Skip to content
Part 39 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

Wajen ya ci gaba da girgiza ya yin da gunkin mutun mutumin ya ke ƙara ɓantarewa, wasu abu kamar dutsuna suka zagwanyewa suna zuba a jikinsa.

Tass suka zube sai ga wani tsamurarren mutum ya bayyana sanye cikin kaya mai uban yawa, da kuma wata zungureriyar hula a kansa. Kayan da ke jikinsa kuwa tsaf za a sawa mutane goma su wadata a jikinsa, sai miƙeƙƙen hancinsa da yafi komai tsayi a fuskarsa, kai kace karas a ka aza a wajen.

Miƙewa ya yi tsaye a lokacin da mutanen suka duƙar da kansu ƙasa, suna risina gwuiwarsu ɗaya a ƙasa ɗayar kuma suka dogara hannunsu a kanta, kansu kuma na durƙushe a ƙasa har a lokacin.

Gefe da su Hafsa ce kwance a sume jini na zuba ta hannunta daga inda  Afoi ya yanke ta da wuƙa.

Dariya tsamurmurin mutumin ya fara yi, yana bin mutanen nasa da kallo.

“Affawio, Wayion Moilowa?” Ya yi maganar da muryarsa mai amo da kuma gargada, kamar kaset ɗin da aka kunna yana scraching.

Da sauri Affawioiya miƙe yana isa gaban mutumin da nuna masa inda Hafsa ta ke kwance bata san inda kanta ya ke ba.

LKallon wajen ya yi, yana ganinta da zubin suturar da ya sha banban da ta mutanensa, kamar dai yadda aka sanar da shi a baya.

Taka siraran ƙafarsa ya ke, wadda zaka yi tsammanin ba xa su iya ɗaukan gaɓɓan jikinsa ba, saboda tsanannin siririnta.

Ya isa kusa da ita, yana ƙara wara manyan rigunan da ke jikinsa, wadda da alamu dai shine ya kwashe kayan mutanen garin gaba ɗaya.

Tsugunnawa ya yi yana ɗora hannunsa a kan goshinya, wadda a take goshin Hafsa ya tsage, jini ya fara  fitowa ta jikinta yana shiga jikin tsamurarren mutumin.

Wadda shigar jinin nata ne zuwa jikinsa ya haddasa jikinsa ɗaukan rawa, ƙasar wajen ta fara girgiza kamar kuma an wulla shi baya, haka ya yi tsalle da tumami sai ganinsa suka yi a kan rushasshiyar kujerarsa.

Da gudu suka iyo kanta suna dafa shi “Abior, Mui furio ambui?” Affawio ya jefa masa maganar cikin tashin hankali, wadda suma mutanen wajen suke cikin tashin hankalin.

Ƙoƙarin miƙewa ya shiga yi, sai dai ƙashinsa da dama kamar ya karye ya fara yin ƙara, sai da ya lumshe idonsa da ƙarfi, ya fara karanto wasu suddabaru, wadda hakan ya haddasa tashin wata guguwa mai ƙarfi, baƙa ƙirin da ita, wajen kam fara girgiza ya yi, manyan dutsunan da suke saman kogon suka fara faɗowa, ƙasar wajen ta fara tsagewa.

Ganin hakan yasa mutanen fara gudu suna neman hanyar da za su fita dan su cuci rayuwarsu. Sun riga da sun san waye ne Abior mugun mutum ne da ya addabi rayuwarsu a shekarun baya da suka wuce, bama iya su kaɗa ba, tasirin shu’ummancinsa ya addabi duniyar saharar da suke ciki.

Basu san wata ƙaddara ba ce ta sa suka yi gigin tado shi daga daskarewa da ya yi.

Sai dai abin tashin hankalin lokacin da suke tunanin suna gudun dan ceton rayuwarsu amma sai suka lura gudun nasu a iya waje ɗaya suke yinsa, babu alamun suna matsawa ko nan da can.

Ihun su ne ya fara cika wajen a lokacin da ƙasar wajen ta dare, wasu a cikinsu suka fara tuftawa cikin ƙasar, waɗanda suke yi yunƙurin matsawa kuma suka kasa.

A lokacin ne Hafsa da take gaf da faɗawa ramin ta buɗe idanuwanta, jin ihun mutanen da ya cika wajen, sai dai bata ganin komai, face baƙar guguwar data cika wajen, sai hucin zafin da ke tasowa daga ƙasan ramin da ke kusa da ita.

Ƙoƙarin miƙewa ta shiga yi, taji wani abu ya danneta, hakan yasa ta kai idonta dan ganin abin, ƙaton dutse ta gani a kan ƙafarta, sai a lokacin ta ji azababben ciwon ƙafarta wadda take jin ciwon kamar ba a jikinta yake ba.

Ganinta ya fara yin duru-duru sakamakon jinin da ya zuba a jikinta.

“Astagfirullah! Ya Allah ka yafe min, kar ka ɗauki rayuwata ba tare da na nemi yafiyar mutanena ba.” Ta yi maganar hawaye na gangarowa a idanuwanta.

Ita kam ba zata iya tuna adadin masifa da wahalar da take cikinta a yanxu ba. Ta sani Allah mai rahama ne ga bayinsa, amma kuma baya yafe laifin wani da wani.

‘To ma wai ita a yanzu da ba zata iya tuna yaushe rabonta da sallah ba wata rahama take tsammanin zata samu idan har ta mutu a yanzu?’

