Skip to content
Part 13 of 41 in the Series Jini Ya Tsaga by Oum Nass

Har zuwa lokacin da motar su ta tsaya a ƙofar gidan Abdul Mannan bata san sun ƙara so ba, sai da Adda Halima ta  mata magana sannan ta dawo hayyacinta.

Da taimakonta ta shiga cikin gidan, tana ganin kamar ya sauya mata a cikin makwanni biyu da ta yi bata gidan.

Sun daɗe a gidan suna hira da ƙoƙarin ganin sun faranta mata, har zuwa yammaci sakaliya, Adda Halima ce ta musu girki da kima farfesun kayan cikin da Sayyadi ya kawo musu. Sai da ta gyara gidan da ko ina sannan suka tafi, suna mata fatan samun lafiya.

Ya yin da Adda Halima ke tabbatar mata da cewar zata wuce Sokoto a gobe idan Allah ya amince, ba zata samu damar zuwa yi mata sallama ba.

Godiya ta musu sosai ta rako su har ƙofar gida tana ɗaga musu hannu, sai da ta ga tashin Motar Sayyadi da ɓacewarsu a kan idanuwanta sannan ta koma cikin gidan.

Zama ta yi a kan kujera tana jinginar da kanta a jikin kujerar da kuma lumshe idanuwanta.

Abubuwa masu yawa suna ta tseren shiga kanta, tana tufka tana warwarewa domin rashin samun matsaya guda ɗaya.

Hannunta ta ɗora a kan shafaffen cikin tana jin ƙaunarsa, tana jin nauyin kasancewarsa a tsakanin wasu ƙaddarori da take da yaƙinin zuwansu, a kusa ko kuma a nesa.

Tana jin kamar ta sadaukar da farin cikinta saboda samuwar walwalar abin da ke cikinta.

Ya daɗe tsaye a kanta yana kallonta, yana ƙirga adadin hawa da sauƙar numfashinta ba tare da ta san da zuwansa ba.

Bai san tunanin me take haka mai zurfi ba. A hankali ya fara ajiye takunsa yana ƙarasowa kusa da ita  har ya yiwa kansa mazauni a kusa da ita, ya ɗauki hannunsa guda ya ɗora a kan nata hannun da ke kan cikinta.

A hankali ta buɗe fararen idanuwanta ta ɗora su fes a kansa, kamar yadda shima yake kallonta, tana iya hango adadin ƙaunarta a cikin idanuwansa, tana kuma iya hango adadin tausayawarsa da girmamata da yake yi.

Idanuwanta ta lumshe ta buɗe su tana kallonsa “Ban san me nake ji a kanka ba, Sayyadi. Amma duk lokacin dana kalli idanuwanka sai na ji ina son na ƙare rayuwata a tare da kai. Sai naji kamar rayuwata ta zaɓar min kai ne a matsayin tsanin takala duk wasu matakan nasarata. Ban ɗauka a tare da kai zan samu wannan abin da nake jin sonsa da kuma rashinsa a lokaci guda ba.”

Kansa ya kwantar a kan kafaɗarta wadda ya sata juyowa ta kalleshi, a hankali ya sauƙe ajiyar zuciya yana fitar da iska daga bakinsa.

“Me yasa kike tunin ba zamu ƙarar da rayuwar mu a tare da juna ba? Me yasa ji kawai kike a yi hakan? Madadin ki ji mu tabbatar da amincin junan mu na har abada mana.” Ya yi maganar yana ɗago da kansa da kallon fuskarta.

“Ni ba irin matar da ta dace da kai ba ce Sayyadi. Ina da banbanci na halayya da ɗabi’a da bata da tabbas, ba ta kuma da kyau.”

