Ya ɗauki lokaci mai tsawo yana zaune yana maida numfashi, kafin daga baya ya tashi yana riƙe da mararsa da ta ƙulle tun bayan zagaye masa fuskar da Hafsat ta ke yi.
A hankali ya shiga ɗakinsa ya kwanta a kan gado, jin zuffa na jiƙa ƙara tsattsafo masa daga jikinsa ya sha ya shiga toilet ya sakawar kansa ruwa. Ajiyar zuciya ya sauƙe mai ƙarfi, jin ruwan na huda ko wata ƙofa ta jikinsa.
Murmushi ya yi a lokacin da idanuwansa suka shiga hasko masa abin da ya faru tsakaninsa da Hafsa 'Hafsa rigima.' Ya fa. . .