Skip to content
Part 11 of 23 in the Series Kaddarar Mutum by Mustapha Abbas

Kamar Ruƙayyan na karantar zuciyarta ta ce, “Na yarda ba kowa ba ce ita, amma idan ya zama dole me zai hana ki sa a kawo miki gyatuma? Kai ni fa gyatumar ma ban yarda da ita ba wallahi, domin ita ma tana iya ɓullo miki ta wata sigar, Halisa ƙawata gyatumar ce ta shuka mata tsiya, ta zagaye ta haɗa mijin da jikar aminiyarta.”

Zubaidah ta ja tsaki “Matsalata da ke gurɓataccen tunani Ruƙayya, a kan komai ma ke ba kya yin tunani mai kyau, ya za a yi kwanyarki ta riƙa buga miki irin wannan makakken lissafin? Wa ce ce Asma’u, me aka yi aka yi ta, meye a tare da ita da har zai ja ra’ayin Ma’aruf?”

Ruƙayya ta bi ta da wani irin kallo kamar ta ga sakarai, sannan ta girgiza kai cikin takaici.

“Wawiyar banza! Har yanzu da sauran ki, to wallahi irin yadda kika raina yarinyar nan ba haka take ba, matsayina na mai ƙaunarki ina baki shawara tun wuri ki sallame ta ta koma gida, har wani aiki ne a gidan nan da zai gagare ki kamar wata ƙaramar yarinya?”

Zubaidah ta yi shiru alamun maganar ta so ta yi tasiri a ranta, sai dai har abada ba ta jin Asma’u za ta kai wannan bigiren, ba ta da wannan isar, kamar yadda ba ta taɓa hasaso haɗaɗɗe kuma gogaggen mutum kamar Ma’aruf ɗinta da wata ƙasƙantacciyar mace irin ta ba ‘For God sake.’

“Kin ga Ruky ni fa ban ce miki yarinyar nan za ta zauna a gidan nan din-din-din ta ci gaba da min aiki ba, duka kwanaki nawa suka rage in rabu da wannan wahalallen cikin, sai ta koma inda ta fito so what?”

“To shi kenan ai.” Suka rufe wannan babin.
Asma’u ce ta fito hannunta ɗauke da kwalin lemon Civita mai sanyi da kofuna ta ajiye gaban Ruƙayya, dai dai lokacin wayar Ruƙayyan ta yi kiɗa, dubawar da za ta yi kuwa sai ta saki salati har tana firgita Asma’u. “K.B fa yana waje, shaf na manta da shi wallahi.” Ta faɗa. “Ya ba za ki manta ba, kin samu kinibibi kina yi ‘yar iskar mata. Asma’u je ki shigo da shi don Allah.”

Yana tsaye a harabar gidan jikin motar da suka zo da ita, babu yadda za a yi Asma’u ta manta fuskarsa, ta yi masa sallama haɗe da gaishe shi. Bai amsa ba ya ce, “Malama ashe kina nan?” Asma’u ta gyaɗa kai sannan ta ce, “Sun ce ka shiga.” Ta wuce yana biye da ita har falon, shi ma ya samu guri ya zauna, suka fara gaisawa da Zubaidah cikin barkwanci. Asma’u ta shige ɗakinta ta zauna, tana jin shewar su har sa’arda Doctor K.B ya tashi ya fita ya bar Ruƙayya a gidan da nufin sai ya dawo daga aiki ya biyo ya ɗauke ta su wuce gida.

Da yammaci ne bayan Ruƙayya ta tafi Zubaidah ta shigo ɗaki ta same ta, lokacin ta kammala cin abinci babu jimawa.

