Skip to content
Part 8 of 23 in the Series Kaddarar Mutum by Mustapha Abbas

Subhanallah! A cikin toilet jini ya ɓallewa Asma’u kai ka ce akuya aka yanka. Duk da Doctor K.B ya tabbatar mata bayan zubar jinin cikin zai fita hankalinta bai kwanta ba, ga tsananin azaba sai dauriya kawai take. Ruƙayya na tsaye a kanta har jinin ya tsaya, ita ta gyara ta ta taimaka mata suka fito. Dr. K.B ya sha mamaki lokacin da ya duba ta ya tabbatar cikin yana nan bai fita ba. Ya ja dogon tsaki. Ruƙayya ta ce, “Yaya dai Honey?”

“Duba duk abin da aka yi cikin nan yana nan bai fita ba. Ta firfito da idanu waje tana kallonsa ta ce, “Garin yaya haka?”

“Shi ne ni ma abin da ban sani ba.” Hankalin Asma’u ya sake tashi, duk a zaton ta uban jinin da ta zubar a banɗaki shi ne cikin.

“Yanzu meye abin yi kenan?” Ruƙayya ta tambaye shi.

Ya ɗan yi jim sannan ya ɗago kai ya dube ta, “Ina ga zan ƙara ƙarfin allurar tunda waccan ba ta karɓe ta ba.”

Asma’u ta saka kuka. Hakan sai ya fara ƙular da Dr. K.B ya ce, “Kin ga dakata, kukan na meye wai?”

“Ni dai Likita tunda ya ƙi fita a qyale shi kawai, bana so in rasa rayuwata don Allah.”

Asma’u ta faɗa cikin kuka.

“Waye ya faɗa miki za ki rasa rayuwarki?” Ba ta ba shi amsa ba ta ci gaba da kukanta. Ruƙayya ta yi tsaki, “Ni na rasa dalilin Zuby na damun kanta kan sai an zubar da cikin nan, ga shi mai cikin ma ba ta so. Kin ga ki kwantar da hankalinki babu abin da zai same ki fa.”

Juyin duniya Asma’u ta ƙi yarda. Tilas Dr. K.B ya kira wayar Zubaidah, ya faɗa mata abin da ke faruwa. Ta ce ya bawa Asma’un wayar. Ta shiga kwantar mata da hankali. “A gwada wannan, idan bai fita ba sai a ƙyale mata abinta tunda haka take so.” Asma’u ta sake amincewa kawai saboda Zubaidah.

Gaba ɗayan su sai da suka yi dana sanin maimaita aikin da aka yi. Zubaidah ta dawo ta iske su a yanayin da Asma’u ba ta san inda kanta yake ba, idan ba ƙudirar Ubangiji ba sauran jinin da ya ragu a jikinta bai zama lallai ya iya jan ragamar rayuwarta ba, tana iya rasa ranta ɗungurungum, still kuma cikin yana nan ko gezau.

Hankalinsu ya tashi ganin yarinyar na neman macewa musamman Zubaidah, ya za ta yi idan ta mutu? Da gaggawa Dr. K.B ya hau mota ya tafi neman jini duk da yana sauri kasancewar lokacin karɓar aikinsa a Asibitin su ya kusa. Da ƙyar ya samo aka sa mata.

Sai gab da sallar magariba ta dawo hayyacinta Zubaidah ta ɗauko ta suka dawo gida Asma’un na kukan da ita kanta ba ta san ko na meye ba.

Hajiya Yaganah ba ta gari, don haka har Asma’un ta warware babu wanda ya san abin da ya faru a gidan, inda Zubaidah ta rufe su Ummita da cewa “Asma’un ce babu lafiya ta kai ta asibiti.”

Daga ƙarshe dai Zubaidah ta ƙudiri aniyar babu ita ba sake shiga hurumin cikin, don Allah kaɗai ya san dalilin ƙin ɓarewar sa.

Bayan Shekara Daya

A cikin shekarar abubuwa da dama sun faru, Zubaidah ta yi aure yanzu haka tana gidan mijinta. Asma’u ta yi rainon cikinta har ta haihu, sai dai rashin sa’ar ɗan bai yi tsawon rai ba ya koma.

