Skip to content
Part 40 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

Tsawon kwanaki uku ta ɗauka ba tare da sanin inda kanta ya ke ba. Daga ƙarshe ta farka tana buɗe idanuwanta da nazartar inda take.

Tana kwance a kan wani gadon kara da aka aza masa yayi a kansa, da wani abu kamar fatar saniya  a samansa, sai ya tashi kamar katifa. Rufin wajen take ganin da ya ƙara tabbatar mata tana cikin bukka ne, duba da ginshiƙin da ke wajen da kuma kalar kararen da ke wajen.

Idanuwanta ta lumshe tana ƙara buɗe su a lokacin da idanuwanta ya dauka a kan ƙafarta da take jin azaba a cikinta, ɗaya ƙafar ta gani an ɗaureta da karare da wani tsumma. Yayin da ɗayar take sanya cikin kwali da ba tare da an sa mata kararen ba.

Ganin zanin atamfar da ke jikinta ta yi, wadda tsabar dauɗa da haɗuwar jini ya fita a kamanninsa, domin idan ba sanin zanin ka yi ba, sai ka ɗauka nakiya a ka kwaɓa a ka mulmula a cikinsa ne.

Hannnunta ta yi yunƙurin ɗagawa sai dai ga mamakinta ya mata nauyi, nauyi na sosai kamar an aza mata dutse a cikinsa.

Kallonta ta mayar ga hannun ta ganshi ya kumbura sintum har sheƙe yake yana ɗaukan ido, ga wani ganye da a ka lulluɓa mata a kansa.

Sai a yanzu ta tuna kalar azabar da ta sha a waccan ranar, da maganin da aka sa mata, gashi a yanzu babu ciwon sai kumburin da hannunta ya yi.

‘Ya Allah ka sassauta min.’ Ta yi maganar a ƙasan zuciyarta, tana sake lumshe idanuwanta, domin a yanzu dai babu wani ɓurɓushin hawaye a idonta, ta riga ta sawa ranta zata amshi duk ƙaddarar da ta faɗo gareta, kuka ba zai zama ƙarshen matsalarta ba, kamar yadda take da yaƙinin ba zai zama mafari na ƙarshen rayuwarta ba.

Koda zata zubar da hawayenta duka, to tasan babu wadda zai ji ta, babu kuma wadda zai kawo mata ɗauki. Amma zata yi haƙuri zata yi addu’ar neman yafiya ga Ubangijin da ya halicceta.

Shigowa ɗakin da a ka yi da motsin muryoyin da ta ji ya tabbatar mata da mutanen ƙabilar sahara ne da suka so ɗaukan rayuwarta.

Tana ganin lokacin da mai maganin ta matso kusa da ita, tana shafata da kuma mayar da kallonta ga mutumin da suka zo, ta masa yare da faffaɗan fara’a a fuskarta, wadda a idanuwan Hafsa gani take kamar tana runtuma ihun kuka ne.

“Affawio, Moilewa agraf hai ma’ah.”
Tana ganin yadda ya faɗaɗa fara’a a fuskarsa yana ƙarasowa kusa da su, ya risina a gaban Hafsa ya fara shafa kanta.

“Hai fahay Moilewa.” Ya shiga nanata mata kalmar da ta fahimci sannu yake mata.

Kai ta jinjina masa tana ƙoƙarin yin fara’a a fuskarta.

Daga nan ta ji Anna ta ce “Noi bilaro Mash, Affawio.”

Tana gama maganar ta ga Affawio ya fita, bai jima da fita ba sai gashi ya dawo da ƙaton faranti a hannunsa da wasu kwanika a kansu suma ƙananu.

Ya miƙawa Anna. Ta amsa ta ajiye, sannan ta shiga ƙoƙarin tada Hafsa zaune, ya yin da Affawio ya taimaka mata ta tashi.

Wani ruwa nai mai ɗumi wadda kalarsa ta banbanta da ruwa asalima kore-kore Hafsa ta ga ni a jikin ruwan.

Hakan dai ta bata tana gwada mata ta kuskure bakinta, kurɓan ruwan ta yi, sai dai ga tsananin mamakinta ta ji ruwan zafi zau a bakinta, ga kuma wani abu kamar gishi-gishiri kamar ɗaci ɗaci a cikin ruwan. Ta ji ko ina a bakinta ya gauraye da ɗanɗano nasu.

