Ta daɗe tana jiran jin wani ya zo ya tasheta daga mummunan baccin da take mai ɗauke da munnan mafarkai. Sai dai bata ga ta yadda abin da ya faru yake kama da mafarkin ba. Domin iskar da ke busawa a jikinta da kuma bushewar da maƙoshinta ya yi shi kaɗai ya isa ya tabbatar mata da cewar ba wai bacci ne take ba.
Jingina ta yi a jikin zauren da yake nata, tana jin sautin muryoyin mutanen na ƙara bata haƙuri suna dannarta "Ki ƙara haƙuri Halima. Mu zamu tafi, idan akwai wani abu. . .