Skip to content
Part 12 of 23 in the Series Kaddarar Mutum by Mustapha Abbas

“Wai tsoro na kike ji ko me?”

Ta yi masa shiru.

“Ko ina miki kama da masu satar mutane ne?”
Muryarta na rawa ta ce “A a.”

“Amma duk inda kike da zarar na zo wurin sai ki tashi ki gudu, ke ina lura da ke duk hanyar da kika san za ki bi don kaucewa haɗuwa da ni ita kike bi Why?” Asma’u ta marairaice murya sosai “Don Allah ka yi haƙuri.”

“Da haƙurin ta mutu sadakar nawa kika bayar? Sarkin bada haƙuri. Zolayar ta ɗan ba ta dariya, sai dai ba za ta iya dariyar ba.

“Ba ni fa da iyaka da shiga ko wane ɗaki cikin gidan nan har ɗakinki, kin ga idan na so tuntuni wasan ɓuyarki ba zai yi tasiri ba, kunyarki ta yi yawa.” Ya dan saurara kaɗan, can kuma ya ce, “Ya kike da su Zubaidah? Ina nufin alaƙarku, don ban san ki cikin jerin ‘ya’yan Hajiya ba?”

“A gidan kawai nake zaune.” Ta bashi amsa a gajarce da alamun ƙosawa da tambayar.

Ma’aruf ya ɗan yi shiru yana danna wayarsa, zuwa can ya sake cewa, “Ok don Allah ki kawo min ruwa zan sha, ke har da yunwa ma nake ji, akwai abinci ko?”

“Eh akwai.” Asma’u ta faɗa sannan ta juya ta nufi kitchen tana harɗewa. Da rawar jikinta ta zuba masa abincin da ta dafa cikin mazubi na alfarma kamar yadda Zubaidah take yi. Bayan ta gama zubawa ta tsaya ta sake nazarin kayan wai ko za ta hangi wani kuskure.

“Alhaji a kawo maka nan ko a kai dinning?” Ɗago kai ya yi ya dube ta sakanni kaɗan kana ya kawar da kan ya ce “Kawo min nan kawai.” Ta ƙaraso ta ajiye farantin a gabansa a hankali, saukowa ya yi ƙasa ya zauna dirshan a kan carpet gaban kayan abincin, tuni ita kuma ta wuce ɗakinta.

Kamar mintuna goma Asma’u tana zaune da littafi a hannunta ta ƙura masa ido, ita da kanta ba za ta ce ga abin da take dubawa ko karantawa ba, ƙofar ɗakin ta buɗe a hankali kawai ta Ma’aruf ya shigo, cikin kaɗuwa ta ɗago kai suka haɗa ido, a taƙaice Ma’aruf ya ƙarewa ɗakin nata kallo kafin ya ƙarasa shigowa, ya ja farar kujerar roba ya zauna nesa da ita kaɗan.

“Asma’u ko? To ya kika gani? Na faɗa miki ina da damar shiga ko ina a gidan nan, da fatan ban yi laifi ba?” Da sauri ta girgiza kai, “A a baka yi ba.”

Shiru ce ta ratsa tsakaninsu tsayin wasu sakanni, baka jin sautin komai sai ‘ya’yan makullan hannunsa da yake karkaɗawa. Shi ya fara kawar da shirun. “Ina da tambaya idan ba za ki damu ba.”

“Ina sauraronka.

“Yanzu zaman me kike a gidan nan?” Tana da baki ta ce, “Abin da aka roƙe ni in yi, kuma na gama yanzu ya rage in koma gida, sai dai har yanzu ban ji Anti Zubaidah ta ce komai game da tafiya ta ba, ni kuma so nake in tafi.”

Ya dube ta sosai, “Ke kuwa me yasa kike son ki tafi, ba kya jin daɗin zaman gidan ne?”

“A a ba haka nake nufi ba, ka san ina zuwa makaranta, na tabbata yanzu an wuce ni abubuwa da yawa.” Asma’u ta bashi amsa.

“Wace makaranta kike yi, meye level ɗin karatunki?” Ya buƙata.

“Makarantar Islamiyya ce TAHFIZUL QUR’AN, kuma sauka ma muke yi.”

