Idanuwanta ba su buɗe ba har sai da hasken rana ya hudo ta windon da ke ɗakin ya haske idanuwanta.
Ta fara buɗe idanuwanta da take jin nauyinsu da kuma gajiyawar da suka yi. Daga kwancen da take tana iya auna adadin kassarewar da gaɓɓoɓin jikinta suka yi da mafi wahalar kasala da kuma gajiya. Ƙasanta kuwa kamar an baɗa mata barkono an bishi da attaruhu an zazzaga mata.
Yunƙurin tashi take ganin agogon bango na biga ƙararrawar ƙarfe tara na safiya. 'Wata irin lalacewa haka na yi? Wadda ko a daren aurena na. . .