Skip to content
Part 9 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

Ya ɗauki lokaci mai tsawo yana zaune yana maida numfashi, kafin daga baya ya tashi yana riƙe da mararsa da ta ƙulle tun bayan zagaye masa fuskar da Hafsat ta ke yi.

A hankali ya shiga ɗakinsa ya kwanta a kan gado, jin zuffa na jiƙa ƙara tsattsafo masa daga jikinsa ya sha ya shiga toilet ya sakawar kansa ruwa. Ajiyar zuciya ya sauƙe mai ƙarfi, jin ruwan na huda ko wata ƙofa ta jikinsa.

Murmushi ya yi a lokacin da idanuwansa suka shiga hasko masa abin da ya faru tsakaninsa da Hafsa ‘Hafsa rigima.’ Ya faɗa a ƙasan laɓɓansa yana shafa sajen fuskarsa.

Shi har mamakinta ya ke yi, da ace ba shi ne ya ɓareta gal a leda ba da babu abin da zai hana shi ya yi tunanin ta yi zama da gogaggu mata fitinannun da ba sa jin magana.

Sai dai ya riga da ya san ko ita wacece da kuma gidan da ya ɗauko ta.

A hankali ya fito daga toilet daga shi sai farin tawul da ke sarƙafe a ƙugunsa, farar jallabiya ya sa a jikinsa sanan ya mayar da tawul ɗin ma’ajiyarsa sannan ya dawo ya shimfiɗa sallaya ya gabatar da sallah nafila kafin ya kwanta.

Bayan ya idar ya fara karatu daga kan abin sallar barci ya ɗauke shi, barci mai ciki da takura da mafarkai marasa kan gado.

******
Washe gari kiran sallahr assalatu ne ya farkar da shi, hakan ya sa ya tashi, yayi mamakin ganin in da ya kwana ko ina na jikinsa yana masa ciwo.

A gaggauce ya shiga toilet ya yi wanka sannan ya ɗaura alwala ya fita masallaci, ya so tsayawa a ƙofar ɗakin Hafsat amma yasan zai iya ɓata lokacinsa ne a iska har shima ya makara.

Kasancewar shine limamin masallacin unguwar yana zuwa ya jagoranci sallah.
Bayan ya idar sai da ya tsaya ya musu wa’azi akan abin da ya shafi rayuwa kamar yanda ya saba yi musu.

Ƙarfe shida da rabi aka shafa fatiha kowa ya kama gabansa, shima ya taho gida, yana taku zuciyarsa na bugawa, saboda tunanin wata kalar sabuwar masifar kuma yau zai tadda.

Sai dai da mamakinsa tun daga falon nasu ya ke jiyo sautin karatun Alqur’ani mai girma, da wata zazzaƙar muryar da yake jin tana amsa ko wani sashe na jikinsa.

“Ya Allah! Wannan wani sauti ne mai daɗin gaske haka?” Ya samu faɗa a ƙasan laɓɓansa, a hankali kuma ya fara cira takunsa yana nufar inda ya ke jin sautin na ta shi.

Ɗakin Hafsat ya nufa da ya ke jin sautin na ta shi, murɗa ƙofar ɗakin ya yi cikin sa’a ƙofar ta buɗe hakan ya sa ya cusa kan sa ɗakin.

Tsayawa ya yi yana wara idanuwansa, ganin Hafsat ce zaune akan abin sallah idanuwanta a lumshe ta jingina da jikin gado tana zazzaga ƙira’ar karatun ba tare da ta buɗe alqur’anin ba.

Idonsa ya murza da tafukan hannunsa ya ƙara ganin tabbas dai HAFSA ɗin ce ke hadda da ka. Ajiyar zuciya ya sauƙe a karo na farko mai sanyi, yana jin wani abu na ɗarsuwa tun daga yatsan ƙafarsa har zuwa kansa.

“Alhamdulillah ala kullu halin! Masha Allah!” Su ne kalmomin da ya shiga mai-maitawa, yana ɗaga ƙafarsa da matsowa kusa da ita.

A jikinta ta ji cewar ana kallonta, ƙamshin turarensa kuma ya sanar da ita shi ɗin ne dai ya dawo.

A hankali ta buɗe idanuwanta tana ɗora su a kansa, ganin ya ƙura mata ido yana murmushi da kuma lumshe idanuwansa a kai-akai ya sata ambaton “Sadaƙallahul Azim.”

“Allahu Akbar!” ya faɗa yana murmushi da matsowa kusa da ita, ya ɗora hannunsa a kan ta.

“Allah ya albarkaci rayuwarki Hafsa. Na gode.” Ya faɗa yana ƙara shimfiɗa murmushi a kan fuskarsa.

Murmushi ta yi itama tana janye hannunsa daga kanta, sannan ta miƙe a kan ƙafafuwanta.

“Ina jin babu daɗi a duk lokacin da na ga kana murmushi haka Abdul. Sai dai idan na tuna cewa wata dama ce na baka, damar da na ke fatan ka min gini da wani kakkauran tubalin da iska, ko ruwa bai narkar da shi. Har zuwa lokacin da zan buƙaci sauƙar da shi, sai na ji hakan ya min.”

Risinawa ta yi kusa da saitin kansa ta haɗa goshinta da nasa tana goga tsinin hancinta da nasa “Adadin wani lokaci kake so na ɗaukar ma wanda zaka ci gaba da sa min albarka irin haka?”

Idonsa ya lumshe jin wani abu na tsikararsa da abin da take masa da kuma maganar da ta ke masa, ga kuma ƙamshin turaren ta na bugar hancinsa da ya ke jin har zuciyarsa na bugawa.