“Kin san abin da nake so a gurinki?”
Asma’u ta girgiza kai cike da fargaba.

“Idan har babu takura ina so ki ci gaba da zama a gidan nan, ba a matsayin ‘yar aiki ba, ki riƙa taimakawa matata, zan riƙa biyanki albashi mai yawa kuma za ki ci gaba da karatunki, akwai makarantu sosai a unguwar nan.”

Tunda suka fara magana kanta a sunkuye yake sai yanzu ta ɗago ta dubi cikin idanununshi, shi ma ita yake kallo yana son gano yadda za ta karɓi maganarsa yana kuma mamakin kansa. Asma’u ta shafe gumin da ya fara jiƙe mata goshi da hannunta. “Ka yi haƙuri ba zan iya ba.” Ta faɗa kanta tsaye.

“Me yasa ki yanke hukunci da sauri haka?” Ya tambaye ta.

“Ba ni ke da ikon yin hakan ba, Hajiya ce da ta saka ni, kuma ko da ta amince ma ba lallai Zubaidah ta so hakan ba.”

“Zubaidar? Don me kike tunanin Zubaidah ba za ta so zamanki ba, bayan ita da kanta ta roƙi a turo ki ki taimaka mata?”

“Mu dai a al’ada irin ta ƙauyenmu mata ita ke da alhakin dukkan ayyukan gidan mijinta, don haka ina ganin Zubaidah ita kaɗai ya fi cancanta ta yi dukkan wani aiki da ke gidan nan ko don ta samu ladan da matan ƙwarai suke samu, kula da gida aikin matar gida ne, ko da ta roƙi in zo ma na ɗan lokaci ne kafin ta haihu, a yanzu na tabbata za ta iya komai, ni na maka alƙawarin duk lokacin da ta sake ɗaukar ciki muddin ina raye in kun neme ni zan sake zuwa in zauna har ta haihu.”

Ma’aruf ya gyara zama a kan kujerar da ya ke zaune kaɗan. “Haba dai, ke ba kya fatan ki yi naki auren ki tafi gidan mijinki kafin lokacin?”

Ga mamakinsa sai ya ga idanunta sun ciko da ƙwalla sosai. Zuciyar Asma’u ta yi rauni, kamar ya fama mata wani ciwo da ke binne a ƙoƙon ranta, ta kasa tausar zuciyarta
“Aure? Kuma ni? To waye ma zai aure ni?” Ta faɗa a zuciyarta a fili kuwa ta kasa cewa komai sai ƙwallar da ta taru a idanunta ta fara sauka a hankali kan kumatunta, sai ga sheshsheƙar kuka. Cike da mamaki Ma’aruf ya ke dubanta. Gaba ɗaya sai ta daina tanka masa, ya ƙari tambayoyinsa ya koma rarrashinta. Da ƙyar dai ya samu ta daina kukan. Tabbas akwai wani gagarumin abin da yake damunta.

*****
Bayan sallar isha’i sosai Zubaidah ta shigo gidan a jigace, kasancewar sun sha tafiya ba ‘yar kaɗan ba, sune har gyaɗi-gyaɗi kai Bushira gidan mijinta, don ma an tafi kai amaryar da wuri. Falon babu kowa, ta tabbatar Ma’aruf ya jima da dawowa yana cikin ɗakinsa.

Tana rungume da Khalifa a kafaɗarta ta tura ƙofar ɗakin Asma’u, kamar ko yaushe Asma’un na zaune a gefen gadonta, ta ɗago kai tana dubanta.

“Sannu da dawowa.”

“Yauwa Asma’u, ni tun yaushe Ma’aruf ya shigo gidan nan ne?”

“Tun bayan sallar la’asar ya dawo. Asma’u ta ba ta amsa. Zubaidar ta isa bakin gado ta kwantar da Khalifa da ke barci kusa da ita tana faɗin “Gashi nan bari in hau saman in yi wanka, na gaji sosai, har gyaɗi-gyaɗi muka kai amaryar gab da sallar magariba.”

“Kai gaskiya Anti kun yi sauri ma, duk da ban san gyaɗi-gyaɗi ba amma gab da sallar magariba fa?” “Wallahi kuwa Asma’u .”