“Asma’u ɗazu na yi miki magana kan hijabi, kawai ki ci gaba da sa kayan ki musamman idan mai gidan nan yana nan saboda tsare mutuncinki, na san duk an koyar da ku a Islamiyya, ke idan yana nan ma ki daina fitowa sam, ki yi zamanki a ɗaki matuƙar ba nice na kira ki ba, don Allah ki ƙara haƙuri insha Allahu kin kusa komawarki gida, na san yanzu kina kewar su Hajiya da karatunki ko?”
Jinjina kai ta yi cike da gamsuwa, ta san dalilin Zubaidah na kafa mata wannan dokar, don ta saurari wani ɓangare na hirar su da ƙorafe-ƙorafen aminiyarta Ruƙayya kan zamanta a gidan, ita ma ko kaɗan ba ta fatan haɗuwa da mijinta, ta yi ƙoƙarin hana faruwar hakan da kanta tuntuni, don tun ranar farko da ta zo gidan kafin ya tafi Abuja ta ji muryarsa a falo lokacin tana kitchen addu’a ta riƙa yi a fili kada Allah Ya shigo da shi kitchen ɗin, domin Asma’u ta yi imanin faɗuwar gaba da tsoron da za ta ji idan suka haɗu sai ta ninka wadda take ji yayin da ta ji muryarsa, ta toshe duk wata hanya da za ta haɗa su. Duk lokacin da yake gari zaman ɗaki ya kama ta, idan za ta shiga kitchen sai ta tabbatar yana sama kasancewar ɗakunan kwanansu a sama suke daga shi har matarsa, sai dai a rayuwa kana taka Allah na tashi kuma bai zama lallai abin da mu ‘yan adam muka tsara wa kanmu ya tabbata ba. Abin da Zubaidah ba ta sani ba ko da ba a wannan duniyar ba, a wata duniyar daban Allah zai iya haɗa su.

Misalin ƙarfe shida da rabi na yamma ƙarar wayar Zubaidah ta kauraye ko ina cikin falon, Asma’u da ke cikin ɗaki ta san Zubaidar ita ma tana cikin ɗakinta tana kwasar barci, alamun bata san ma wayar na qasa a falo ba. Yanzu ma da take zaune gefen gado bayan ta fito daga wanka kamar yadda ta saba kullum bayan ta kammala girka abincin dare ta kan shiga ta yi wanka ta dauko littafanta ta yi ta bita, tana jin wayar na sake amsa-kuwwa a karo na uku bayan ba a fi wasu gajerun sakwanni da ta tsinke ba.

A gaggauce Asma’u ta kammala shafa mai ta saka doguwar rigarta mai hula da Zubaidah ta ba ta ta fito falon da sauri, niyyarta ta ɗauki wayar ta kai hau sama ta kai mata ɗaki tunda ta ga alamun mai kiran na son samunta ko ta yaya, ga Zubaidah na da ɗan karen nauyin barci. Asma’u ta kai hannu ta ɗauki wayar kenan suka haɗa ido da Ma’aruf da tuni ya riga ya shigo falon da tasa wayar a kunne.

A iyakar saninta mijin Zubaidah ba ya gari sai dai ko yanzu ya sauka, don ga jakarshi nan rataye a kafaɗa, wannan ɗin kuma waye? Ta tambayi kanta tana dubansa.

Ma’aruf ya cire wayarsa daga kunne ya datse ta, take wayar Zubaidan ma ta dakata daga kiɗan da take, kenan dama shi yake kiran.

Tabbas mijin Zubaidah ne Asma’u ta yi tsaye cak da wayar a hannunta tana kallonsa. Ya ƙaraso cikin takunsa na cikakkun maza lokaci guda kuma ya ɗauke kansa daga kallonta. “Ina me wayar ne? Tun ina air port nake kiranta fa.”

Durqusawa Asma’u ta yi har ƙasa tana miƙa masa wayar tare da faɗin “Tana cikin ɗaki, ina ganin barci take.” Bai karɓi wayar ba ya nuna mata inda ta ɗauke ta da hannunsa nufinsa ta ajiye ta kawai kana ya samu guri ya zauna cikin kujera yana ci gaba da latsa wayarsa, don haka ita ma Asma’u sai ta ajiye wayar hannunta ta juya da sauri za ta koma ɗakinta.

“Ji mana.” Ya faɗa da sassanyar muryarsa. Asma’u ta yi tsaye cak! Faɗuwar gabanta ta ƙaru, ta juyo a hankali tana kallon inda yake zaune amma ko kaɗan ba ta bari sun haɗa ido ba duk da cewa shi kuma ita yake kallo. “Ba sannu da zuwa, ba gaisuwa ba komai, ko baki san ni a gidan nan ba?” A nan inda take tsaye ƙirjinta na bugun uku-uku ta ce “Na sani mana.” Ya ɗan gyara zamansa kaɗan a kan kujerar, “Shi ne za ki tafi da gudu kamar kin ga dodo?”

