Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Kabari by Ummu Adam

Bissimillahi da sunan rabbana na fara mai duka mai komai hakika, masani yau da kullum da dukkan sirri gare ki

Yau dai na kai ziyara na ganewa idona wa’azi gare ki to Allahu ya sa na gyara

Kabari ba ki ga babba ba ki ga yaro

Kabari ba ki ga gado ba ki ga katifa

Dana tino da ke sai na ji duniya sam babu nauyi gareni

Bawa na kashe milliyoyi ga daki ya mance makwanci gare shi ciyawa karmami gareshi baya fidda sule a gyara.

Haba hajiya sassauto da buri super ko England wax basu zuwa kabari gare ki balle suyi ceto gare ki

Ita zuciya buri da damuwa gare ta maganinta sallah ko salati dan jannah sam bata kai ziyara

Kabari ba kiga babba ba kiga ga yaro

Kabari ba kiga mai kuddi ba kiga tallaka duk tsiya dai nan zaka koma

Kullum mutane na ziyarta shin basu ganin wataran su za’a kaima to mene daɗin ka tara

Kabari ba’a zabar gari gareki, ba’a zabar unguwa gareki, ba’a zabar makwabci gareki

Bawa kaɗe ƙura ga shimfida ga ƙasa nan ga kabari babu daman kakkaba

Kowa ka ganeshi nan kaishi ankai, komai ka gani cikinga da shi ka jena

Kabari ba ki ga babba ba ki ga ga yaro

Kabari ba ki ga bako ba ki ga dan gari kowa gareki zuwa yake

Ruwa ka daka, rana ka buga, iska ka zezeye har watarana kamar ba kai guringa

Kabari makwancin na tsaye dana kwance idan tai kyau kaina ka gyara idan ta yi muni shuka ka girba

Kabari makwancin uba da dansa, makwancin zuriya da dangi, wanga gida na dakon wande bai nan duniya ina ga kai wagga agga cikinta

Kabari ba ki ga babba ba ki ga ga yaro

Kabari makwancin uban gida da bawa

Shin bawa ya san dake yake haɗama ga dukiya, mulki harda ɗagawa

Shin me shirka labarinki bai je ga kunnuwansa bane?

Ina ga matsafa, mahandama ga dukiyar maraya shin basu idda jana’iza ne?

Kabari makwancin masoyi da abar ƙaunarsa, kina dakonmu muna gudu, kina kira Muna tushe kunnuwanmu wai bamu so mu juyo gare ki

Kabari ba ki ga babba ba ki ga ga yaro

Wasu kwance gare ki wasu kwance ga mashaya na watsa nera ga kilaki shin basu idda jana’iza ne?

Kabari da an kai sai kaji ana an dawo shin ba’a barin matayin zama gareki ne?

Kabari mai yalwa da ƙunci, ba kiga babba ba kiga ga yaro

Bawa baya sanin muhimancin lokaci sai ya ji daga na kwance gareki sai dai kash babu dama gare shi

Kabari bakiga babba bakiga ga yaro.

Allah yasa yazamu yalwa garemu, rahama garemu, aminci garemu, aljannah ta zamu Makoma garemu, ya ji ƙan dukkan mamatanmu. Aamin.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×