Skip to content
Part 4 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

Ido Umma ta lumshe tana cilla tunaninta a shekarar da ta sabunta labarinta, ta raba tsakaninta da yaranta.

25,Mayu 2001

“Salamatu, yau ba zan sakaya na kiraki da sunan da ba wanda iyayenki suka raɗa miki ba.
Dan kina matsayin uwar gidan Alhaji hakan ba yana nuna zaki na mulkarmu bane. Daga rana mai kamar ta yau, bana buƙatar ki sanya kasafin abincinki da ni.”

Ɗagowa Salamatu tayi fuskarta ƙunshe da murmushi ta kalli mai maganar “Wanan ra’ayinki ne ai Kandala, amma ni ba’a min iyaka akan hana wata abinci da kuma bawa wata ba.
Zan sauƙe nauyin da yake kaina kawai.”

Tsaki Kandala tayi da ƙarfi tana kyaɓe baki “Andai faɗi ba nauyi, idan kin haifu a cikin tsoho da tsohuwa masu dattin hula kada ki ƙara yin kasafin abinci da ni.

Idan kuma tsintacciya daga sama ce zanga zahiri daga lokacin da na shigo cikin ƙidayar lissafin ki.”

Ɗagowa Salamatu tayi idanuwanta sun rine da kalar ja, wanda yake nuna tsan-tsar ɓacin ranta a bayyane.

“Ni kuma zan tabbatar miki da cewar na haifu a cikin iyayena.
Daga yanzu na haramta ma kaina yin abinci da ke da yaranki.”
Tana gama faɗar haka ta jefa mata ƙatuwar kular da ake zuba mata abinci ita da yara.

Guɗa Kandala tayi tana kiran “Tafi nono fari.” Ta ɗauki abarta ta ƙara gaba.

Da ido Salamatu ta bita da kallo. Tabbas Kandala fitinanniya ce, haka kuma mace ce mai iya sharri da ƙwarewa a kaidi irin na mungwagen mata.
Sai dai tana roƙon Allah da ya mata tsari da ko wani kaidi irin nata.

Bayan Sa’a Bakwai

Lokaci ne da Alhaji malam yake zama suna taɗi da iyalansa, anan kuma yake fuskantar matsalar da yaransa suke ciki da matansa dan a warware ta.

Bayan an gabatar masa da abincinsa, kafin yayi tunanin fara ci yaran Kandala da su uku suka kewaye shi suna kiran “Alhaji muma zamu ci”

Da mamaki ya kallesu kafin ya ɗora da tambayar su “Ba kun ci naku abincin ba?”

Kai suka girgiza kafin ƙaramar cikinsu da bata fi shekara huɗu ba tace “Yau duka bamu ci abinci ba. Umma taƙi bamu.”

Jin ta kira sunan Umma yasan cewar Salamatu ce tayi girkin ranar. Amma yaushe Salamatu ta rabu da kyawawan ɗabi’un da ya santa da su, har take yima yara ƙanana horon yunwa? Abin da ba tayi a lokacin ƙuruciyarta ba shine yanzu zatayi.

“Bazan juri hakanba ko kaɗan.”

Ya faɗa a fili yana tura ma yaran abincin gabansa.
Abin tausayi ganin sun shiga ci hannu baka hannu ƙwarya, kai kace sun shekara da yunwa, kafin ya gama mamaki yaran sun cinye abincin tass.
“Ruwa ALHAJI.” ƙaramar yarinyar ta faɗa, miƙa mata yayi yana jinjina ƙoƙarin cin da tayi ba tare da ta nemi ruwan ba.

“Salamatu! Kandala! Abu! ” sunayen matansa kenan da yake ƙwala musu kira.

Cikin sauri suka fito suna zama, dan basu taɓa jin sautin Alhaji irin haka ba.
“Lafiya malam da ƙwala kira haka?” Kandala ta faɗa tana dai-daita tsayuwarta.

Harara ya wurga mata yana maida kallonsa ga yaran, ya nuna mata su “Kina ina kika bar min yara da yunwa a duka yinin yau? Kuma a haka kina a matsayin uwa a garesu.”