Ta kuskure bakin nata, ta zubar, da mamaki a tare da ita, sai taga jini ya fito a cikin ruwan. Kai Anna ta jinjina tana faɗaɗa murmushinta da kuma sake cewa ta kuskure ɗin. Haka ta yi ta yi har sai da ruwan ya ƙare, sai kuma ta ji bakinta saƙayau, tana jin wata iska mai daɗi na shiga cikinta.

Ɗauko wani kwanon Anna ta sake yi ta buɗe, shi wani abu ne kamar dawa kamar gero sai ganyayyakin da suka cika shi. A haka dai abin idan ka kalla kamar ka zura da gudu dan rashin kyansa.

Bata ta yi tace ta ci. Ido Hafsa ta fiddo waje, wani sabon tashin hankali na bijiro a gareta, ta ya zata iya cin abin nan.

Kai Anna ta gyaɗa mata tana sake umartarta da ta ci, ganin babu fuska a wajen Anna ɗin ya sa ta fara ci, tana jin wani uban ƙarni da bauri ya karaɗe sassan jikinta da bakinta.

Amai ya fara taso mata, amma babu komai a cikinta balle ta amayar da shi. Ajiye kwanon take son yi, amma Anna ta sake sa mata tsawa dole ta shiga tura abin.

Tana yi tana ƙoƙarin amayar da shi, amma ganin idanuwan Anna masu kama da na mujiya yasa ta haɗiye aman ta ci mai yawa sannan ta ture kwanon.

Kai Anna ta girgiza mata ala dole sai ta cinye ganyen. Hawayen da take tunanin ta daina zubar da shi, sai gashi ya gangaro a kan fuskarta, amma bata ga alamun sassauci da tausayinta a fuskarsu ba. Har sai da ta fara cusa shi, zuwa lokacin kuma ta gaza riƙe amanta, ta shiga dawo da abin da ta ci.

Bayan ta yi aman jikinta ya ɗauki rawa ganin kallon da Anna ta ke mata, sai dai ga mamakinta taga Anna ɗin ta tashi ta ɗauko wani tsumma ta goge wajen.

Ta ɗauko wani abu kamar kofi  kamar tasa, a jikinsa tana iya hango dafaffen abu fari yana fidda turiri.

Miƙa mata shi Anna ta yi, ta fiddo idonta waje “Me zan yi da shi?” Ta samu kanta da yin tambayar, dan ta manta ma da cewar basa jin yarenta.

Da hannu ta mata nuni a kan ta sha. Tana zazzare mata idanuwanta.

Dole ta kai abin bakinta ta kurɓa, shi kam jinsa ta yi kamar ɗanyen man shanun da ba a soya shi ba.

“Wayyo Allah nah! Ashe akwai kasada a cin abinci ban sani ba?

“Ashe ba yunwa ba ce wahala, shi kansa ƙoshin ma wahala ne?”

Ta yi maganar a ƙasan zuciyarta hawaye na gangarowa a idanuwanta.

Shima sai da ta shanye rabinsa, sannan ta ajiye kofin, wannan lokacin Anna bata hanata ba, ta karɓa ta ajiye.

Ruwa take buƙatar sha, sai dai da alamu su basu san ruwa ba, tana so ta kwantar da zuciyarta da take ƙoƙarin dawo da damammen abin da bata san ko mene ne shi ba, sai dai da alamu zata dawo da shi ɗin ne.

Ƙoƙarin Amai ta shiga yi, sai dai kafin ta yi, taji an matse mata hancinta tam, an kuma buga mata tsakiyar kanta da ƙarfi.

Hakan yasa ta haɗiye yawun ta shiga kakarin neman numfashinta, gashi hannu ɗaya gareta ba zata iya ƙwatar kanta daga ruƙon da Anna take mata ba.

tsawon minti guda sannan Anna ta sake ta, ta koma ta zauna, a lokacin Hafsa ta fara maida numfashi tana ɗora hannunta ɗaya a kan ƙirjinta.

