Skip to content
Part 9 of 23 in the Series Kaddarar Mutum by Mustapha Abbas

A can ƙauyen kuwa bayan tafiyar su babu jimawa Kakannin Asma’u suka zo daga garin gabas sakamakon labarin zuwan ta da ya riske su. Sun tarar da gidan ya ƙone ƙurmus ya sha wuta saɓanin yadda suka san shi. Kasancewar dama suna zuwa akai-akai neman labarinta tun bayan tafiyarta. Har bayan rasuwar Inna Hauwa ma sun zo sosai. Hankalin su ya tashi da suka samu labarin yunƙurin ƙone jikar su da ranta da Maigari Nuhu ya sa aka yi, sannan aka kore ta daga ƙauyen.

Sun tsinci kan su cikin tsananin baƙin ciki da ɓacin ran da ya sa suka kasa haƙura da wannan zalunci. Kai tsaye suka wuce birni inda suka shigar da ƙara kan abin da ya faru. Hukuma ta yi aikinta inda ta umarci Maigari ya nemo Asma’u duk inda ta shiga ya damƙa ta a hannun Kakanninta, domin shi da kansa ya sa aka kore ta bayan an samu ta dawo daga shafe tsawon lokaci ana neman inda ta shiga. An kuma ci su tara mai yawa. Wannan shi ne hukuncin laifin su.

*****
Hajiya Yaganah ta shafe tsayin kwanaki tana rarrashin Asma’u. Da ƙyar ta samu ta rabu da kukan da take, amma ba don zuciyarta ta rabu da raɗaɗin mutuwar mahaifiyarta ba, ta dai ɗauki dangana kurum, da taimakon addu’o’i da ta riƙe ba ji ba gani sannan ta samu nutsuwa.

Tsoron Allah Ya ƙaru a zuciyarta sosai, ta dage da zuwa islamiyyar da Hajiya ta saka ta tuntuni. Asma’u ta yi imanin a yanzu wannan shi ne kaɗai gatan da za ta yi wa rayuwarta. Ta manta cin zarafin da ƙauyen su suka yi mata, zuwa yanzu ta tabbatar raba su da jahilcin da ke tare da su sai Allah, don haka ta miƙa dukkan lamarin gare shi.

Lokaci na tafiya sannu-sannu ga mai yawan rai kuma ga mai kyakkywan tunani ya san rayuwar gudu take zuwa riskar ajali. Hajiya Yaganah ta daina sintirin yawon tallar da take, domin yanzu kasuwanci ya haɓaka fiye da da, kuma Nasir na iya tsaiwa da ƙafafunsa ya kula da dukkan dukiyar da taimakon yaran shago biyu.

Tabbas a yanzu ba su da wata gagarumar matsalar da zai kasance sai Hajiyar ta tashi haiƙan tana nema da guminta kamar dai da, sannan Zubaidah da taimakon mijinta tana iyakar bakin ƙoƙarinta wajen tare wasu buƙatun, domin mijin nata mai hali ne kuma mai hannun kyauta. Da wannan ta mallaki kadarori da kuɗaɗe bakin gwargwado. Ga dai aljannar duniya ta samu irin wadda Zubaidah ke mafarkin samu. Ita kam ta yi dacen auren Ma’aruf Mahmud Mahuta, mamallakin kamfanin M.M Textile & Brothers da ke da babbar Plaza a kasuwar Kwari.

Wata rana ta kira waya gida kan tana so ta dawo ta haihu a nan, ƙorafinta babu mai taimaka mata a can, don cikinta ya kai munzalin da ya fara hanata aiyukan gida saboda ɗan karen laulayi sannan ita ba ta son mai aiki.

Sam Hajiya ba ta amince da buƙatarta ba, ta ce ta zauna ta haihu a ɗakin mijinta, za ta kawo mata dattijuwa Asabe daga ƙauyen su ta zo ta zauna wajenta. Meye ma amfanin dawowarta gidan? Muhimmin abin da Hajiyar ta guda bai wuce idan ta dawo gidan su haɗu da Ummita su yi ta ɗaga mata hankali tunda ba tunani ne ya ishe su ba?

Zubaidah ma ta hau dokin na ƙi, ba ta buƙatar ire-iren su Asabe a gidanta, sam ma ba ta yarda da tsaftar tsohuwar ba, mijinta ba ɗan hayaniya ba ne, yana da bala’in tsantseni, ba ko wace mace ke girka abinci ya zauna ya ci ba. Har yau har kwanan gobe girkin Mahaifiyarsa yafi so fiye da na ita kanta da take matsayin matarsa.

