Har zuwa lokacin da motar su ta tsaya a ƙofar gidan Abdul Mannan bata san sun ƙara so ba, sai da Adda Halima ta mata magana sannan ta dawo hayyacinta.
Da taimakonta ta shiga cikin gidan, tana ganin kamar ya sauya mata a cikin makwanni biyu da ta yi bata gidan.
Sun daɗe a gidan suna hira da ƙoƙarin ganin sun faranta mata, har zuwa yammaci sakaliya, Adda Halima ce ta musu girki da kima farfesun kayan cikin da Sayyadi ya kawo musu. Sai da ta gyara gidan da ko ina sannan suka tafi, suna mata fatan samun. . .