“Ka yi haƙuri don Allah mijin Zubaidah.”
“No ni baki min laifin komai ba fa, ba buƙatar ki ban haƙuri, za ki iya kawo min ruwa in sha?” Girgiza kai Asma’u ta yi alamar amsawa, shi kuma ya mayar da hankali kan wayarsa, don haka ta samu damar shigewa ɗaki, hijabinta ta sako ta fito sannan ta zarce kitchen ta ɗauko ruwan roba da kofuna har da lemo ta dawo ta ajiye masa, ta yi amfani da damar don wanke laifinta, wato yi masa sannu da zuwan da ya yi ƙorafi.

Sai da ya ɗan ɗauki lokaci kafin ya amsa mata, ba tare da hakan ya dame ta ba ta juya ta koma ɗaki abinta, ko yaya dai yana da sauƙin kai, bai kuma raina darajarta ba, ma’ana a matsayin da yake kai za ta iya cewa ya mutunta ta, sai dai har yanzu ƙirjinta bai daina bugawa ba, kai tsaye za ta iya danganta faruwar hakan da tsananin ƙwarjinin da ya yi mata, bugu da ƙari kuma yau ne ta taɓa ganin Ma’aruf fuska da fuska tunda ta zo gidan sannan a rayuwarta wannan shi ne karon farko da ta taɓa keɓewa da wani namiji kamarsa tun barowarta ƙauyensu, babu ta yadda za ta haɗa mijin Zubaidah da ire-iren mazan ƙauyensu.

Ba iyakar kyau, ilimi, wayewa da nasarorin rayuwa ba, hatta nagarta da kyakkyawar mu’amala a zahiri ma ba ta ga kamar Ma’aruf mijin Zubaidah ba kaf ƙauyensu. Alal haƙiƙa ita ba mai zuzzurfan ilimi ba ce, amma Allah Ya yi mata baiwar karantar halayyar bil ‘adam bakin gwargwado.

Kiran sallar magariba ne ya tashe ta daga karatun littafin da take yi kamar yadda ta tsara, ta shiga banɗaki ta ɗauro alwala ta fito ta shimfiɗa darduma ta tayar da sallah, har lokacin tana jin motsin Zubaidah a kitchen tana shirya wa mai gidanta abinci. Tana cikin ɗakin ba ta fito ba har aka yi sallar isha’i.

Dare ya fara yi, tun Asma’u na jin hirar su sama-sama da na sautin T. V a falon har komai ya dakata alamun sun kashe kayan sun shige ɗaki, ta ɗaga kai tana kallon agogon bangon ɗakin da ya nuna mata ƙarfe sha ɗaya har da rabi na dare Ko kaɗan Asma’u ba ta yi mamakin rashin barcinta a dai-dai wannan lokacin ba, domin abu ƙalilan ke hana ta barci tun tana ƙarama bare kuma abin da ya wakana tsakaninta da Ma’aruf.

Idan ta lissafa dukkan waɗancan Qualities da Ma’aruf yake da su sai ta ga dama a matsayinta na cikakkiyar ‘ya mace zai wahala ta iya controlling kanta wajen shafe babinsa daga ranta. Sha biyu ta wuce sosai ta idar da sallar shafa’i da wutiri kamar kullum ta fara jera doguwar addu’a ga Innarta.

Yunwa take ji, sai dai ta ƙudirce a ranta a daren ba za ta sa wa cikinta komai ba, hakan duk yana cikin kaucewa haɗuwa da mijin Zubaidah.

Amma yunwa ba a sha mata la haula, ba a je ko ina ba Asma’u ta kasa jurewa, ala tilas ta tashi daga kan dardumar.

Kafin ta fito sai da ta ɗaga labule a hankali bayan ta buɗe ƙofa. Tana iya hangen wani ɓangare na falon cikin launikan hasken fitilar lantarki, babu kowa, don haka kai tsaye ta fito ta yi wa kitchen tsinke, ta zuba abinci ta fito.
Gabanta ne ya faɗi! Tsoro ya cika mata zuciya, saura kaɗan kwanon abincin da ta riƙo ya kufce ya faɗi ƙasa. Ma’aruf ne zaune shi kaɗai a falon, hankalinsa duka yana kan na’ura mai ƙwaƙwalwar da yake aiki, abin da ya bawa Asma’u tsoro da mamaki lokacin da za ta shiga sam ba ta ganshi ba, sai da ta fito, wataƙila bayan shigarta ne shi ma ya fito.

