Skip to content
Part 35 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

“Hafsa, ki zo ki buɗe ni. Idan kika bari na fito sai na ɓaɓɓallaki gida-gida yadda ba zaki samu mai ɗoraki ba.” Nasir Nasar ya yi maganar yana dukan ƙofar da ƙarfin gaske.

Dariya ta yi mai sauti, jin wai NasiR Nasar ɗin ne zai ɓalle ƙofa, ko da wani jikin, abu kamar sandar raken da aka fire.

“Fatan alkhairi jarumi.” Ta yi maganar tana zuba abinci a filet wadda tuni ƙamshinsa ya cika hancinta.

Ai tuni ta sambaɗe abincin tana korawa da haɗɗen ruwan inibin da aka haɗa shi, ita kam mamakinta a bayyane yake, ta yadda matar Nasir ta iya haɗa wannan haɗaɗɗen abincin.

Idonta ta ƙara lumshewa tana zuba abincin, tana sake ci, sai da ta ji cikinta na barazanar fashewa sannan ta miƙe.

Har a lokacin Nasir na dukan ƙofar, ta matsa jikin ƙofar da murya mai sanyi ta fara magana “Allah ya huci zuciyar mazan fama. Zan je na gaida yayata, idan na dawo sai mu ɗora daga inda muka tsaya.”

“Ki buɗe ni Hafsa.” Ya yi maganar da hargagi. Wadda inda ace wata ce ba Hafsa ba babu abin da zai hana zuciyarta tsinkewa.

“Wai nikam Nasir anya ba wani abin ka sha ba kuwa? Dan ban taɓa ganin jaraba irin taka ba, har yanzu kana hargagi a kan na buɗe ka min yaga-yaga, Allah kaɗai yasan adadin matan da ka farke.” Ta yi maganar tana buga ƙofar da hannunta.

Shikam ji ya yi zuciyarsa kamar ta ƙone dan takaici, yana jin ina ma ta zama hanman ko super man ta yadda zai yi filla filla da ƙofar.

“Ka kwantar da hankalinka Angon Hafsa, da na dawo zan zo na kwantar da jarabarka. Amma kafin nan ka ji daɗin raƙashewa da abin da ka kwankwaɗa.”

Daga haka ta juya ta fice, tana jin sautin ƙaran buga abu, wadda tasan wani abun ya fasa. Bata damu ba, dan ta riga da ta shirya kowanne irin zama ne da zata yi, kamar yadda ba zata taɓa lamunta ya kasheta da ranta ba.

A wayonta da gogewarta a duniya, ta san babu wani bahaushen namijin da zai yi wannan jarabar, domin bai haɗa jinsi da ayu ba balle tasa ran dauwama a haɗe.

Ita kam ai taga dalala. Ƙoƙarin daurewa ta yi da daidaita tafiyarta gudun kada mutane sun ankare da ita.

Cikin sa’a ta samu harabar gidan ba mutane sai ma’aikatan da suke ta faman kaiwa da kawowa, ta kuma riga da tasan sashen Zahra Zakar Dabo bata buƙatar wani ya mata rakiya.

Da sallama ta shiga cikin madaidaicin palon nata, wadda take da tabbacin nata ya fi wannan girma nesa ba kusa ba.

Sai dai duk da haka sai taga wannan ɗin yafi nata tsaruwa, wataƙila saboda kular da ya samu daga mamallakinsa, da kuma ƙawata shin da aka yi da gyara.

Ƙamshin da ta ji ya shigeta har tsakiyar jikinta, tana girmama matar, a ranta taji koba komai ta san me take, tun da har ta iya gyara sashenta haka.

Sallamar ta sake yi da ɗan ƙarfi a karo na biyu, ta ji an amsa mata daga cikin wani ɗakin. Tana tsaye har a lokacin tana wurga idanuwanta da kallon ko ina na falon.