Tuna hakan da ta yi ne ya sata fashewa da kuka, ta rufe idanuwanta, a hankali ta buɗe bakinta ta fara karanto Alqur’ani tana karanto suratul Rahman. wataƙila ta zama kankarar zunubi a gareta da kuma rage mata raɗaɗin zuciyar da take ji.

Sai dai abin da bata sani ba, karatun da ta fara yi ya kawo tsayawar guguwar da Abior ya haddasa, ƙasar da ta rabe kuma ta haɗe a lokacin. Ya yin da mutanen da suke gudu a waje ɗaya suka ji kamar an sakar musu ƙafafuwansu.

Sai dai kuma sun gagara tafiyar ne, a lokacin da kunnuwansu ya ke jiyo musu wani sauti mai daɗi da yake ratsa kunnuwansu, yana ta yar musu da tsikar jikinsu, sautin da ba su taɓa jin irinsa ga a tsawon rayuwarsu.

Da sauri suka mayar da kallonsu ga inda suke jin sautin, ganin Hafsa kwance idanuwanta a rufe hawaye na gangarowa a idanuwanta tana kuma karanto zancen da ba su san ko menene ba, yasa suka matsa kusa da ita, suna tsugunnawa da fatan kada ta tsayar da waƙen da ta ke rera musu.

Daga can kuwa Abior ji ya yi wani abu mai zafi yana huda fatar jikinsa, hannunsa da ya ɗora a goshin Moilowa kuma yana zangwayewa kamar dalma.

Ƙara ya sa mai rangaji sai dai ƙaran babu wadda ya ji shi, asalima kamar a iya shi kaɗai ne ya tsaya.

Cire zungureriyar hular kansa ya yi, sai ga gabjejen kansa ya bayyana, wadda ya fi komai girma a jikinsa. Kayan jikinsa ya fara cirewa yana ɗaurewa  hannun nasa da shi, amma kuma da kayan sun sauƙa a hannunsa sai su kama da wuta.

Abu kamar wasa sai da ya rage daga shi sai ɗan fatarin da ke jikinsa. Ya zubawa hannun nasa ido hawaye na zuba a idonsa. Bai yaɓa ganin masifa irin wannan ba kamar yadda bai yi tsammanin akwai wani iftila’i da ya wuce na zamansa a matsayin gunki ba.

Daga ɓangaren su Hafsa kuwa ganin halin da take ciki da rawar da muryarta take, karantun nata ma ya daina fita yasa Affawio ya bada umarnin Joille ya ɗauke dutsen ya ɗauko Hafsa su fita da ita kamar yadda suka kawota.

Cire mata dutsen ya yi sannan ya sanƙamota kamar jaririya suka fice a  cikin kogon ba tare da sun ƙara bi ta kan Abior ba, wadda sam bai ma lura da al’amarinsu ba.

Sai dai suna fita daga cikin kogon, kogon ya nutse ya ɓace ɓat, wadda hakan ya haddasa musu sauƙe ajiyar zuciya, daga nan masu kuka suka fara kokawa a kan ɓatan da ‘yan uwansu suka yi.

Wasu kuma yaran su ne suka faɗa a cikin kogon bayan ramin ya buɗe.

Sun ɗauki lokaci a haka kafin Affawio ya bada umarnin tafiya.

Suka sake dawowa bukkokinsu, Affawio ya kira mai maganinsu dan ta duba Hafsa da ya lura ƙafafuwanta na reto a kuma tsayar da jinin da ke zuba a hannunta.

Mai maganin tana xuwa ta fara ƙoƙarin daka wani ganye a dutse ta dago da ruwan cikinsa ta sa a hannun Hafsa, wadda take wajen ya fara suya kamar an sa albasa a cikin mai. Hakan yasa Hafsa rafka uban ihu da ya sa har ‘yan wajen sai da suka ji.

Sai da ta lime da yin ihun, sannan ta fara mayar da numfashinta.

Ƙafarta matar ta ɗaga, sai dai ko alamu Hafsa bata san ta taɓa ƙafar ta ta ba.

Daddana wajen ta yi, sai taji kamar ƙasusuwan wajen ne suka yi rugu-rugu. 

Ɗago da kallonta ta yi ga Affawio ta girgiza masa kai “Moilewa gai lahrabbior, Affawio.”

Dafe kai ya yi yana kallonta mai maganin, cikin takaici da tsananin tausayin Moilewa da yake ji a ransa.

“Agrah mio Muiwa, Anna.” Ya yi maganar cikin sanyin murya.

Kai Anna ɗin ta girgiza ta sake taɓa ƙafafuwan Hafsan, da ƙoƙarin gyara ɗayar da take tunanin zata iya gyaruwa, ƙafar hagun ɗinta kuma babu ta yadda xata iya gyara mata ita, saboda tadda ƙashin ya yi raga-raga.

Za dai ta sa mata magani raunin da ke fatarta ya warke amma banda ƙashin da ya riga ya dandatse.

Ta mata ɗaurin wadda sai da aka rirriƙe Hafsa Affawio da Joille suka riƙeta.

An yi nasara ƙwarai an ɗaura ƙafar tata guda ɗaya, wadda bayan gama ɗorin ne kuma ta sake sumewa a wajen saboda azaba.

Ga yunwa ga wahala, ga kuma zubar jinin da ta yi a jikinta.

Hakan ya zame mata goma bala’i a rayuwarta, wadda ya wuce hakan musamman da ko ruwa bata samu ta ɗiga a harshenta ba…

Oum Nass

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Jini Ya Tsaga 38Jini Ya Tsaga 40 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×