Motsin rufo ƙofar kitchen da ta yi ne yasa Ma’aruf ɗago kai a hankali ya kalli wajen kitchen ɗin, sum-sum ta zo ta wuce ta gabansa ta shige ɗaki, ta janyo ƙofar ita ma a hankali ta zauna ta fara cin abincinta.

Washegari ba kamar yadda ta saba ba, da wuri sosai ta tashi ta shiga kitchen ta kammala aiyukanta, kafin su tashi daga barci. Duk wani abu da ake girkawa da safen nan ta girka ta zuba a inda ba zai huce ba ta rufe ta zuba wanda za ta ci ta koma ɗaki, babu abin da kuma ya rage mata don haka ta koma barci abinta.

Motsin su a falon ne ya tashe ta daga barci, ta kalli agogo, a ƙarfe goma na safe mintuna kaɗan ne babu, tashi ta yi ta shiga bayi ta yi wanka ta fito ta zauna, ta riga ta yi wa Zubaidah duk abin da ta san zai ba ta wahala, don haka ta san a yau dai zai yi wahala ta neme ta, sannan babu ita babu fita ko da gaishe da ita kamar yadda ta saba, ta samu gado ta ƙara lafewa.

Ranar dai Ma’aruf wuni ya yi a gidan, don haka ita ma a wunin nan ko da wasa ba ta fita ba. Abincin rana ma Zubaidar ce ta kawo mata har ɗaki bayan ta girka. Babu abin da ya ɗan faranta ranta irin da Zubaidah ta ce da ita “Asma’u Allah Ya biya ki kan ƙoƙarin da kike min, na san zaman gidan nan tun tuni ya ishe ki, don Allah ki ƙara haƙuri, komai ya kusa zuwa ƙarshe insha Allah kin ji?”

“Sam kar ki damu Anti, wallahi ni bana jin wata takura a hakan, fatana dai Allah Ubangiji Ya raba ku da abin da ke cikinki lafiya.”

Zubaidah ta ji daɗin kalami da addu’arta, ta amsa da “Amin, kin gani jiya mai gidan ya dawo ya sauka a air port yana ta kiran wayata kasancewar mun yi zan tura direba ya ɗauko shi, sai barci ya ɗauke ni, wayar kuma na ƙasa tana ta haukanta, Wallahi sai tasi ya hawo.”
Asma’u ta ce “Ayyah, Allah Sarki, ai barci varawo ne Anti.”

*****
“Asma’u! Asma’u!! Kina ina?” Da sauri Asma’u ta fito falo inda Zubaidah ke kwance a ƙasa tana ta juye-juye, matsowa ta yi ta durƙusa a kusa da ita tana tunanin taimakon da ya dace ta fara yi mata, kafin ta san abin yi ta sake jin muryar Zubaidar na faɗin “Ga wayata can ɗauki ki kira min Ma’aruf don Allah.”

Asma’u ta ɗauki wayar tana dubawa a hankali ta lalubo lambar, ta gane ta ne da sunan da ta gani ya kira ta ranar da zai dawo.

Wayar kuwa na shiga a can ɓangaren bugun farko aka ɗauka muryar nan tasa ta ratsa kunnenta “Honey ya aka yi?” Asma’u ta san ma’anar kalmar tunda jefi-jefi tana karanta litattafan hausa wanda akasari jigonsu soyayya ce

“Ba ita ba ce, ba ta da lafiya shi ne ta ce in kira ka, ina tunanin ma haihuwar ce ta zo.” Bai ce komai ba ta dai ji ya katse kiran, ita ma ta ajiye tana ci gaba da jera wa Zubaidah sannu.

Mintunan da ba su haura biyar ba wata mace kakkaura fara sanye da fararen kaya irin na likitoci ta shigo falon. Ta duba Zubaidah sosai, “Wannan fa sai mun je asibiti, tashi maza ki shirya komai da za a buƙata a can, haihuwar ce in sha Allah.” Asma’u ta tashi ta shiga ɗakin Zubaidah ta tarkato duk wani abu da ta san za a buƙata, har ruwan zafi ta zuba a fulas. Tuni matar ta taimakawa Zubaidah sun fita har sun shiga mota, a can ta same su ita ma ta shiga.