Kai ta sunkuyar cikin kissa da munafurci irin nata, wanda turo yaran ma yana daga cikin shirinta.
“Ayya wanan ai ba sabon abu bane malam. Duk ranar girkin Umma Salamatu haka yarana ke yini, harda ni kaina, sai dai idan ina da sarari a lokacin sai na siya musu ‘yar taretsa ko kuma zogale a gidan Ma’u”

Ta ƙarasa maganar tana matsar hawayen munafurci “Ban san mi nayima Umma Salamatu ta tsaneni ni da yarana a gidan nan ba, duk da tsananin girmamatan da nake, kamar yayar da muka fito ciki ɗaya da ita.

Amma ko almajiran gidan nan sun fi yarana muhimmanci da kima a idonta.”

Tsananin mamaki da al’ajabi ya hana Umma salamatu magana, sai kallon Kandala da take, tana girmama ƙoƙarin ƙarya irin nata.

“Mi yasa baki taɓa faɗa min ba?”

“Bana so na tada hankalinka, na shiga tsakanin ƙaunar da ta daɗe a tare, ƙarin daɗawa ma, ba halinta bane, inaga da laifin da na mata har take horani haka, amma dan Allah ka tayani bata haƙuri horon ya isa haka, koda ban samu ba yarana ƙanana ne tana basu.”

“Ya isa!” Ya faɗa cikin dakekkiyar muryarsa, wadda kana gani ta ɓacin rai ce.

“A gidana za’a kawo min sabon abu? Har ayima yarana horo da abinci. Wanan abu ne da bazan iya jurarsa ba ko kaɗan.”
Magana ma samun dama ce, amma mamakin da ya daskarar da Umma salamatu ya hanata furta koda kalma ɗaya ce, ta kare kanta.

“Bana buƙatar mutanen da ke da son zuciya a tare da su, ba zan iya zama da matar da take da son kai da son zuciya ba. Ba zan iya zama da macen da bata tausayin yara ƙanana ba.

Dan haka ku sheda NI KAMALUDDEN na datse igiyoyin aurena dake kan Salamatu, daga yanzu babu ni babu ita har abada.”

“Inna lillahi wa inna ilaihirraji’un! Alhaji kayi gaggawa, bakayi bincike akan gaskiya ne ko kuskure bane, da girmanka ka aikata wanan mummunan hukunci haka.

Na shiga uku ni ABU! wanan tashin hankalin da mi yayi kama.”

Wata guduma ke sauƙa akan Umma tun daga tsakiyar kanta, har zuwa ƙafafunta, bata yarda akan abin da kunnuwanta suke jiye mata ba, sai a lokacin da taji mabiyarta Abu na nanata kalmar da kiran kuskure.

‘Ƙaddara bata mata adalci ba, sai a wanan lokacin zata raba tsakaninta da ahalinta. Gidan da tun da ta shigo bata taɓa sanya ƙafarta da sunan yaji ba, amma sai gashi yau ta samu zungurerren sakamako mai ɗauke da gurɓatattun ababuwa, mafi munin sakamako a wajan ‘ya mace.

Saki bama ɗaya ba har uku tashi ɗaya akan kuskuren da ba nata ba.’
Lallai ƙaddara faɗi gareta, kuskure ɗaya kan sabunta kyawawan labaran da kake da su.

Taka ƙafafuwanta tayi da ƙyar ta ƙarasa kusa da Alhaji malam, da ƙyar bakinta ya iya buɗewa ta fara ajiye kalmominta a kunnuwansa.

“Sakamako ya fita, waɗanda ke zurfafa tunani sun raunata, hakan ba na farko bane, sai dai ina fatan zamowarsa na ƙarshe.
Ina fatan lokaci zai buɗa maka ta hanyar haskaka maka giɓin da ka ma rayuwata. Nagode sosai da ingancin yarda da kyakkyawan sakamakon da ka bani, wanda zan shedawa duniya labarina.”

Tana gama faɗar hakan ta ƙarasa kusa da Kandala “Ba kiyi nasara ba Kandala, yaƙin da ke gabanki yafi wanda kika haƙo.

Bazan wai-wayeki dan ɗaukan fansa ba, amma ina fatan Allah ya saka min dai-dai da abin da kika min.”

Tana faɗa mata ta juya, a lokaci idonta ya sauƙa akan Hafsa, wadda tana jin duk abin da ya faru, ta kuma gani.