Dole Hajiya ta jingine maganar Asabe. Dama ba a maganar ƙannenta da suke tsananin jin kan su musamman Ummita da ko da wasa ma ba za ta yi gangancin tura ta ba, saboda ba sa haɗa inuwa guda.

Daga ƙarshe dai muradin Zubaidah ya faɗa kan Asma’u.

Asma’u tana ji tana gani a ka shiga rigar alfarmarta aka dakatar da karatun Islamiyyar da ya fara saita rayuwarta. Babu wanda ya damu ya faɗa mata adadin wa’adin zaman da za ta yi a gidan Aunty Zubaidah kafin ta dawo ta koma makarantar ta, ta kuma kasa tambaya saboda tsananin kawaici da ganin girman Hajiya da take yi. Har zuwa lokacin da ta haɗe kayanta kaf, ta koma gidan Zubaidah da ke unguwar Rijiyar Zaki don faranta ran Hajiya kaɗai. Mabuɗi kenan na sake buɗe babin wata sabuwar ƙaddarar ga Asma’u.

Da fari zaman gidan ya so ya ba ta matsala dalilin sam ba ta sakewa kamar yadda ta saba da gidan Hajiya, dukkan wasu kayan amfanin gida da ta riska sun sha bam-ban da waɗanda ta sani ta saba amfani da su. Sai ta wuni cikin ɗakin da a ka ajiye ta matsayin inda za ta zauna tsayin zamanta a gidan, don hatta banɗaki a cikin ɗakin yake, ba komai take yi ba, sai idan Zubaidar ta kira ta don ta kama mata wani aikin, ko ta karɓi abinci.

Tana gamawa kuma za ta koma.


Yau da gobe ta ga wannan ba za ta kai mata ba, ta tsiri karance-karancen litattafan da ake koyar da su a makaranta. Sannu a hankali kuma sai Zubaidah ta fara saka ta girka abincin da za su ci a gidan kacokam, tunda a lokacin mai gidan ba ya gari, don haka Zubaidan ba ta da matsalar shiga kitchen tana fama da kanta, in don girkin Asma’u ne ita kam sam ba ta ga aibunsa ba, to a gida ma kafin ta zo nan a wasu lokutan shi take ci. Ba ta yi kuskure ba idan ta ce kaf ɗin su, har ita Asma’un ta fi su iya girki, ga tsafta gun yarinyar.
Tun Asma’u ba ta san yadda ake amfani da kayan kitchen ɗin gidan ba, har ta fara ganewa, don Zubaidar da kanta take nuna mata komai, bugu da ƙari ta zama ‘yar aike, cefanen gidan kaf ita take yi. Tun ba ta gane guraren da ake siyayyar har ta kai ta san ko ina. Asma’u yarinya ce mai saurin fahimtar abu, don ba a ɗauki dogon lokaci da shigarta makaranta ba ta iya karatun hausa sosai kasancewar tun a ƙauyen su dama ta san wasu abubuwan musamman ɓangaren addini.
Yau da gobe kuma sai rayuwar gidan ta fara yi mata daɗi, daga ita sai Zubaidah, ba ta cusguna mata, sai dai yawan aiki. Wannan kuwa ta saba da shi, ba ta ɗauke shi bakin komai ba, don ba yau ta saba bauta musu da jinin jikinta ba.
Duk aikin da Zubaidah za ta saka ta ba ta ganin wahalarsa. Su Firdausi suna yawan zuwa gidan, don Maryam idan ta zo har kwana take yi musamman ranar juma’a da za a wayi gari asabar babu makaranta, Firdausi kam ko ta yi niyyar kwanan sam ba ta iya wa, don da zarar yamma ta yi wayarta za ta fara aiki kamar wata babbar ‘yar kasuwa. Tunda Asma’u ta zo gidan sau ɗaya Ummita ta taɓa zuwa, shi ma wasu dangin Babansu ta rako da suka zo tun daga Maiduguri, ranar Zubaidah ta yi ta zolayarta har suka shirya sama-sama.
Zubaidah zaune a ƙayataccen falonta da tirtsetsen ciki a gaba, kallo take yi da remote a hannunta. A ɓangare guda kuma tana dangwalar madarar L & Z da yatsa tana kaiwa bakinta. Asma’u ta fito daga ɗaki sanye da zumbulelen hijabinta, don tun a gidan Hajiya ta saba da saka hijabi, ta samu guri ta zauna a ƙasa fuska da idanunta na fuskantar allon talabijin. Kusan ko da yaushe a irin wannan lokacin kallon su suke sha a falon, Asma’u ma kallon na ɗebe mata kewa.
“Ni dai ban san ranar da za ki waye ba Asma’u, nan fa a cikin gida muke amma ko yaushe sai ki ɗauki ƙaton hijabi ki rataya kamar wata ɗiyar Limamai, ko zafin garin nan ba kya ji?”
Asma’u ta kama hijabin za ta cire kuma sai Zubaidan ta ce, “A a kinga, nifa ban tilasta miki kan sai kin cire ba, don ban san irin yadda kike son hakan ba, idan kina ra’ayi bar kayanki.”