Zubaidah ta faɗa tana ƙoƙarin ficewa daga ɗakin.

Ta iske Ma’aruf zaune a kan gado da computer sa a gaba da alama aiki yake, sallamar da ta yi ya sa shi ɗago kai ya dube ta sannan ya ci gaba da abin da ya ke.

“Sannu da aiki.”

Ya amsa kawai, sai ta samu guri ta zauna gefen gadon kusa da shi, a ɗan nazarin da ta yi sai take ganin kamar ya fara gajiya da zirga-zirgar bikin da take fita duk da ta san hakan sam ba halayyarsa ba ce, ya san su waye Ruky da Bushira a wajenta. Tana shirin sake yi masa wata magana don tabbatar da abin da take zargi sai ta ji ya ce, “Ina Khalifan?”

“Yana ƙasa ɗakin Asma’u.” Ta bashi amsa a gajarce. Jim kaɗan tana zaune ita ma tana danna wayarta, can ta miƙe, “Bari in shiga toilet ɗin ka in watsa ruwa ko na ji daɗin jikina.

Mintuna biyar ta fito daga banɗakin kana kuma sai ta fita, ɗakinta ta nufa, ta sauya kayan jikinta zuwa na barci, sannan ta sauko ƙasa ɗakin Asma’u ta ɗauko Khalifa ta koma ɗakin mai gidan.

“Gashi ya zo ya taya ka aikin.” Ta faɗa dai-dai sa’ar da take ƙoƙarin kwantar da shi a gefensa. Ma’aruf ya juyo ya shafi kumatunsa har zuwa laɓɓan bakinsa yana murmushi.

“Honey ina son magana da kai fa, gashi na ga aiki kake ko?” Cewar Zubaidah bayan ta zauna kan gadon.

“Yi maganarki mana ina sauraronki.” Ya faɗa ba tare da ya dakata da abin da yake ba.
“A game da yarinyar nan ne Asma’u, zuwa yanzu ya kyautu a ce ta koma gida, don ko ɗazu sai da Hajiya ta min waya saboda karatunta, gashi ni kuma har ga Allah ina jin daɗin zama da ita, tana taimaka min sosai, ba ta da matsala.” Ma’aruf ya ɗan yi jim sannan ya ce, “To yanzu wace shawara kika yanke kenan?” Ta rausayar da kai, “Haƙura kawai zan yi in sallame ta ta tafi, sai ka bani wasu ‘yan kuɗi in ba ta, amma ba haka na so ba wallahi, honey ko dai in roƙi Hajiya ta barta ta zauna ta ci gaba da taimaka min zuwa wani lokaci kafin ta yi aure? Tunda ka ga yanzu da zan koma school ɗin nan dole sai da mai aiki, in ba haka ba abun sai ya taru ya min yawa.”
Shiru Ma’aruf ya yi na ɗan lokaci hannunsa na kan madannin computer (keyboard) idanunsa suna kuma kallonta da mamakin halinta, babu yadda bai yi da ita ba kan ya ɗauko mata mai aiki fafur ta ƙi, amma yanzu wai da kanta take so yarinyar ta zauna, har tana faɗin ta ji daɗin zama da ita, ko da yake shi da kansa ya gano yarinyar ba ta da matsala.

“To me zai hana ki tuntuɓi Hajiyar, ko za ta amince, sai ki ɗauke ta bisa sharaɗin biyanta wasu kuɗi matsayin ladan aikinta, ki jarraba ki gani sai mu biya ta.”

Zubaidah ta yi shiru, zuwa can ta ce, “Matsalar ita ce sam bana jin Hajiya za ta amince, da ƙyar ta barta wannan ɗan zaman ma da ta yi, tana ji da ita musamman tun daga lokacin da suka je ƙauyensu suka tarar mahaifiyarta ta rasu.”

“Kenan ba garinku ɗaya ba ma? Ai na ɗauka daga Maiduguri ita ma take, yaya ne alaƙarku da ita?”

“Daga ƙauyukan Zinder take, labarin rayuwarta akwai abun tausayi, a baya idan ka ganta ba za ka ce ita ba ce…

Sai da ta bashi labarin Asma’u kaf, iyakar wanda ta sani.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kaddarar Mutum 11Kaddarar Mutum 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×