Skip to content
Part 10 of 23 in the Series Kaddarar Mutum by Mustapha Abbas

Kamar Ruƙayyan na karantar zuciyarta ta ce, “Na yarda ba kowa ba ce ita, amma idan ya zama dole sai kin zauna da wani a gidan me zai hana ki sa a kawo miki gyatuma? Kai ni fa gyatumar ma ban yarda da ita ba wallahi, domin ita ma tana iya ɓullo miki ta wata sigar, Halisa ƙawata gyatumar ce ta shuka mata tsiya, ta zagaye ta haɗa mijin da jikar aminiyarta ta cuce ta a banza, namiji ai ba a sha masa alwashi.”

Zubaidah ta ja tsaki “Matsalata da ke gurɓataccen tunani Ruƙayya, a kan komai ma ke ba kya yin tunani mai kyau, ya za a yi kwanyarki ta riƙa buga miki irin wannan makakken lissafin? Wa ce ce Asma’u, me aka yi aka yi ta, meye a tare da ita da har zai ja ra’ayin Ma’aruf?”

Ruƙayya ta bi ta da wani irin kallo kamar ta ga sakarai, sannan ta girgiza kai cikin takaici. “Wawiyar banza! Har yanzu da sauran ki, to wallahi irin yadda ki ka raina yarinyar nan ba haka take ba, matsayina na mai ƙaunarki ina baki shawara tun wuri ki sallame ta ta koma gida, har wani aiki ne a gidan nan da zai gagare ki kamar wata ƙaramar yarinya?”

Zubaidah ta yi shiru alamun maganar ta so ta yi tasiri a ranta, sai dai har abada ba ta jin Asma’u za ta kai wannan bigiren, ba ta da wannan isar, kamar yadda hasashenta bai taɓa gwada mata haɗaɗɗe kuma gogaggen mutum kamar Ma’aruf ɗinta da wata ƙasƙantacciyar mace irin ta ba ‘For God sake’
“Kin ga Ruky ni fa ban ce miki yarinyar nan za ta zauna a gidan nan din-din-din ta ci gaba da min aiki ba, duka kwanaki nawa suka rage in rabu da wannan wahalallen cikin, sai ta koma inda ta fito so what?”

“To shi kenan ai.” Suka rufe wannan babin.
Asma’u ta fito hannunta ɗauke da kwalin lemon Civita mai sanyi da kofuna ta ajiye gaban Ruƙayya, dai dai lokacin wayar Ruƙayyan ta yi kiɗa, dubawar da za ta yi kuwa sai ta saki salati har tana firgita Asma’u. “K.B fa yana waje, shaf na manta da shi wallahi.” Ta faɗa. “Ya ba za ki manta ba, kin samu kinibibi kina yi ‘yar iskar mata. Asma’u je ki shigo da shi don Allah.”
Yana tsaye a harabar gidan jikin motar da suka zo da ita, babu yadda za a yi Asma’u ta manta fuskarsa, ta yi masa sallama haɗe da gaishe shi. Bai amsa ba ya ce, “Malama ashe kina nan?”

Asma’u ta gyaɗa kai sannan ta ce, “Sun ce ka shiga.” Ta juya ta wuce, yana biye da ita har falon, shi ma ya samu guri ya zauna, suka fara gaisawa da Zubaidah cikin barkwanci, Asma’u ta shige ɗakinta ta zauna, tana jin shewar su har sa’arda Doctor K.B ya tashi ya fita ya bar Ruƙayya a gidan da nufin sai ya dawo daga aiki ya biyo ya ɗauke ta su wuce gida.

Da yammaci ne bayan Ruƙayya ta tafi Zubaidah ta shigo ɗaki ta same ta, lokacin ta kammala cin abinci babu jimawa.
“Asma’u ɗazu na yi miki magana kan hijabi, kawai ki ci gaba da sa kayan ki musamman idan mai gidan nan yana nan saboda tsare mutuncinki, na san duk an koyar da ku a Islamiyya, ke idan yana nan ma ki daina fitowa sam, ki yi zamanki a ɗaki matuƙar ba nice na kira ki ba, don Allah ki ƙara haƙuri insha Allahu kin kusa komawarki gida, na san yanzu kina kewar su Hajiya da karatunki ko?”