Duk da haka bayan wani ɗan lokaci sai Asma’u ta cire hijabin tunda ta fuskanci dai Zubaidan kamar ba ta so.

Maigadi ya yi sallama daga ƙofar falo ya sanar da zuwan baƙi a waje. Zubaidah ta tambaye shi “Su waye?”

Ya sosa ƙeya kamar tana kallon sa kana ya ce “Wannan ƙawar taki ce.” Yana faɗin haka ta gane Ruƙayya yake nufi. “Je ka shigo da ita mana, tunda kuma ka gane ta ai ba sai ka shigo ka yi min bayani ba.” Ya juya ya tafi.
Dokar gidan ce duk baƙon da ya zo ba a barinsa shiga kai tsaye ba tare da samun izini daga masu gidan ba, wasu lokutan ma sai an kira shi kansa mai gidan ta waya an faɗa masa kalar baƙin da suka ziyarci gidan duk da na’urar CCTV da ke aiki dare da rana saboda tsaro.

Ruƙayya ta shigo falon, tana ganin Zubaidah ta sa dariya. ‘Yar iska, haka kika zama? Ina ruwan tirtsi bulli.” Suka kwashe da dariya gaba ɗaya lokacin da Ruƙayyan ke ƙoƙarin zama.

Zubaidah ta umarci Asma’u ta kawo musu abin sha. Babu ɓata lokaci ta tashi ta kama hanyar kitcen, yayin da Ruƙayya ta bi ta da kallo har ta ƙule.

“Ba dai mai cikin ki ba ce ta zama haka?”
“Ita ce, me ta zama?” Zubaidah ta ba ta amsa da ƙarin tata tambayar.

“Kamar ba ita ba lokacin baya da za a cire mata cikin nan, yanzu ta fara zama mace cikakkiya, me take yi a gidan nan ne Zubaidah?”

Zubaidah ta muskuta kaɗan a inda take zaune kana ta ce “Wallahi ayyukan gidan nan ne suka fara sha min kai Ruƙayya, na fara gajiya da bauɗaɗɗen ra’ayin Ma’aruf, a watan nan na so in sulale in gudu gida in haihu a can, Hajiya ta ƙi yarda, da na matsa shi ne ta turo yarinyar take kama min wasu ayyukan, kina ganin dai yadda na zama wata sorry, wallahi ina da na sanin ɗaukar cikin nan da na yi tun yanzu.” Zubaidah ta ƙarasa furucinta da jan siririn tsaki ga kuma alamun takaici bayyane a fuska da muryarta.
Ruƙayya ta zuba mata ido tsayin wasu sakanni sannan ta kawar da kai zuwa duban ko ina na cikin falon kamar tana nazarinsa kana ta sake juyowa gare ta ta ce, “Humm ishashshiya, wato har kin yarda da kanki irin haka, ta yadda za ki ajiye zankaɗeɗiyar budurwa kamar wannan tana shige da fice a gidanki da sunan mai miki aiki.”

Zubaidah ta saki murmushi kaɗan a ƙarƙashin zuciyarta tana qara girmama sanin halin ƙawarta da ta yi, ta gane inda ta dosa kai tsaye, sai dai mijinta ko ƙwaya ya sha babu abin da zai ci da wata bush girl, bagidajiya, ragowar fyaɗe Asma’u.

<< Kaddarar Mutum 8Kaddarar Mutum 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×