Ɗauko wani kofi Anna ta yi ta miƙa mata, da sauri ta amsa bata tsaya duba ko mene ne ba  gudun kada ta ga abin da zai tada mata hankali, tana kaiwa bakinta da mamakinta sai ta ji ruwa ne, sai dai bai fi kurɓa shida ba ta ji wayam har ya ƙare.

Murmushi Anna ta yi ta miƙe tana tattara kayan da miƙawa Affawio da yake kallon abin da suke yi.

Daga nan Anna ta dawo ta jingineta a jikin ginin ta na mayar da numfashi, ta lumshe idanuwanta.

Bata son yin tunani shi yasa ta fara rero karatun alqur’ani a hankali. Wadda hakan tasa Affawio zama yana kallonta da sauraronta, shi dai yana son waƙen nan da take yi, yana jin nutsuwa a duk lokacin da take yinsa.

Ya yin da a gefen Hafsa ta ke karatun tana hango fuskar Alhaji malam da Sayyadi, mutane biyun da suka shimfiɗa rayuwarta a kan tsayuwa da addininta. Mutanen da kullum suke nata uzuri a kan duk abin da take musu ba.

Bata taɓa ganin ɓacin rai a tare da su ba, bata taɓa jin kalmar ɓatanci daga gare su ba, kullum addu’arsu ɗaya a kanta, Allah ya shiryeta.

Yau ga shiriyar ta zo mata a baibai, tana neman su dan ta nemi yafiyarsu amma sun yi nesa da ita, kamar yadda take nesa da su, tana tunanin wataƙila rayuwarta ta zo ƙarshe ne ba tare da zata sake sanya su a idanuwanta ba.

A hankali muryarta ta fara yin rauni hawaye na cin ƙarfin idonta, tun tana yin karatun a bayyane, har kuka ya ci ƙarfinta.

A lokacin ne Affawio ya dafa kanta hakan yasa ta buɗe idanuwanta, ganinsa tsaye a kanta shi da wasu mutanen da bata san yaushe suka zo wajen ba ya sa ta ƙara buɗe ƙananun idanuwanta.

Kai Affawio ya girgiza mata alamun ta yi haƙuri ta yi shiru, yana girgiza mata kan yana mata magana da yaren su.

Dole tasa hannunta ta share hawayen.

Ya yin d ta ɗaga ɗaya hannun nata da mai lafiyar ta fara yi masa addu’a da karatu, tana tawassali da shi da fatan ace kaurin hannun nata ya ragu da kuma raɗaɗin ciwon sa da take ji a tare da ita.

*****
Bayan watanni Huɗu.

Zuwa lokacin Hafsa ta saba da rayuwa da mutanen da ƙaddara ta shimfiɗa zamanta da su, ƙafarta ɗaya da aka ɗaura ta warke, yayin da ɗayar kuma ta zama marar amfani a gareta, idan ka ganta sai ka ɗauka tana amfani amma a zahiri bata wani amfani a gareta.

Hannunta kuma saboda yadda take masa addu’a da shafe shi da ruwan addu’ar shima ya dawo daidai, amma duk da haka bata iya ɗaukan abu mai nauyi da shi, asalima ya dawo ne kamar fanko a gareta, taimakonta ɗaya da ya kasance hannun hagun ɗin ta ne.

Ta fara jin yaren mutanen garin tana kuma yin aikin da suke yi, banbancinta da su ɗaya ne, bata irin shigar da suke yi, sai dai wani burgujejen bargon da take lilliɓe jikinta da shi musamman saboda mutuwar da kayanta suka yi.

Idan ta yi alwala tana sallah sai su ringa kallonta, idan tana karatu kuma su kewayeta suna sauraronta.

Wani lokacin Affawio na tambatarta me ta ke yi tana bashi amsa da sallah ta ke da kuma karatun Alqur’ani.

“Mene ne sallah? Menene ne ALqur’ani?” Ya ke tambayarta duk da yarensu.

“Sallah ibada ce da ta zama wajibi a kan kowanne musulmi. Haka kuma gaisuwa ce da bawai ke yi da Ubangijinsa a kan hakan ana rubutawa mutum lada. Sallah ke banbance tsakanin musulmi da bawansa.