Riƙo hannun Umma tayi tana aikama da Alhaji malam da Kandala da mummunan kallo.
Ɗaci take ji na sauƙa a ƙasan zuciyarta, a gaban idonta mahaifinta ya saki mahaifiyarta har saki uku, akan labarin ƙanzon kuragen da bai duba inganci da fitar sa ba.

Hijabi ta sanyawa Umman ta riƙo hannunta suka bar gidan, tana jin sauƙar kukan Ummanta a ƙasan zuciyarta.

“Wanan hawayen naki ba zai zuba a banza ba Umma. Zan ƙuntatama rayuwar mutanen da suka zama sila na zubar hawayenki! Zan hora duk wanda ke da alaƙa da hakan. Wanan gidan, wanan ahalin, zasu ɗanɗani mummunan giɓin da suka ma rayuwarsu.”

Damuwar da ke cin ran Umma a lokacin bai bari ta fahimci haƙiƙani abin da Hafsa ke nufi ba.

Sai dai tafi yarda akan itama ɓacin rai ne na ɗan lokacin, da an kwana zata manta hakan.

*******
“Ya Allah” Ummah ta faɗa tana shafo fuskarta da tafukan hannayenta.
Tana share hawayen da ke zuba akan idonta.

Hafsa tayi nasarar raba Kandala da gidan Alhaji malam, ta hanyar yin amfani da nata rashin mutunci kuma ta je ta faɗama Alhaji malam ƙarya akan Kandala na zaginta da mata gori.
Sai da tayi fatan dama da Mahaifiyarta take zaman kishin ba da ɗiyarta ba, da kanta ta nemi saki da sauwaƙe mata, har tana fallasa kanta a matsayin itace ta shirya makirci da kuma asirin da boka ya mata har ya saki Umma.
Tana tsoron hakki ya bibiyi rayuwarta, gara ya mata hukunci irin wanda yayima Salamatu.

Ranar Alhaji malam yayi kuka, ya kuma yi tur da halin da bai san ya akayi ya ɗauke shi ba, amma jin asiri ne yasha mamaki kama shin da yayi, amma ba abin mamaki bane, tunda ya ci Annabi s a w. balle shi.

Sai dai ta ɗauka lamarin zai tsaya a nan, bata taɓa tsamanin zai shafi ƙiyayar mahaifinta ba.

ko wani ɗan Adam yana tare da ajizaci, wanda shine ya ƙaddara ma Alhaji malam sakin Umma ba tare da yayi bincike ba.
Sai dai Hafsa ta gaza fahimtar wanan ƙaddararsu ce cikin rubutaccan al’amarinsu.

Numfashi Ummah ta ja tana share hawayen da ya gangaro akan fuskarta “Ya Allah ka tausasa zuciyar Hafsa ta koma mai sanyi a gidan mijinta. Ka rabata da wanan mummunan ɗabi’ar da take ƙoƙarin ɗaukanta.” Ta faɗa tana ɗaga hannayenta sama.

Sanan ta tashi ta futo tsakar gidan, a haka aka ci gaba da gudanar da shagalin biki, kowa na musu murna da barka da arziqi akan mijin da Hafsa ɗin ta samu, wanda da yawa ‘yan mata ke burin ace su ne suka same shi a matsayin mijinsu.

Ka sancewar Alhaji Malam baya son wada bidi’a tun a daren ya kira Hafsa ya mata nasiha mai ratsa jiki sai dai yanda nasihar take shiga haka take fita kamar kaɗawar iska a kunnuwanta.
Har ya gama surutunsa da take ganin kamar surkulle ya ke mata ta kaɗai jikinta ta tashi “Nagode Alhaji da zaɓa min miji na gari da kowa ke faɗa. Amma ina fatan ka faɗa masa labarin ko wa ka aura masa, dan ni ban yarda da kalmar nan ta mace tayi haƙuri namiji ya cuceta ba.” Tana gama faɗar haka ta share hawayen fuskarta ta fuce tabar ɗakin.

Baki buɗe Alhaji Malam ya ke kallonta har ta ɓacema idonuwansa, ya kasa tunanin matsaya guda ɗaya, kamar yanda fargaba da tsoro ya cika zuciyarsa. “Ya Allah kada ka jarrabe ni da abun da yafi ƙarfina.” Ya faɗa cikin rawar muryarsa.

