Wajen ya ci gaba da girgiza ya yin da gunkin mutun mutumin ya ke ƙara ɓantarewa, wasu abu kamar dutsuna suka zagwanyewa suna zuba a jikinsa.
Tass suka zube sai ga wani tsamurarren mutum ya bayyana sanye cikin kaya mai uban yawa, da kuma wata zungureriyar hula a kansa. Kayan da ke jikinsa kuwa tsaf za a sawa mutane goma su wadata a jikinsa, sai miƙeƙƙen hancinsa da yafi komai tsayi a fuskarsa, kai kace karas a ka aza a wajen.
Miƙewa ya yi tsaye a lokacin da mutanen suka duƙar da kansu ƙasa, suna risina. . .