Alqur’ani kuma zancen Allah ne da ya sauƙarwa Annabinmu Muhammad (S.A.W). A cikinsa akwai haske na shiriya, da kuma samar da nutsuwar zuciya, shine maganin duk wani damuwa a duniya. Sannan ana rubutawa mutum lada idan yana yawan karanta shi, zuciyar mutum tana yin sanyi da samun nutsuwa.”

Shiru Affawio ya yi, yana nazarin maganarta, tabbas duk lokacin da ta ke yin karatun yana samun nutsuwa sosai a zuciyarsa, wadda har ta kai ba ya iya tashi daga inda take.

“Wane ne Ubangiji?  Wanene Muhammad?” Ya sake jefa mata tambayar.

“Ubangiji shine Allah wadda ya halicce mu, ya raine mu da ni’imarsa, ya halicci sama da ƙasa da bishiyoyi, da duwatsu, ya halicci komai da komai.

Muhammadu kuma ya kasance Annabi ne da Allah  ya aiko shi zuwa ga mutane, dan ya kira su zuwa ga addinin musulunci, ya kuma hana su bautawa kowa idan ba Allah ba, ya kira su zuwa ga hanyar tsira, ya tunasar da su Aljannar Allah ga wadda suka bi shi, da kuma wutar jahannama ga wadda suka kafirce masa.”

Kai Affawio ya sake gyaɗawa yana jin zuciyarsa na buɗewa da jin zancen Hafsa abin da bai taɓa ji daga bakin wani ba a tsawon rayuwarsa.

“A ina Allah ya ke?”

“Yana sama ta bakwai a kan al’arshinsa.”

Kai ya sake gyaɗa mata   “A ina zan ga Addinin musulunci na shiga?”

Jin maganarsa ta yi kamar sauƙar ruwan ƙanƙara a zuciyarta, wadda kuma bata taɓa tunanin zata ji maganar daga gare shi ba.

Kai ya gyaɗa mata “Ina so na yi musulunci, na yi karatun Alqur’ani na yi sallah yadda kike yi.”

Hawayen daɗi ne ya gangarowa Hafsa, hawayen  da zata iya cewa na farin ciki ne.

‘Ashe akwai rana irin wannan da zata zo gareta? Ashe akwai wata farfagandar rahama ga rayuwarta? Allah na gode ma da wannan rahamar da ka sauƙar gare ni.’ Ta sake maganar hawaye na gangarowa a kan fuskarta wadda a yanzu ba zaka taɓa zatan Hafsa Kamaludden ba ce, saboda baƙin da ta yi da kuma kwantsamewar da ta yi kamar sikelato.

“Ki faɗa min ina zan ga Addinin musuluncin na shiga?” Maganar Affawio ta dawo da ita daga duniyar tunanin da ta ke.

“Addininku na da kyau, Moilewa. Tun da kika zo abubuwa suka yi ta faruwa da ke, amma ko sau ɗaya ba ki daina Karatu ba. Wadda karatun naki ne ya ce ci rayuwarmu da ta mutanen da suka rage mana. Ya kuma yi silar kawo mana ƙarshen Abior daga masifar da ke shirin jefo mana.

Moilewa ke alkhairi ce tun da a dalilinki muka tsira da rayuwar mu. Duk da a dalilin mu kin rasa ƙafarki da hannunki ɗaya. Amma baki zauna kina jira a baki ba, kina miƙewa da ƙafarki kina neman abin da za ki ci.

Gashi koyaushe jikinki a lulluɓe yake da mayafi, babu mai ganin jikinki. Moilewa, ki sanar da ni inda zan  samu irin hasken da kike da shi.”

Kai ta jinjina kafin ta yi magana ta ji maganar mutanen da suke garin suna cewa “Moilewa, muma za mu yi addininki.” Kallonsu ta ƙara yi hawaye na sauƙo mata, ashe duk zaman da suka yi da Affawio suna tare a waje ɗaya.

Kai ta girgiza musu “Addinina mai sauƙi ne da ba ya buƙatar a je wani wajen dan a shige shi. Addinina yana bawa kowa damar ya musuluntar da wani mutuƙar ya kasance musulmi ne.

Dan haka zan faɗi wasu kalmomi kuma sai ku faɗa.”

Kai suka gyaɗa mata cikin gamsuwa da ɗokin jin kalmomin.

“Ku ce Ash hadu al’ilaha illallahu, wa ash hadu anna muhammadu rasulillah.” 