“Maraba lale da Amaryarmu.” Sautin muryar da ta ji daga gefenta yasa ta juyo, tana hango matar na tattakowa da shigar atamfa ɗinkin doguwar riga, fuskarta fayau babu kwalliya saɓanin jiya.

“Bismilla ki zauna mana kike tsaye.” Ta safe yin maganar har a lokacin fuskarta da faffaɗan murmushi.

Wadda Hafsa ta lura murmushin daga zuciyarta yake, kamar yadda take da tabbacin ɗabi’arta ne yin sa.

Zama ta yi a kan kujerar tana fuskantar Zahra da ƙara murmushi a kan fuskarta “Na gode.” Ta faɗa bayan ta daidaita zamanta.

“Ban yi tunanin zaki samu fitowa da wuri haka ba, da na haɗa miki wani abin motsa bakin.”

“Wadda aka kai mana ma mun gode ƙwarai da gaske.”

Ta bata amsa da murmushi a kan fuskarta.

Miƙewa Zahra ta yi tana nufar fridge da ke falon ta ɗauko ruwan faro da lemon fanta na jarka.

Ta haɗo da kofi ta ƙaraso tana ajiye mata a gabanta kan wani ɗan madaidaicin table dake wajen. Ƙoƙarin zuba mata take Hafsa ta dakatar da ita.  

“Bana tare da ƙishi a yanzu. Zan sha kafin na tafi, idan sanyin sa ya ragu.”

Hakan yasa ta Zahra ta koma ta zauna tana ƙara fuskantar Hafsa, da tun shigowarta take jin gabanta na harbawa da ganinta, duk da bata ga wani abu a tare da ita na ƙi ba.

Amma tana da yaƙinin ita ce matar farko da Nasir ya auro data ziyarceta a ranarta ta farko, kamar yadda ita ce babbar macen da ta shigo cikin rayuwar aurensu.

Taga mata da yawa, ta kuma ga kalolinsu, sai dai duk a cikinsu basa kwashewa da daɗi, wasu sukan bar miki ga yaranta, wasu kuma su bar tabo ga zuciyarta da jikinta.

Ta sani babu wata jarrabawa a rayuwa da za a mata wadda ta zarta ta auren Nasir da ta yi, babbar jarabawar kuma shine yaranta da take tausayawa idan babu su ɗin.

“Kina tunani ne a kaina da irin zaman da za mu yi tare da ke?” Maganar Hafsa ta ratsa dodon kunnenta tana kuma kawar da shurun da ya ratsa tsakanin su.

Ɗago kai Zahra ta yi ta kalli Hafsa tana ƙaƙalo murmushin yaƙe “A’a ina mamakin yadda amarya ta fito ta bar ango ne.” Ta yi maganar da sigar tsokana wadda Hafsa ta yi murmushi tana jinjina hikimar irin ta zahra.

“Na zo ne dan na gaida ki, na kuma baki girma a matsayinki na uwargidan kuma yayata, duk da ina da yaƙinin ba zaki zarta ni a shekaru ba.” Ta ƙare maganar tana murmusawa wadda hakan yasa Zahra murmushi ita ma.

“Haka ne kam. Na gode sosai.” Zahra ta faɗa tana murmushi.

Gyara zama Hafsa ta yi tana buɗe lemon da ke gabanta ta zuba a kofi.

“Ban zo dan na zama kishiya a wajen ki ba Zahra. Asalima na zo ne dan na zama ‘yar uwa a gareki, na kuma zama inuwa ga yaranki.” Ta yi maganar tana kurɓan lemon a bakinta.

Ya yin da mamakinta ya hana Zahra yin shiru “Ban fahimci maganarki ba.”

Sai da ta sha lemon sannan ta kalli Zahran a karo na ba adadi, ta kuma ƙara murmushi.

“Nasan ba zaki rasa jin labarina ba. Kamar yadda nake da tabbacin an sanar da ke wacece ni. Idan kuma baki sani ba zan ƙara miki haske a kan ko ni wacece.