Acan kuwa Hafsa tana futa ta shige motar ɗaukan amarya, idanuwanta fes babu alamun hawaye a cikinsa, sai dai wani ƙunci da ke ziyartar zuciyarta.
Tasha ji ana cewa mace gajeriyar rayuwa ke da ita, ba zata sake ta wala yanda take so ba, sai a ƙarƙashin kulawar namiji. Sai dai a gareta ta musanta hakan, ita zata sabunta wanan labarin, domin ba kamar sauran mata ba ce ita, asalima tana da dogon buri. Burin yin rayuwa mai cike da armashi, ba wai ta ƙare rayuwarta a ƙarƙashin namiji ba. Tana da sabon karatun da zata koyar da maza su fahimci ko wacece mace.

Har aka kawota gidan tana saƙa da warwara, sai da gwaggonta ta buɗe mata ƙofa ta ruƙo hannunta sanan ta fahimci sun zo gidan, ba laifi tun a ƙofar gidan zaka fahimci gidan na zamani ne, domin yasha fantin da kalar milk da cofee a ƙofar gidan.
“Ki shiga da bismillah sanan kiyi addu’ar kauda sharri a cikin gidan kamar yanda musulunci ya koyar da mu.” Gwaggonta ta faɗa mata tana riƙe da hannayenta da kuma tsayawa a ƙofar gidan alamun jira ta ke ta yi addu’ar kafin ta shigar da ita gidan.

Murmushi tayi tana kallon ƙofar gidan “Gwaggo ai nice sharrin, me zai sa na kori kaina bayan na bayyana?” Ta faɗa tana kallon Gwaggon da itama take kallonta baki a buɗe.

“Ke ban son shashanci, ki yi addu’a mu shiga gida.”

Kawar da kanta tayi daga kallon Gwaggon nata, a hankali ta buɗe bakinta ta fara yin addu’ar.

Hafsa tana da ilimi sosai, duk a gidan Alhaji Malam itace macen da ta amsa sunanta, ko malam da kansa zai bugi ƙirji akan Hafsa zakaran gwajin dafi ce a fannin karatu.

Bayan ta gama addu’ar ta zura ƙafarta ta dama ta shige gidan, hakan yasa sauran masu take mata baya suka bita.

Har gaban gadonta Gwaggo ta kaita “Ki zauna da amincin Allah. Allah ya albarkaci rayuwar aurenki, ya kaɗai fitina a cikinsa.
Dan Allah ki zama mai haƙuri da ladabi da biyayya a gidan aurenki Hafsa, nasan kina da ilimin addini, shi kaɗai ya isheki ki samu nutsuwa a cikin rayuwar aurenki.

Mijinki masani ne kamar mahaifinki, Allah ya zaɓeki ya fidda ke daga hannu mai kyau, ya mayar da ke cikin mafi kyau. Ki cika gidanki da ƙamshin aminci, ki kunna futular hasken da zata haska zuciyar mijinki.”

Kai ta gyaɗa murmushi na sauƙa akan fuskarta “Nagode Gwaggo.” Ta faɗa cikin sunkuyar da kanta a ƙasa.

Daga haka Gwaggo ta tattara ‘yan rakiyar amarya suka fara tafiya da shiga motar ɗakin amarya.

Ruƙe hannun Gwaggon tayi wani munafukin hawaye ya gangaro akan idanuwan Hafsat “Gwaggo dan Allah kada ku tafi ku barni ni kaɗai anan.”

“Ki yi haƙuri Hafsatu kowa da haka ya girma, ina amfanin mu zauna goɗai-goɗai a gidan surikinmu? Wanan shine girman ai Hafsatu.”

“Ni bana son wanan girman Gwaggo, dan Allah ku maida ni gida.”

“Ba kya so gobe mu dawo mu ganki kenan?”
“Ina so Gwaggo.”

“To ki barmu mu tafi, na miki alƙawarin gobe zaki ganmu harda wasu ma da baki zaci zuwansu ba.”

Sakin hannun gwaggon tayi ba tare da ta mata magana ba, ganin hakan yasa Gwaggon ta juya da sauri ta fice a ɗakin nata.