Jinjina kai ta yi cike da gamsuwa, ta san dalilin Zubaidah na kafa mata wannan dokar, don ta saurari wani ɓangare na hirar su da ƙorafe-ƙorafen aminiyarta Ruƙayya kan zamanta a gidan, ita ma ko kaɗan ba ta fatan haɗuwa da mijinta, ta yi ƙoƙarin hana faruwar hakan da kanta tuntuni, don tun ranar farko da ta zo gidan kafin ya tafi Abuja ta ji muryarsa a falo lokacin tana kitchen addu’a ta riƙa yi a fili kada Allah Ya shigo da shi kitchen ɗin, domin Asma’u ta yi imanin faɗuwar gaba da tsoron da za ta ji idan suka haɗu sai ta ninka wadda ta ke ji yayin da ta ji muryarsa. Ta jima da toshe duk wata hanya da za ta haɗa su. Duk lokacin da yake gari zaman ɗaki ya kama ta, idan za ta shiga kitchen sai ta tabbatar yana sama kasancewar ɗakunan kwanansu a sama suke daga shi har matarsa, sai dai a rayuwa kana taka Allah na ta sa kuma bai zama lallai abin da mu ‘yan adam muka tsara wa kanmu ya tabbata ba. Abin da Zubaidah ba ta sani ba ko da ba a wannan duniyar ba, a wata duniyar daban Allah zai iya haɗa su.

Misalin ƙarfe shida da rabi na yammaci ƙarar wayar Zubaidah ta kauraye ko ina cikin falon, Asma’u da ke cikin ɗaki ta san Zubaidar ita ma tana cikin ɗakinta tana kwasar barci, alamun bata san ma wayar na qasa a falo ba. Yanzu ma da take zaune gefen gado bayan ta fito daga wanka kamar yadda ta saba kullum bayan ta kammala girka abincin dare ta kan shiga ta yi wanka ta dauko littafanta ta yi ta bita, tana jin wayar na sake amsa-kuwwa a karo na uku bayan ba a fi wasu gajerun sakwanni da ta tsinke ba.
A gaggauce Asma’u ta kammala shafa mai ta saka doguwar rigarta mai hula da Zubaidah ta ba ta ta fito falon da sauri, niyyarta ta ɗauki wayar ta kai hau sama ta kai mata ɗaki tunda ta ga alamun mai kiran na son samunta ko ta yaya, ga Zubaidah na da ɗan karen nauyin barci. Asma’u ta kai hannu ta ɗauki wayar kenan suka haɗa ido da Ma’aruf da tuni ya riga ya shigo falon da tasa wayar a kunne.

A iyakar saninta mijin Zubaidah ba ya gari sai dai ko yanzu ya sauka, don ga jakarshi nan rataye a kafaɗa, wannan ɗin kuma waye? Ta tambayi kanta tana dubansa.

Ma’aruf ya cire wayarsa daga kunne ya datse ta, take wayar Zubaidan ma da ke hannunta ta dakata daga kiɗan da take, kenan dama shi yake kiran. Tabbas mijin Zubaidah ne Asma’u ta yi tsaye cak da wayar a hannunta tana kallonsa.

Ya ƙaraso cikin takunsa na cikakkun maza lokaci guda kuma ya ɗauke kansa daga kallonta. “Ina me wayar ne? Tun ina air port nake kiranta fa.”

Durqusawa Asma’u ta yi har ƙasa tana miƙa masa wayar tare da faɗin “Tana cikin ɗaki, ina ganin barci take.” Bai karɓi wayar ba ya nuna mata inda ta ɗauke ta da hannunsa nufinsa ta ajiye ta kawai kana ya samu guri ya zauna cikin kujera yana ci gaba da latsa wayarsa, don haka ita ma Asma’u sai ta ajiye wayar hannunta ta juya da sauri za ta koma ɗakinta.

“Ji mana.” Ya faɗa da sassanyar muryarsa mai kama da rada, ko kadan ba shi da hayaniya, gashi kuma da alamu mutumin kirki ne. Asma’u ta yi tsaye cak! Faɗuwar gabanta ta ƙaru, ta juyo a hankali tana kallon inda yake zaune amma ko kaɗan ba ta bari sun haɗa ido ba duk da cewa shi kuma ita yake kallo. “Ba sannu da zuwa, ba gaisuwa ba komai, ko baki san ni a gidan nan ba?”

A nan inda take tsaye ƙirjinta na bugun uku-uku ta ce “Na sani mana.” Ya ɗan gyara zamansa kaɗan a kan kujerar, “Shi ne za ki tafi da gudu kamar kin ga dodo?”
“Ka yi haƙuri don Allah mijin Zubaidah.”

“No ni ba ki min laifin komai ba fa, ba buƙatar ki ban haƙuri, za ki iya kawo min ruwa in sha?” Girgiza kai Asma’u ta yi alamar amsawa, shi kuma ya mayar da hankali kan wayarsa, don haka ta samu damar shigewa ɗaki, hijabinta ta sako ta fito sannan ta zarce kitchen ta ɗauko ruwan roba da kofuna har da lemo ta dawo ta ajiye masa, ta yi amfani da damar don wanke laifinta, wato yi masa sannu da zuwan da ya yi ƙorafi.