Dr. Murja ke tuƙa motar, ita da Zubaidah suna baya yayin da ta kwanto jikinta tana nishi sosai da salati. Hankalin Asma’u ya ƙara tashi, ta san irin yadda Zubaidah take ji, kawai ta ci gaba da karanta mata addu’o’i har suka iso asibiti. Tana kallo aka ɗora ta a gado mai tafiya aka shiga da ita ɗakin haihuwa.

Ba a jima ba Ma’aruf ya shigo asibitin yana dube-dube, suka haɗa ido sai ya nufo wajenta. “Yaya ba ta haihu ba ko?” Ta sauke ajiyar zuciya a hankali kana ce, “Har yanzu dai babu wanda ya fito daga ciki.” Kafin ya sake cewa wani abu wayarsa ta yi kiɗa ya ɗaga.

“Eh Mum, yanzu ni ma na iso asibitin, ban san halin da ake ciki ba don har yanzu ba su fito ba, yes akwai yaruwarta a wajen, to to shi kenan zan sanar da ke duk yadda ake ciki.” Bayan Ma’aruf ya katse wayar ya ci gaba da safa da marwa a wajen, ita dai tana tsaye kusa da ƙofar ɗakin da aka shiga da Zubaidah tana nema mata sassauci wajen Ubangiji.
Ƙofar ta buɗe Dr. Murja ta fito nan da nan Ma’aruf ya ƙarasa gare ta “Doctor yaya, meye labari?” Babu ɓata lokaci ta sanar da shi albishir mai daɗi.

“Madam ta sauka, masha Allah an samu fine boy, yau fa yallaɓai ya zama Baba, sai a ba ni goron albishir.” Ya saki murmushi tare da zuba hannaye a aljihu ya ɗauko kuɗin da bai san ko nawa ba ne ya miƙa mata. Dr. Murja ta sa hannu ta karɓa tana godiya.
“Amma Doctor zan iya shiga in ga Baby da Madam?”

Ta yi ‘yar dariya “Ƙwarai za ku iya shiga, ina ma ƙanwar tata take sai a samo mata ko da tea ne ta sh… Kafin Dr. Murja ta ƙarasa tuni Ma’aruf ya sa kai cikin ɗakin, Asma’u ta bi bayansa.

Zubaidah na kwance har an shiga da ita ɗakin hutu, tamkar ba ita ce ɗazun ba ta san inda kanta yake ba, kusa da ita kyakkywan jaririnta yana ta wutsil-wutsil cike da kuzari. Ma’aruf ya ƙura musu ido fuskarsa ƙunshe da murmushin farin ciki, ya sunkuci jaririn yana kallon shi, sannan ya kalli Zubaidah ya ce, “Honey kin min wayo, Babyn ya fi kama da ke fa, next time ba zan bar hakan ba.” Hararar sa ta yi, shi ko ya sa dariya yana tambayarta lafiyar jikinta, ta ce da shi “Da sauƙi, sai cikinta kawai da take jin kamar an yashe mata ‘yan hanji, kuma Doctor ta ce ta sha ruwan zafi.” Ya juya ya kalli Asma’u da ta yi saurin isa inda filas yake ta fara haɗa mata ruwan shayi mai kauri. Za ta miƙa mata Ma’aruf ya ajiye Babyn ya ce ta ba shi cup ɗin.
Da kansa ya tallabo ta ya riƙa ba ta a hankali. Asma’u ta juyar da kanta zuwa duban jaririn na su mai cike da ƙoshin lafiya, komai nasa irin na Zubaidah ne sai hasken fatar uban. Nata jaririnta ya faɗo mata a rai, tabbas a ce ka haifi ɗa abin akwai daɗi, ko da cewa nata ba irin wanda ake so ba ne. Ta share hawayen da ke ƙoƙarin sulmiyowa daga idanunta.
Kafin wani lokaci ɗakin ya fara samun baƙuntar mutane daga gidajen su duka biyu. Sai ga Maryam da Firdausi, zuwan su ne ya sa Asma’u sakewa, amma da duk a takure take. Har yanzu Ma’aruf bai daina faɗawa mutane ta waya ba, kowa ya ganshi ya san yana matuƙar farin ciki da murnar zuwan yaron da aka haifa masa duniya, shaidar son mahaifiyarsa kenan.