Faɗa suka yi tana nanata musu har suka faɗa.

Daga nan ta sauƙe hamdala tana jin wani sanyi na ratsa gaɓɓan jikinta “Alhamdulillah barkanku da shigo addinin musulunci, addinin tsira addinin haske. Yanzu ni da ku mun zama abu guda ɗaya.”

Suma kansu sai murna suke suna shimfiɗa murmushi a kan fuskokinsu, musamman yadda suka ji wani sanyi a zuciyoyinsu, suna jin kamar an sauƙe musu wani ƙaton gumgumemen dutse a ƙirjinsu.

“Yanzu saura abu ɗaya, za ku yi wankan shiga musulunci, wadda zai kore ƙara tsaftaceku daga waccan abin da kuka bari na rashin addini.”

Kai suka gyaɗa kamar wasu ƙadangaru, ta koya musu yadda za su yi wankan musulunci, sannan ta umarce su da su rage sumar kansu da gashin fuskarsu da suka yi butu-butu kamar wasu birrai.

Ai nan take suka tafi suka aske gashin nasu ma gaba ɗaya, wadda hakan ba ɗaramin daɗi suka ji ba, suka yi wanka kamar yadda ta koyar da su.

Daga nan suka sake dawowa.
“Yanzu zan fara koya muku karatu na alqur’ani da kuma na sauran littafan da zaku fahimci musuluncin kansa.

Cikin farin ciki suka zauna ta fara koyar da su, tun daga fatiha suna maimaitawa. Daga nan ta koyar da su yadda za su yi tsarki da alwala. Da kuma sallah.

Abin da ya birgeta ganin yadda suke ganewa, musamman da ta ke yin abin tana nuna musu yadda za su yin, da alola kam da ruwa a kusa ta ke koya musu ita.

A cikin wata biyu ta koyar da su abubuwa da yawa, su kansu a yanzu sun fahimci rayuwarsu ta fi ta baya kyau, sun daina sa ɗankamfe da ganye sun koma sa kaya sak a jikinsu.

Hafsa tana ganinsu a matsayin wasu dangi nata, kamar yadda sume suke kallonta a matsayin hasken da ta shigo cikin rayuwarsu.

Akwai banbanci sosai tsakanin Hafsa baya da ta yanzu, sai dai wani lokacin takan rufe kanta a ɗaki ta yi ta kuka, kukan da ita kaɗai tasan kona mene ne, dama ɗaya ta ke nema a rayuwarta, damar ganin ‘yan uwanta da yaranta dan ta nemi yafiyarsu, domin vata jin a yanzu zata iya wata rayuwar ba tare da waɗan nan mutanen ba.

Waɗanda a yanzu duk sun sauya sunayen su Affawio ya dawo Muhammad saboda yadda Hafsa take basu tarihi da kissar Annabi, yace ya na so ya yi koyi da mai sunan kamar yadda yake ƙaunarsa. Anna ma ta mayar da sunanta Fatima.

Haka sauran mutanen garin duk sun sauya sunayensu sun koma na musulunci.
  Hafsa ce dai har yanzu suna kiranta da Moilewa domin sun ce ma’anar sunan ta dace da ita “Wato Haske.”

A wata safiya ne kuma suka wayi gari da hango wasu dandazon motoci masu ƙirar langruza suna nufowa inda suke. Hankalin su ya tashi sosai, musamman tun da suke ba su taɓa ganin mota a rayuwarsu ba.

Sai gashi motocin sun zagaye su, sojoji ne a cikinsu birjik ya yin da wata take tashi da jiniya, tana iya ganin sojojin da suke riƙe da manyan bindigu a hannunsu.

Salati suka fara suna ambatar kalmar inna lillahi wa inna ilaihirraji’un.

Domin kawo tsira daga rayuwarsu, daga nan sai suka ga an wullo wasu mutane guda uku a ɗaure kayan jikinsu ya yi fata-fata, kamar yadda jini ya ke fita a jikinsu.

Wani balaraben mutum ya fito a cikin ƙatuwar motar  da tafi sauran girma, yana sanye da kayan sojojin shima.

Yayin da wasu jami’an sojojin ke biye da shi, sai wasu samari su biyu da suke kai ɗaya su kuma sanye da kaki ruwan ƙasa a jikinsu.