Sai da ya ɗan ɗauki lokaci kafin ya amsa mata, ba tare da hakan ya dame ta ba ta juya ta koma ɗaki abinta, ko yaya dai yana da sauƙin kai, bai kuma raina darajarta ba, ma’ana a matsayin da yake kai za ta iya cewa ya mutunta ta, sai dai har yanzu ƙirjinta bai daina bugawa ba, kai tsaye za ta iya danganta faruwar hakan da tsananin ƙwarjinin da ya yi mata, bugu da ƙari kuma yau ne ta taɓa ganin Ma’aruf fuska da fuska tunda ta zo gidan sannan a rayuwarta wannan shi ne karon farko da ta taɓa keɓewa da wani namiji kamarsa tun barowarta ƙauyensu, babu ta yadda za ta haɗa mijin Zubaidah da ire-iren mazan ƙauyensu.

Ba iyakar kyau, ilimi, wayewa da nasarorin rayuwa ba, hatta nagarta da kyakkyawar mu’amala a zahiri ma ba ta ga kamar Ma’aruf mijin Zubaidah ba kaf ƙauyensu. Alal haƙiƙa ita ba mai zuzzurfan ilimi ba ce, amma Allah Ya yi mata baiwar karantar halayyar bil ‘adam bakin gwargwado.

Kiran sallar magariba ne ya tashe ta daga karatun littafin da take yi kamar yadda ta tsara, ta shiga banɗaki ta ɗauro alwala ta fito ta shimfiɗa darduma ta tayar da sallah, har lokacin tana jin motsin Zubaidah a kitchen tana shirya wa mai gidanta abinci. Tana cikin ɗakin ba ta fito ba har aka yi sallar isha’i.
Dare ya fara yi, tun Asma’u na jin hirar su sama-sama da na sautin T. V a falon har komai ya dakata alamun sun kashe kayan sun shige ɗaki, ta ɗaga kai tana kallon agogon bangon ɗakin da ya nuna mata ƙarfe sha ɗaya har da rabi na dare Ko kaɗan Asma’u ba ta yi mamakin rashin barcinta a dai-dai wannan lokacin ba, domin abu ƙalilan ke hana ta barci tun tana ƙarama bare kuma abin da ya wakana tsakaninta da Ma’aruf.
Idan ta lissafa dukkan waɗancan Qualities da Ma’aruf yake da su sai ta ga dama a matsayinta na cikakkiyar ‘ya mace zai wahala ta iya controlling kanta wajen shafe babinsa daga ranta. Sha biyu ta wuce sosai ta idar da sallar shafa’i da wutiri kamar kullum ta fara jera doguwar addu’a ga Innarta.

Yunwa take ji, sai dai ta ƙudirce a ranta a daren ba za ta sa wa cikinta komai ba, hakan duk yana cikin kaucewa haɗuwa da mijin Zubaidah.

Amma yunwa ba a sha mata la haula, ba a je ko ina ba Asma’u ta kasa jurewa, ala tilas ta tashi daga kan dardumar hijabinta na kanta ta nufi kofar daki.

Kafin ta fito sai da ta ɗaga labule a hankali bayan ta buɗe ƙofa. Tana iya hangen wani ɓangare na falon cikin launikan hasken fitilar lantarki, babu kowa, don haka kai tsaye ta fito ta yi wa kitchen tsinke, ta zuba abinci ta fito.

Gabanta ne ya faɗi! Tsoro ya cika mata zuciya, saura kaɗan kwanon abincin da ta riƙo ya kufce ya faɗi ƙasa. Ma’aruf ne zaune shi kaɗai a falon, hankalinsa duka yana kan na’ura mai ƙwaƙwalwar da yake aiki, abin da ya bawa Asma’u tsoro da mamaki lokacin da za ta shiga sam ba ta ganshi ba, sai da ta fito, wataƙila bayan shigarta ne shi ma ya fito.

Motsin rufo ƙofar kitchen da ta yi ne yasa Ma’aruf ɗago kai a hankali ya dubi wajen kitchen ɗin, sum-sum ta zo ta wuce ta gabansa ta shige ɗaki, ta janyo ƙofar ita ma a hankali ta zauna ta fara cin abincin kirjinta na dukan uku-uku.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kaddarar Mutum 9Kaddarar Mutum 11 >>

2 thoughts on “Kaddarar Mutum 10”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×