Tabbas Zubaidah ta yi sa’ar miji mai sonta, ƙauna da ba ta kulawar da ko wace ‘ya mace za ta so samu. Ma’aruf fari ne sosai, da alamun ya haɗa jinsi da fararen fata ko fulanin asali, don yalwatacciyar baƙar sumarshi ta alamta hakan, yana da kyau dai-dai misali.

Sai washe gari aka sallame su suka koma gida.
A gidan ma jama’a ne ke ta ɓullowa abokan Ma’aruf da ƙawayen Zubaidah har ranar suna.
An yi shagali irin wanda Asma’u ba ta taɓa gani ba, ko babu komai ta bawa idanunta abincin da ba su taɓa ci ba, har Hajiya Yagana sai da ta zo ganin jikanta, ta ji daɗin ganin yadda Asma’u ta ƙara samun sauyin ci gaba a ɗan zaman da ta yi gidan Zubaidah. Sam ba ta ga alamun rashin walwala ko takura a tare da ita ba. Yarinya ce ita mai saurin saba wa da duk yanayin rayuwar da ta tsinci kanta, sannan ta iya zama da mutane. Duk abin nan da ake tana nan sanye da hijabinta, sai dai ta sauya shi da wanda Zubaidah ta siya mata mai launin ruwan ƙasa.

*****
Bayan kwana arba’in Asma’u na ta zuba idon ganin ranar da Zubaidah za ta sallame ta ta koma gidan Hajiya, don duk wani taimako da ya kamata ta yi mata, a halin da ake ciki ma tuni mai jego ta ware har ta fara yawonta, wasu lokutan tare da Ma’aruf suke ficewa a mota su barta a gidan. Shiru kake ji, ta ma daina yi mata zancen komawar, ita kuwa kawaici ya hana ta sake tuntuɓarta.


LHaka rayuwar ta ci gaba da tafiya lokuta na shuɗewa. Yanzu Zubaidah ta sakar mata ragamar girkin abinci tare da sauran ayyukan da ba su kamata ma ta ɗora mata ba, ko haihuwar da ta yi ne ya sa ta sangarce babu abin da ta sa a gaba yanzu sai yawo, ko kuwa dama can haka take cikin ne ya taka mata burki? Ko ma dai mene ne Asma’u ta lura Ruƙayya na taka muhimmiyar wajen shiriricewar zaman gidan aurenta2e
Ranar wata litinin da rana bayan Asma’u ta kammala girki, ta gyara kitchen tsaf, Ruƙayya ta zo ta kwashi Zubaidah suka fita, gidan ya rage sai ita kaɗai, Ma’aruf ma kwanaki biyu ba ta jin motsinsa, idan ta yi la’akari da yadda yawon Zubaidah ya ƙaru ta san tabbas ba ya gari.

A wasu lokutan tana tausaya wa Ma’aruf da Zubaidah, domin ta hango gagarumin haɗarin da ke tattare da aurensu matuƙar Zubaidah na tare da su Ruƙayya. Sau zaya Zubaidah ta fita da ita unguwa don ta taya ta riƙon jaririnta. Bikin Bushira ake yi wata ƙawar tasu, Asma’u ta sha mamakin ganin shaiɗanar da suka gudanar matsayin shagalin biki kamar ba matan aure ba.

T.V ɗin falo a kunne, don haka Asma’u ta fito ta zauna tana kallon tashar MBC Drama, saboda samun dama har da ɗaukar remote tana canza tashar da ranta yake so. Babu zato ba tsammani kawai ta ga Ma’aruf a bakin ƙofar shigowa, duk sai ta kiɗime, sai da ya yi sallama sau biyu sannan ta iya amsawa.

Ya ƙaraso ya zauna tare da kwantar da kai jikin kujera ya ce “Wash Allahna!” Akwai tazara tsakaninsu sosai amma ji take kamar ƙasa ta tsage ta shige don kunya, ta daure ta yi masa sannu da zuwa. Bai kalli inda take ba ya amsa sama-sama da gajiya a muryarsa.

Miƙewa ta yi tsam za ta bar gurin, takunta na biyu biyu kenan za ta ƙara na uku taji ya ce “Zo mana.”

Asma’u ta koma ta zauna a hankali ƙirjinta na dukan uku-uku.

<< Kaddarar Mutum 10Kaddarar Mutum 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.