“Ni ne mafi cancanta da ke, Nahna! Domin ko sau ɗaya ban taɓa jin rashin kyau ko rashin dacewa na ɗabi’arki ba. Ni ke nake so da kasancewa tare da ke har ƙarshen rayuwa. Halayanki kuma ɗabi’a ce wadda nake kyautata zaton gyaruwarsu ko sauya su a tare da ke, amma hakan ba zai dame ni har na ji lallai dole sai kin sauya ba kafin na rayu da ke.”

Kallon sa ta yi, a wannan lokacin bata da amsar da zata bashi, bata jin ma akwai sauran kalma da ta rage da zata masa magana ya fahimce ta. Abdul ya yi nisa, nisa na sosai da take da tabbacin ba zata kira shi ya ji ba, ba za ta buɗe idanuwansa ya fahimceta ba.

“Lokaci zai tabbatar mana da hakan Sayyadi. Shekaru uku masu zuwa idan muna raye.”

Ta yi  maganar tana kai bakinta goshinsa ta sumbace shi, wadda hakan ya tsayar da maganar da yake shirin yi mata.

Kafin ya dawo daga inda ya ke ta zame hannunta ta ɗora nasa a kan cikinta daidai ƙasan mararta “Kana jin bugawar zuciyar yaronka?”

Shuru ya yi yana kasa kunne ‘Wata biyu da sati biyu ta ya zai ji motsin yaro?’

“Oh ashe fa ba zaka ji ba Sayyadi. Ni kaɗai zan ji a yanzu. Akwai wahala, akwai mutuƙar wahala rayuwar wani a cikin wani, akwai rauni da kuma ƙarfin zuciya ga wadda aka ɗorawa nauyin zama uwa.

Haƙiƙa Allah mai hikima ne da buwaya, da ya tsara halittar rayuwar wani a cikin wani.” Ta yi maganar tana ɗora hannunta a kan nasa hannun da yake kanta.

Kan sa ya jinjina cikin gaskata maganar ta, yana kuma da yaƙini akan kowata kalmarta tafe take da gaskiya, gaskiyar da ba a sauyata ba kuma a sirkata.

“Shi yasa kuma Allah ya sa soyayya da shaƙuwa tsakanin uwa da yaranta. Ya kuma bawa Uwa daraja mafi girma  a kan yaranta. Kalmar uwa a kan ɗanta wanzazziyar kalma ce da bata tsayawa. Tun yara suna ciki ake son uwa ta fara musu addu’a ta gari, ta kuma nema musu kariya da shiriya ga Allah. Domin Addu’arta na tafiya kai tsaye ne ba tare da samun gargada ba.”

Hannunsa ya ɗora a kanta yana kallonta da lumsassun idanuwansa da basa buɗewa gaba ɗaya “Nahna yanzu ke uwa ce. Kin samu soyayya da ƙauna ga ahalinki, ina fatan wannan ma zai samu soyayya fiye da wadda ahalinki suka miki?”

Kanta ta girgiza masa tana kallon cikin idanuwansa “Wannan naka ne Sayyadi. Sai dai zan ci gaba da riskar da kyakkyawar kalmata daga duk inda na ke.”

Miƙewa ta yi tsaye yana binta da kallo “Kar ka ga ban ciri kuɗin asusun bankin ka ba, ka ɗauka na yafe Sayyadi. Zan jira zuwa lokacin da kuɗaɗen za su cika adadin rabin abin da na tambaya sai na ɗauka.” Daga haka ta juya tana shigewa ɗaki yana binta da rakiyar ido.

QBa wai sabon abu ba ne yake gani a wajenta ba, a a yana ganin saurin juyewarta ne, yana kuma daidaita kowata kalmarta da nema mata wajen ajiya.

Sai dai kalaman Hafsa kan zo masa a jirkice da ruɗaɗɗun kalamai da sai ya ɗauki lokaci yana nazarin su. A ƙarshen nazarin kuma ya tashi bai fahimci komai ba sai tsagwaren shirme.
Bayan Watanni Uku

Bai yarda zata iya yin amafani da kuɗin ba, har sai da ya ji an masa saƙo a bankinsa, ya bi wayar da kallo yana ganin an cire kuɗaɗen cikin asusun bankin gaba ɗaya.