Zuwa yanzu Asma’u ta san ciwon ɗanta kuma tana nadama kan wautar da ta yi na yunƙurin zubar da cikin sa. Lokaci guda hankalinta ya yi ƙauyen su wajen Innarta.

Wata rana ta samu Hajiya da maganar. Hajiyar ta tabbatar mata za su je tare sannan matuƙar babu wani ci gaba ta ɓangaren Innar tata za su ɗauko ta su dawo da ita nan gidan Hajiyar.

Asma’u ta nuna farin cikinta a fili duk da ba ta jin hakan zai yiwu. Ƙaunar Hajiya a gare ta kawai daga Allah ne.

A wata ranar daban suka durfafi ƙauyen Somayi bisa jagorancin Asma’u da ke cike da ɗokin sake ganin Innarta, a ranta ta san kamar yadda Hajiya ta faɗa mata babu wani ci gaba da za su tarar wajen Innar sai ma tarin ci baya. A ƙalla shekara da watanni rabonta da ƙauyen, anya ta yi abin da ya dace kuwa?

A kulle suka tarar da gidan don haka ta fara tambayar kanta ko ina Innar ta shiga? Wataƙila ta gaji da zaman kaɗaici da rashinta kusa da ita ta tattara ta koma garin gabas.

Suna tsaye a ƙofar gidan suna tattaunawa da Hajiya kan inda za su fara shiga domin neman Innar. Kafin su ankara tuni jama’a sun fara zagaye su ana kallo.

Tabawa ce ta iso wajen da ɗaurin kayanta a ka, tana ganin Asma’u ta ce, “Wa zan gani kamar Ma’u, ke ce ki ka zama haka? Lallai karuwancin ya karɓe ki, Kaicho! Ina ma Hauwa na da rai da idonta ya gane mata sakamakon ƙin aurar da ke da ta yi ta tura ki binni yawon dandi, ke Ma’u Allah wadaran ki.”

Tabawa na rufe bakinta Asma’u ta silale ta faɗi a gurin, Hajiya Yaganah ta yi kanta a ruɗe tana jijjiga ta, tuni jikinta ya saki laƙwas ta sume. Ko da Hajiya ta fahimci haka ta fara neman ruwa domin farfaɗo da ita, ba ta samu ba, babu kuma alamun jama’ar da ke cike da gurin za su taimaka mata.

Ana cikin haka Munari ƙawarta ta faɗo wajen ɗauke da ruwa a tulu, dawowarta kenan daga rafi ta iske abin da ke faruwa, babu ɓata lokaci ta juye wa Asma’u ruwan a fuska. Sai kuwa ta sauke doguwar ajiyar Zuciya tare da buɗe ido. Bayan da ta gama dawowa hayyacinta ne kuma sai ta ɗora hannu a ka ta rafsa ihu.

“Na shiga uku na lalace, Inna me yasa ki ka tafi ki ka bar ni, bayan kin ce za ki jira in dawo in same ki, ashe ba za mu sake haɗuwa ba? Inna lillahi wa inna ilaihir raaji’un!”

Hajiya Yaganah ta riƙe ta gam tana rarrashinta. Munari na tsaye riƙe da tulu, bin Asma’u kawai take da kallo yadda ta sauya kamar ba ita ba. Ita fa sai jin labari ta yi katsam wai ta bar ƙauyen duk yadda suke da ita.

Maigari da kan sa ya ratso cikin taron har inda suke yana cike da muradin huce haushin yadda Ma’u ta zama sanadin salwantar ɗansa. Tunda ta sa ƙafa ta tafi shima Muntari ya bar ƙauyen, ba a sake jin ɗuriyarsa ba sama da shekara guda, gashi ita ta gama karuwancinta ta dawo shi kuwa har yau ba a san duniyar da yake ba duk kuma saboda tsananin son da yake mata.

“Da gaske ne Ma’u idonki nake gani a ƙauyen nan, kin ƙare yawon dandin shi ne kika dawo? To ai ko kin tafka rashin sa’ar isko uwar ta ki a raye, bare ta gan ki a yadda take so. Kuma in dai wannan shi ne ilimin naki sam bai amfana miki komai ba, Allah wadarai.”