Murmushi Hafsa ta yi tana share hawayen kan fuskar ta “Haba yaushe zan ɓata hawayen kan fuskata akan wani aure. Dama lamfo nayi kada akai ni gaba ace banyi kuka ba da aka kawo ni gida.”

Ta ƙarasa maganar tana sakin wata dariya mai sauti.

Ta ɗauki tsawon lokaci a haka kafin ta miƙe ta fara zagaye ɗakin, wani zafi da ƙunci take ji yana sauƙa a zuciyarta.

Dai-dai lokacin kuma ta fara jiyo sautin maganar maza, hakanne yasa ta yi sauri ta zauna a tsakiyar gado ta lulluɓai kanta da mayafi.

Can bayan wani lokacin kuma taji an murɗa ƙofar ɗakin nata, a hankali take jin takun takalminsa da kuma ƙamshin turarensa na cika mata hancinta.

“Amaryata bakya laifi.” Ya faɗa cikin tattausar muryarsa.

Zama yayi a kusa da ita, yana ƙoƙarin ɗage mayafin da ke kan fuskarta, saurin riƙe hannunsa ta yi ba tare da ta ɗago ba “Kafin ka samu ganin wanan fuskar akwai buƙatar ka biya kuɗin ganinta.”

Murmushi Abdul-mannan yayi “Duk sadakin da na biya har sai na sake biyan wani Kuɗin na ganin Fuska Hafsat? Ai komi da ke gareki ya halatta a gareni tun lokacin da na biya sadakinki shedu kuma suka sheda da hakan.”

“Sadakin da ka biya na ƙulla alaƙa tsakanina da kai ne, amma ba na kallon fuskata kullum ba.”

Murmushi yayi yana tashi akan ƙafafuwansa da tuƙo hannayenta “Ki zo muje falo ga su Yasir na jiranmu dan mana nasiha.”

Sauƙowa tayi daga kan gadon “Matsalata da auren malami kullum cikin nasiha. Duk kalar wa’azin da aka sauƙe min a wanan auren bai wadace ku ba har sai kun sake min wani.”

Juyowa yayi yana kallon Hafsan maganar da zai yi ma ya kasa, kasancewarsa mutum mai shuru-shuru da haƙuri.

“Kema ina da labarin malamarce ai, kinga kenan zamu yi haɗaka wajen yin abu ɗaya.”
A haka suka futo falon. Yasir ya fara magana “Kai kuma daga kiran amarya sai ka shanya mu? Gashi har kun cinye mana lokacin namu.”

“Ayi haƙuri, kunsan aamarya akwai sarauta.” Abdul-mannan ya faɗa yana haɗe hannayensa waje ɗaya.

“To ya zamu yi ai dole mu yi haƙuri. To a gurguje dai nasihar da zamu muku kun riga da kun santa, amma duk da haka zamu ƙara muku da nasiha akan kuyi haƙuri da juna. Haka kuma ku kare sirrin junanku, dan a yanzu babu wani wanda ya kaiku kusanci da junanku.

Lallai duk abu mai kyau yana farawa ne daga tushensa na asali, kenan zaku gina rayuwar aurenku da nagarta da kuma yakanah a cikinta.

A ƙarshe muna ƙara muku nasiha da kuji tsoron Allah a zaman takewar aurenku, Allah ya amintar da ku da samun kyakkyawar rayuwa, da kuma albarkar aure.”

“Ameen ya rabb.” Sauran abokanan nasu suka faɗa, daga nan Yasir ya rufe musu da addu’a bayan ya tambaye su ba mai magana suka amsa masa da babu.

Daga haka suka fice suna tsokanarsa bayan ya musu rakiya zuwa ƙofar gida,daga bisani kuma ya rufe ƙofar ya dawo gida fuskarsa ɗauke da fara’a.

Sai dai abun da ya bashi mamaki ganin Hafsat zaune ta cire mayafin da ke kanta, ta janyo ledar kaxar da ke gabanta ta fara ci “Me yasa baka zaɓo min kazar da ta fi wanan girma ba? Tun yanzu ka fara nuna min tsumulmular da zaka fara min a gidanka.”

Tsayawa yayi cak ba tare da yayi magana ba yana kallonta…

<< Jini Ya Tsaga 3Jini Ya Tsaga 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×