Kafin ya dawo daga karanta saƙon yaji wayartasa ta yi ƙara alamar shigowar saƙo, ganin sunan _*Nurul Khair*_ A jiki ya sa shi buɗe saƙon.

_’Ina tsoron jiran gawon shanu. Kada na je garin jiranye na ji ɓallewar jinga. Na ɗauka daga abin da ya rage ga Sayyadin mijina, na kuma yafe sauran dan nasan ba za su fito da kyau ba._

_Hafsat Kamaludden Muhammad’_

Ya karanta saƙon fiye da adadin da zai iya karantawa, kafin ya yi murmushi ya mayar da wayar aljihunsa, yana ci gaba da bada karatu ga ɗaliban da ke gabansa.

Har zuwa lokacin da ya gama ya tafi gidan ya ganta zaune da kayan marmari a gabanta, ga kuma remote a hannu tana sauya channel. Cikinta ya turo ya yi tirtsitsi a gaba, sai  ka ɗauka yau zata haihu.

A hankali ya ƙarasa kusa da ita ya ajiye litattafansa a kan kujera, ya miƙar mata da ƙafarta ya fara mammatsa mata ƙafar.

A hankali ta fara yamutsa fuskarta tana jin daɗin tausar da yake mata. “Da kin faɗa min zaki yi amfani da kuɗin ai da na ciro miki, da baki wahala haka ba. Ke da kika je asibiti awu. Kuma na faɗa miki ki kirani idan kin gama na ɗauko ki na dawo da ke.”

A jiye cokalin da ke hannunta ta yi tana kallonsa “Oh dan na ɗauki hakkina ne kake min mita a fakaice? Ina da ma an daɗe da maganar kuɗin.”

Kai ya girgiza yana tsiyaya tacacciyar madarar da ke gabanta, wadda ta ke da sanyi ba sosai ba “Ni ba matsalata a kan waɗannan kuɗaɗen ba ne. Ina damuwa ne da lafiyarki da kuma duba kowanne motsin ki.

Kuma dai ban ga ma laifinki ba da kika buƙaci kuɗin rainon cikin, duba da tarin wahalar da ke tare da dakonsa. Allah na tuba ni ko da kuɗi ma ai ba zan iya ba. Jinjina ga jarumar matata.” Ya yi maganar yana jinjina mata babban yatsansa.

Wadda hakan ya sa ta kalle shi. ‘Shin anya Sayyadi ya cancanci kowanne tasgado daga gareta?’ Ta tambayi kanta kafin ta zamar da kallonta zuwa ga allon Tv da ke jikin bango.

“Ya kamata ka je ka yi wanka ka ci abinci Sayyadi.” Ta yi maganar a hankali.

“Ƙafafuwanki sun kumbura Nahna, da buƙatar na taimaka miki su huce. Idan ina kallonki bana jin gajiya, bana jin yunwa a tare da ni.”

“Kada ka zurma da yawa.” Ta yi maganar tana janye ƙafafuwanta da tashi a hankali, wadda sai da ya taimaka mata ta miƙe, sannan ta riƙe hannunsa ta ja shi har zuwa ɗakin, yana kallonta kamar raƙumi da akala.

Ita ta cire masa kayan sannan ta shigar da shi toilet ɗin.

“Ka yi wankan ko kuma ni na zo na ma?” Ta yi maganar tana matse fuska da kuma turo ƙaramin bakinta.

Hakan ya sa ya kalli turtsetsen cikinta da da kuma kallon fuskarta, yana son dariya yana tsoron ya ɓata haɗaɗɗen zaman da aka nuna masa a yau ɗin.

<< Jini Ya Tsaga 12Jini Ya Tsaga 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×