa, sharrinki ya wuce na danginsa sai dai uwar da ta haife shi. Zan ci gaba da neman tsarin Allah daga sharrin ki.”

Juyowa Hafsa ta yi ta kalli Adda Halima kamar yadda itama take kallonta, hakan yasa murmushi ya suɓuce a bakin Hafsa, murmushin da har sai da jerarrun haƙoranta suka fito, idonta ya rufe.

“Na ji daɗi da kika fahimci haka a tare da ni. Bana da ja a duk maganarki. Idan Hafsa ta yi kyauta bata dawowa ta ce a bata, wannan ne kawai kika manta. Dan haka zaɓin ki ne ki sha ko ki zubar ko ki barwa marayun yaranki.” Daga haka ta fice ta bar ɗakin tana rera waƙarta ta Baba mai gyaɗa agege.
    _Halin ‘yan duniya nake so_
      _in kwatanta, Sun fi ƙaunar
        _Attajiri fa ba marar kwabo ba,_
       _Idan baka da dukiya a yau an_
        _Rainaka. Kai yaro ta shi nema._
     _Tashi nema kafin dare ya Ƙurema_
Daga nan kuma sai ta saki waƙar ta ƙara ɗauko ta Hajiya Barmana choge:
      _Mai soso ka wanka._
      _Duk wanda bata da shi sai ta ara_
      _Ga lale-lale maraba da ke_
      _Attajira._

Daga nan sai ta bushe da dariya “Ho ni Hafsatu Attajira.” Ta sake faɗa da sauti mai amo.

Girgiza kai kawai Adda Halima ta yi tana nema mata shiriya, ta riga data san ba zata sauya.

Yinin ranar dai kusan Hafsa ce ke sha’aninta a gidan dan ko ƙofar gida bata fita ba, ƙarshe data gaji da zaga tsakar gidan bayan ta gama musu girki, ta dawo ɗakin Adda Haliman ta zauna ta sata a gaba tana kallon ta.

“Baki ci abinci ba har yanzu Adda Halima.” Hafsa ta faɗa da murya mai rauni kamar xata yi kuka.

“Bana buƙatarsa ne.” Ta bata amsar a taƙaice, tana kan abin sallarta tana azkar.

“To ai shikenan na dai riga nasan ciki ba ƙanin uwa ba ne. Idan ya gaji da kansa zai nemawa kansa abin da zai shiga cikinsa. Ba na kwanta na huta.”

Daga haka ta kwanta a ledar ɗakin tana sauƙe numfashi da kumshe idanuwanta “Yanzu na dai riga nasan matsalar duk a kan Nasir Nasar ce da bakya so ko Adda Halima? To na yanke hukunci akan zan dakatar da maganar aurensa har zuwa lokacin da zaki ji kina son sa. Idan kuma baki ji ba ɗin zan barwa lokaci naga abin da zai biyo baya a cikinsa. Wataƙila na samu wadda ya fishi alkhairi a gaba.”

Ta yi maganar tana kwantar da muryarta ƙasa, sai dai ga mamakinta har a lokacin Adda Haliman bata tanka mata ba.

“Duk da nace zan rabu da Nasir amma nasan ba zaki taɓa yarda da ni ba.” Ta yi maganar tana buɗe feƙaƙƙun idanuwanta.

Murmushi Adda Haliman ta yi, tana girgiza kan ta “Rayuwarki taki ce Hafsa. Babu wadda zai miki shamaki da ita, kina da zaɓi da damar yin abin da kike so a sanda kike so a kuma lokacin da kika so.

Ni kawai yayarki ce amma ban isa na shiga hurumin abin da zuciyarki ke so ba. Ina fatan duk wadda zaki aura ya zama sila na daidaituwar al’amuranki.”

“Al’amurana!” Ta ja maganar kamar mai neman wani abu a tare da ita.

Shafa tafukan hannunta ta yi a kan fuskarta kafin ta juyo ta fuskanci Hafsa tana jingina da bangon ɗakin.

“Ina fatan hakan Hafsa.” Ta ƙara nanata fatan nata a kan nata. 

Sai dai a wannan lokacin ba ita take gani ba, sai dai tunaninta da ya wullata a wata duniyar.

Sallamar da aka rangaɗa da amo da sautin muryar yaran Adda Haliman da suke ihu suna kiran Umman Boɗinga shine abin da ya tarwatsa tunanin Hafsa ta neme su ta rasa a wasu lokutan, fatan hasashen Umman su ta musu dirar mikiya a saɓaɓɓen lokacin da bata gama fahimtar maganar Adda Halima ba, bata kuma da tabbacin ko ta huce ne a kan abin da ta mata a daren jiya da kuma yau ɗin.

“Kai kai ku saketa kar ku kada min Uwa.” Sautin maganar Adda Haliman da yake fita tar cike da annashuwa da jin daɗi, ya ƙara sagar da gwuiwarta.

“UWA!”_ Maganar ta ƙara fita a kunnenta. Shin ita yaushe ma rabon da su gaisa da Umman balle ta tabbatar da muhimmancin sunan Uwar da take amsawa nata.

“Shigo Umma.” Adda Halima ta faɗa tana ƙara faɗaɗa murmushin fuskarta, sai dai tana jin Muryar Umma na ratsa kunnenta cike da Nagarta da kamalar da take da ita “Halimatu kuna nan abin ku cike da jin daɗi. Ai na jima da zuwa ina tare da Umman Walid da Maman Khadija, baki ga yadda suka amshe ni ba, kai kin yi dacen maƙota na …”

Maganarta ta dakata a lokacin da idanuwanta suka washe suka sauƙa a kan fuskar Hafsa, fara’ar fuskarta ta ɗauke cak tana kallon Haliman da Hafsa.

“Halima me nake ganin a nan? Har yanzu Hafsa na gidan ki baki koreta ba?” Muryar mahaifiyarta ta dira tsaf a kanta tana jin kamar an kwaɗa mata guduma ne a kan nata, kuma kamar an tarwatsa mata wani fatan da ta daɗe tana yi, fatan tabbatuwar farin ciki a rayuwarta…

<< Jini Ya Tsaga 26Jini Ya Tsaga 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×