Tasallah (mahaifiyar Muntari) kuwa da ta iso burinta ɗaya ta kama Asma’u ta fara jibgarta har sai ta daina motsi, don haka ko da suka yi arba da ita sai ta cakumo ta tana huci kamar kumurci tana faɗin, “Munafuka yau mai raba ni da ke sai Allah.” Hajiya Yaganah ta angije ta gefe, sai kuwa ta yo kan Hajiyar cike da tsananin masifa.

“Ke tsohuwar Kilaki, hala ke ce uwar ɗakinta a can binnin?” Tuni ai kika bayyana kanki, don tunda na zo wajen nan na gane ki MAGAJIYA, to ki tattara ta ku koma inda kuka fito ku ci gaba da irin rayuwar da kuka zaɓa wa kanku tun kafin in yi umarni a kashe min ku, don rayuwarku ba ta da sauran amfani.”

Hajiya Yaganah ta rasa abin yi sai kallon ikon Allah, tsananin mamaki ya fi rinjaye a zuciyarta fiye da tsabagen takaicin da ya lulluɓe ta. Kai ita ba ta san ma akwai ire-iren waɗannan jahilan mutanen ba a cikin duniya, me yasa suka tsani Asma’u haka, ya aka yi ma ta fito cikin su?

Ta duƙa ta kamo Asma’un ta tashe ta tsaye a ƙoƙarinta su bar wajen, amma sai ta kufce ta tasamma ƙofar shiga cikin gidan da aka kare da wani ƙyauren kara, ta ture ƙyauren ta sa kai ciki, don haka ita ma Hajiyar sai ta rufa mata baya.

Gidan yana nan yadda Asma’u ta tafi ta bar shi, sai tarin shara da bola, wani ɓangaren ma ya fara zubewa. A cikin ɗakin su Hajiya Yaganah ta iske ta ta haɗa kai da bango tana ci gaba da kuka mai ban tausayi. Babu komai a ɗakin in ka ɗauke gadon karar Inna da buhun kayanta, sai sauran tarkacen su na amfanin gida.

“Asma’u ki yi haƙuri ki dangana, dukkan mai rai mamaci ne, tuni Ubangiji Ya tsara ba za ki dawo ki sami Inna ba, ki yi mata addu’a ya fiye mata wannan kukan.”

Kuka sosai Asma’u take kamar ranta zai bar jikinta, Inna ce komai nata, kuma ta tafi ta barta, tabbas yanzu rayuwarta ba ta da wani amfani.

Ihun jama’a ne ke ƙara yawaita daga waje, leƙowar da Hajiya Yaganah za ta yi sai ta ga katangun karan gidan suna ci da wuta ganga-ganga. “La ilaha illallahu Muhammadur Rasulillah Sallalahu alaihi wa sallam! Sun sawa gidan wuta Asma’u, waɗannan wane irin mutane ne? Rayuwarki kawai suke nema, maza tashi mu fita kar mu ƙone.” Kafin Asma’un ta yi wani yunƙuri tuni ta janyo ta suka fice daga gidan ta baya.

Gaggan matasan ƙauyen ne da makamai suka rufa musu baya niyyar su su sake tare su. Hajiya ta tabbatar za su iya aiwatar da komai a kan su idan suka cimma su, don haka ta fisgi Asma’un suka fara keta gudu cikin gonaki.

Sun yi gudu ya kai na tsayin mintuna biyar kafin a daina bin su, tabbas ƙyale su kawai aka yi, don in ba ikon Allah ba babu abin da zai kuɓutar da su, hakan kuwa ya biyo bayan umarnin da Maigari ya yi na cewar a tabbatar sun bar ƙauyen gaba ɗaya, yadda ba za su sake marmarin dawowa ba.

Sun gaji sosai, ga raunika a ƙafafunsu, ga Asma’u har yanzu babu abin da take sai kuka. Hajiya mamakin mutanen ƙauyen ya hana ta sake cewa komai har suka tare mota suka shiga, kamar wasu maguzawa, arnan kan dutse ko irin jahilan farko. Wannan wace irin masifa ce?

Har suka isa gida idanun Asma’u ba su bar zubar da hawaye ba. Abu guda ne a ranta ƙuncin rashin Innarta. Me ya rage yanzu da zai sa ta farin ciki a duniya?

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 1 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kaddarar Mutum 7Kaddarar Mutum 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.