Fuskokinsu babu walwala ko kaɗan, amma kuma hakan ba zai hana a ga tsantsar kyan da suke da shi ba.

“Ku nuna mana ina ta ke?” Kyakkyawan matashin ya faɗa da yasa mutanen wajen mamaki jin yana yare irin na Moilewa.

Jikin matasan da suka sha duka ya fara rawa, domin Allah kaɗai yasan kalar uƙubar da suka sha  a wata ɗayan da ya gifta.

“Wallahi nan muka kawo ta, a waccan bukar muka a jiyeta.” Na tsayarsu ya faɗa yana rawar murya da jiki. 

Hakan yasa balaraben ya matso kusa da mutane da yake da tabbacin basa jin yaren Hausawa duk da gashi a zahiri sun yi shiga irin ta su.

“Dan Allah ko kun ga wata mata a waccan Bikkar watanni takwas baya da suka wuce.” Mutumin ya yi maganar da muryarsa mai sanyi, wadda suke jinta kamar busar sarewa, ba su taɓa tunanin za a samu murya mai daɗi haka ga ɗa namiji ba.

“Moilewa ce.” Wani yaro ɗan shekara goma ya faɗa.

Hakan ya sa Affawio ya gyaɗa kai yana cewa “Moilewan mu ne.”

Kan sojan ya ɗaure jin suna kiran wani suna da bai san wanne iri ba ne “Ina ta ke?” Ya yi maganar, hakan yasa suka nuna masa inda take idanuwanta a rufe duk a bin da ake tana zaune ta lumshe idanuwanta, tana karatu.

Wadda kallonta da ya yi sai da ya ji zuciyarsa ta harba da ƙarfin gaske ‘Ta ya za a ce Hafsa ce ta dawo wannan komaɗaɗɗiyar matar, ga baƙin da ya zarta na taɓo a tare da ita, wani uban bargo ne a jikinta ta duƙunƙune jikinta da shi.’

Takawa ya fara yi yana ƙoƙarin aro dauriya da juriya dan ya isa inda take, yana isa yana jin sautin karatun Alqur’anin da take yi a cikin suratul Ali’imran. yana jin sanyin murya da ƙira’ar da take tashi wadda ta ke tuno masa abubuwa da yawa.

Tabbas Hafsa ce. Har ya ƙarasa kusa da ita ya tsugunna yana ƙara kallonta, hawaye na taruwa a idanuwansa, hawayen da bai san kona mene ne ba.

Na tausayinta ne ko kuma na ƙaunarta da ya shafe shekaru yana riƙe da ita.  

Kamshin da ta ji ya yiwa hancinta maraba yasa ta fara ƙoƙarin buɗe idanuwanta, tana  jin baƙon abu da harbawar zuciyarta a lokacin da take jin ƙamshin.

Juyo da kanta ta yi ta kalli inda ƙamshin ke tasowa sai dai halittar da ta gani a gabanta yasa ta wara idanuwanta tana ɗora su a kan mutumin, da idan ba saninsa ka yi da gaske ba zaka ɗauka balarabe ne ya fito daga ƙasar misrah.

“Nahnaaa!!” Ya kira sunan a hankali.
Duk duniya mutum ɗaya ne ya ke kiranta da wannan sunan, mutum ɗayan da take fatan sake ganinsa a rayuwarta ta ƙarshe da ta rage mata, mutum ɗayan da ya ke mata uzuri a kan komai na rayuwarta.

Kanta ta girgiza tana da tabbacin ba shi ba ne, ba zai taɓa zuwa dan ya neme ta ba, ba gaskiya ba ne. Mafarkin da ta saba yi ne yau ma ya zo mata a matsayin gizo, sheɗan na ƙoƙarin gindayar da ita daga karatun da take yi.

Amma kuma koda mafarkin ne ya kamata ace ta ci gaba da kallonsa ta samu kalma ɗayan da zata faɗa ta neman yafiya a gare shi, wataƙila saƙon ya isa, amma kuma ina bakin ta ya tafi? Babu kalmar da ta dace da zata faɗa masa koda ace shi ɗin ne..

******

A kafta

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Jini Ya Tsaga 39Jini Ya Tsaga 41 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×