Ban zo gidan Nasir dan na dauwama a cikinsa ba Zahra, asalima zamana ba zai wuce na wasu ƴan ƙidayayyun lokaci ba wadda a yanzu ba zan iya faɗar ko wannne lokaci ba ne.

Amma ina da yaƙini idan rayuwa ta miƙe zai nuna mana.”

“Kina so ki ce min kin yi auren manufa da Nasir kenan?” Zahra ta faɗa da fuskarta ke ɗauke da zallar mamakin Hafsa da ya kasa ɓacewa a idanuwanta.

Kai Hafsa ta girgiza “Na aure shi ne saboda ke.”

Miƙewa Zahra ta yi tana dafe ƙirjinta da ta ji kamar ana biga mara mashi a cikinsa.

“Ni kuma?”

Miƙewa Hafsa ta yi tana murmushi da ajiye kofin “Na gode da tarba mai kyau. Ina fatan na saka miki da mafi girman sakamako fiye da wadda kika min a yau ɗin.”

Daga haka ta juya da niyar barin palon “Me yasa saboda ni?” Muryar Zahra ta sauƙa a kunnenta. Muryarta da sanyi kamar yadda ɗabi’arta ce sanyi ga komai na rayuwarta.

“Idan lokaci ya yi zan faɗa miki dalili. Amma kafin nan ki waiwayi rayuwarki da tsawon zamanki da Nasir, ki nazarci kyawawan abubuwan da ya mallaka miki. Idan na dawo zamu tattauna a kan hakan.”

Daga haka ta fice ta bar ɗakin tana rufe da ƙofar palon.

Kai tsaye sashenta ta nufa, bata tsaya ɓata lokaci ba ta buɗe ɗakin, domin ta shiryawa komai daga Nasir ɗin, zata jure zafi na ɗan lokaci, za kuma ta saba da zafin zuwa lokacin da ta so.

Tana buɗe ƙofar ta same shi a kwance a kan gado ya kifa cikinsa, hannayensa damƙe a cikinsa, sai juya kansa ya ke.

Da sauri ta ƙarasa kusa da shi “Subhanallah! Nasir me ke faruwa? Mene ne?” Ta yi maganar a ruɗe tana jin gabanta na harbawa, tana tsoron kada a ce ta yi kisa ne.

Jijjiga shi ta fara yi “Dan Allah Nasir kada ka mutu. Mene ne? Me ka sha haka?” Ta yi maganar da tashin hankali.

Sai a lokacin ya juyo da birkitaccen idanuwansa, da suka gama shigewa ciki, sun zurma sun ƙanƙance saboda tsananin fitinar da ta ci shi, tana kuma shirin hallaka shi.

Kamo hannunta ya yi da ƙarfi, yana birkito da ita, ya kwantar da ita, da zafinsa yake son yin watsi da duk kayan jikinta.

Bata hana shi ba, saboda ta shirya ma hakan, ya kuma bata tausayi fiye da kima, sai dai bata sani ba ashe shirin nata na banza ne, domin sai da ra raina kanta, tun tana ɗaukan abin na hankali har ta fara kukan tashin hankali, Allah kaɗai yasan yawan marukan da kumatunanta ya sha, sambatu kam yin su take da yaruka mabanbanta.

Bata taɓa tunanin zata waye lafiya lau da laɓɓanta ba, musamman a yadda yake tsotsarsu da taune su, yana gunji kamar zakin da ya hango kura a fadarsa.

‘Ban shirya mutuwa yanzu ba. Karka kashe ni ta wannan sigar Nasir.’_ Ta yi maganar a ƙasan zuciyarta, a yayin da hawaye ke gangarowa a kuncintaa.

“Haka mazan suke dama?”
Ta sake tambayar kanta a karo na biyu, wani ƙunci na mamaye zuciyarta da gaɓɓan jikinta….

<< Jini Ya Tsaga 34Jini Ya Tsaga 36 >>

1 thought on “Jini Ya Tsaga 35”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×