Fincikota ya yi ta faɗo jikinsa, sannan ya mirgina da ita zuwa kan gadon, ya mata rumfa da faffaɗan jikinsa, har a lokacin idanuwansu na sarƙafe da na juna.

“Ba ke zaki ba ni lokacin nan ba Nahna! Idan har zan yi tsawon rayuwa ina mai tabbatar miki bakina ba zai gaji da sa miki albarka ba.”

Idonta ta wara sama da ƙasa ta ɗan yi murmushi wanda iya karsa kan laɓɓanta ne “Idan kuma muka rabu fa?”

Hancinsa ya goga a kan nata, kafin nan ya hura mata iska akan idanuwanta “Ban da sani akan ilimin gaibu da kuma hasashe akan abin da zai faru a gobe.

Amma ina mai tabbatar miki ko da rayuwa zata sauya, yanayi ya juya ta hanyar hargitsa shimfuɗaɗɗun layika masu kyau da nagarta, su koma kamar tsutsotsin da suke ɗauke da munanan rubutun da ba sa karantuwa. Zan yi murmushi zan kuma gode miki, zan yabe ki da baki zaɓi akan abin da kike so muddum hakan zai sa ki dariya.”

Idanuwanta ta lumshi tana jin yana sauƙar mata da kasa, tana jin kamar zuciyarta na son kaita ta baro ta, duk da bata shirya hakan ba.

Hannunta ta sa ta ɗora akan Laɓɓansa “Ka yi shuru Abdul! Kada ka yi maganar da idan lokacin cikarta ya zo ka kasa cikata. Kada daɗin yanayin nan ya sa ka ji kamar za mu dauwama a haka ne, har ka yanke hukunci akan mummunan goben da ba ka shirya mata ba.”

Hannunta ya janye daga gare shi ba tare da ta shirya ba sai jin bakinsa ta yi cikin nata, yana sarrafa harshensa a cikinsa.

Ƙananun idanuwanta ta zaro waje sai dai bai kula da ruɗin da ke cikinsa ba, ya ci gaba da sarrafata dai-dai son ransa, har sai da ya sauƙe dukkanin abin da ta ɗora masa a kwanaki biyun.

Sai da ya samu gamsuwar jiki da ya zuciyarsa sannan ya kwanyar da ita akan cikinsa, da take jin kamar zata iya cizge fatar jikinta da duk wani sassa na jikinta.

Karo na biyu wani sabon Hawaye ya sake gangarowa daga idanuwanta, hawayen takaici da kuma rashin sanin madogarar da zata kama.

Bata farga ba ta ji sauƙar hannunsa akan fuskarta yana share mata hawayen da ke sauƙa akan fuskarta. “Rayuwa ba zaɓen gold ba ce a kasuwa, balle ka ɗaga ka juya shi ka zaɓi wanda ya ma. Hakan ya sa ƙaddara kan zama tsani da shimfiɗa matakalai ga ko wani ɗan Adam.

Na tabbata ba ni ne zaɓinki ba, amma zan gamsarwa da zuciyarki cewar ‘Ni kaɗai ne mutumin da zai ƙawata miki duniyarki’ Ina son ki! Zan ci gaba da son ki har gaba da Abadan.” Ya ƙarasa maganar yana sumbatar hannunta, da kuma ɗaukanta cak suka shiga Toilet.

Tare suka yi wanka sannan ya futo ya barta ta samu ya yi wankan tsarki.

Kai tsaye ya fice zuwa kitchen ganin 9:02am har ta yi, ƙarfe goma yana da ɗalibai.

Abin da ya ba shi mamakin ganin abinci a jere a cikin filas. Kai ya girgiza yana murmushi, yana ji a ransa Nahna Hafsa ta sauya.

A gurguje ya shirya cikin wani farin yadi mai taushi, da shara-shara kasancewar yanayin damina garin. Ya ɗora hula a kansa, fuskarsa ta yi fayau ta ƙara haske, wanda ke nuna tabbacin yana kan Angoncinsa.

Dai-dai fitowarsa itama ta futo cikin farar atamfa ma ratsin da gold, ɗinkin riga da siket ne ya kamata ya futo da ita ɗas.

Babu kwalliya a fuskarta sai kwallin da ta sa da ɗan farin man baki. Sai ɗankwalin da ta ɗaura ta turo gabanta.

Fuskarta da murmushi kamar ba ita ce ta gama kukan ba.

“Masha Allahu laƙuwata illah billah!” Abdul ya faɗa akan laɓɓansa yana murmushi.

Ɗan sama ta yi da idonta tana juyawa, a hankali ta fara takowa zuwa gabansa, sai da ta matso saitinsa sannan ta ja dogon numfashi, kafin ya farga ya ji ta sumbace shi a kumatunsa.

Ido ya waro waje wanda hakan ya sata murmushi da kanne masa ido ɗaya “Ka yi kyau sosai a ido. Amma ban ji a zuciyata ka yi kyau ɗin ba.”

Murmushi ya yi mai sauti har tana ganin jerarrun haƙoransa “Na gode! Allah ya miki albarka da wannan Sumbatar da kika min sai na ji na ƙoshi daga dukkanin yunwar fa ke kawo min farmaki.”

Kujera ta ja masa tana nuna masa “Ka zauna dai, karo na farko ka ci abincin Amaryarka, daga nan sai ka gode min da ƙara sa min albarka. Wata ƙila ya kasance shine lokacin da zaka fi sauƙin tunawa da jin alfahari a zamanmu da kai.”

Idonsa ya ɗaga yana kallonta kamar yanda itama ta ke kallonsa, So ya ke ya ce wani abu, kamar yanda zuciyarsa ta hautsine da bugawa da ƙarfi.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Jini Ya Tsaga 8Jini Ya Tsaga 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×