"Wai tsoro na kike ji ko me?"
Ta yi masa shiru.
"Ko ina miki kama da masu satar mutane ne?"Muryarta na rawa ta ce "A a."
"Amma duk inda kike da zarar na zo wurin sai ki tashi ki gudu, ke ina lura da ke duk hanyar da kika san za ki bi don kaucewa haɗuwa da ni ita kike bi Why?" Asma'u ta marairaice murya sosai "Don Allah ka yi haƙuri."
"Da haƙurin ta mutu sadakar nawa kika bayar? Sarkin bada haƙuri. Zolayar ta ɗan ba ta dariya, sai dai ba za ta. . .