Kamar Ruƙayyan na karantar zuciyarta ta ce, "Na yarda ba kowa ba ce ita, amma idan ya zama dole sai kin zauna da wani a gidan me zai hana ki sa a kawo miki gyatuma? Kai ni fa gyatumar ma ban yarda da ita ba wallahi, domin ita ma tana iya ɓullo miki ta wata sigar, Halisa ƙawata gyatumar ce ta shuka mata tsiya, ta zagaye ta haɗa mijin da jikar aminiyarta ta cuce ta a banza, namiji ai ba a sha masa alwashi."
Zubaidah ta ja tsaki "Matsalata da ke gurɓataccen tunani Ruƙayya, a kan. . .
Assalamu alaikum
Amin wa alaikassalam