Skip to content
Part 14 of 23 in the Series Kaddarar Mutum by Mustapha Abbas

Ba ta tsaya ba, ta wuce su a qoqarinta na isa ɗakinta, tana jiyo sa’ar da Ruƙayya ta ja tsaki tsuut! Lamarin da ya ja hankalin Suwaiba kanta ta ce, “Ya ya dai shegiya naji kina tsaki, ke da wa?” Bushira ce ta cafe, “Ita da yarinyar nan ne, kawai ta ɗauki karan tsana ta ɗorawa ‘yar mutane babu laifin tsaye ba na zaune.”

“Yar mutane fa kika ce, kin san asalinta ne? To ita kanta Zubaidar ba ta san daga inda ta fito ba.”

Iyakar abin da kunnuwan Asma’u suka ji kenan ta tura ƙofar ɗakin ta shige, ta yi imanin duk wani abu da zai biyo bayan wannan ma aibatawa ce da cin zarafi gami da kushe daga Ruƙayya, kuma babu mai iya taka mata burki, addu’a kawai za ta ci gaba da yi kan duk sharrin da ta ke nema mata ya ƙare kanta, domin ƙiyayyar da Ruƙayyan take mata ta yi yawa, a ce ko ganin mutum ka yi sai gabanka ya faɗi?

Mintuna masu yawa ta ɗauka a cikin ɗakin tana jiyo hargowarsu da sautin music da yake tashi a falon, so take ta fita zuwa kitchen ta ɗauki abincinta ta ci, amma ba za ta iya ba duk da tsananin yunwar da ke cinta, tun karin safe har kawo yanzu ƙarfe biyar da wasu mintuna ba ta sa komai a cikinta ba saboda jarrabawar da ta sha kansu. Banɗaki ta shige ta ɗauro alwala ta tayar da sallah. Bayan ta idar ma ci gaba ta yi da zamanta a ɗakin, domin za ta iya jure tsananin yunwar da ta shigo da ita har zuwa lokacin da su Ruƙayya za su fita, don ta tabbatar ba a gidan za su kwana ba.

Sai dai kuma misalin ƙarfe shida sai ga Zubaidah ta shigo ta same ta idanunta a kanta tana nazarin yanayin da ke kan fuskarta “Asma’u lafiya kike kuwa?”

“Lafiya ƙalau Aunty.” Ta amsa mata da ƙoƙarin ƙirƙirar fara’ar dole a kan fuskarta.

“Don Allah daure ki shiga kitchen saboda ina baƙi, yaya jarrabawar taku?” Asma’u ta zuro ƙafafunta ƙasa daga kan gado za ta miƙe tsaye ta ce, “Zuwa jibi ma za mu kammala in sha Allah Anti.”

Lokacin da suka fito idanun Asma’u da Suwaiba suka fara yin arba tana ta tiqar rawa cikin ƙwarewa ba ta ko jin kunyar matsatstsiyar sutturar da ke jikinta, Ruƙayya da Bushira kuwa daga zaune suke ta su rawar bakunansu na bin waƙar Davido da ke tashi, ganinta bai sa sun daina ba, Suwaiba ta yi juyi, ta yi girgiza sai ta kai hannu suka kashe da Bushira ji kake tass! Sannan shewa ta biyo baya, Zubaidah ta yi dariya suka shige kitchen tana faɗin “Allah Ya ya yafe miki Suwaiba.” Sai da ta tsara mata yadda za a girka abincin dare sannan ta fita ta bar kitchen ɗin.

Bayan sallar magariba suka bar gidan, sai dai sun yi wa falon kaca-kaca, wanda kuma gyara da kimtsa wajen da suka ɓata duk aikin Asma’u ne, don Zubaidah tuni ta haye sama.

Saboda tsabar aiki Asma’u ba ta samu fita daga kitchen ba, har bayan magariba, lokacin Ma’aruf ya dawo, ya jima a tsaye yana nazarin falon, sannan ya tsince remote-remote da ke zube a ƙasa ya adana su a muhallinsu kana ya tsallake kwalaye da gwangwanayen lemo, shinkafa da ƙasusuwan kazar da aka zubar ya haye sama.

Sai da Asma’u ta kammala aikin da take a kitchen sannan ta fito ta gyara wajen ta koma ɗaki don ta yi Sallah.

Bayan ta idar da sallar isha’i ta koma ɗaukar abincin darenta kafin su sauko ƙasa, sai dai ta makara, domin tana shiga kitchen, ta fara zuba abinci kenan ta ji motsin saukowar su kamar suna hayaniya, ba kasa kunne ta yi ba amma tana jiyo duk abin da suke faɗa kasancewar ɗaga murya suke musamman Ma’aruf.

“Tambayar ki fa nake Zubaidah, ki ban amsa.”
“Amma saboda Allah Ma’aruf don kawai ta zo gidan nan sai ya zama laifi, har ka ke titsiye ni kana min shouting irin haka, ko kuwa idan ta zo don yarfi kawai sai in kore ta?”

“Yes, ki yi hakan mana, tunda ai kin san ba na son alaƙarki da ita, ke ko Ruƙayya fa ba da son raina kike tarayya da ita ba, don haka kar shegiyar da ta sake zo min gida.”

Hoɗijan! Duk da Asma’u ba ta ga fuskar Zubaidah ba amma ta san ranta in ya yi dubu ya bala’in ɓaci, sai kuwa ta sake jin muryarta cikin hasala.

“Look Ma’aruf! Ba fa tun yau ba na lura da take-takenka, dama dai ba Suwaiba kaɗai ba ce baka son gani a gidan nan, ka fito fili kawai ka faɗa min baka son hulɗar da nake da ƙawaye na.”

Asma’u na son fitowa daga kitchen saboda ta tabbatar su da komawa sama sai lokacin barci, don haka ta wanke hannun da ta ci abinci ta yi fitowarta, amma kuma ga mamakinta sai ta ga babu ko ɗayansu a falon sai kayan abinci shirye a dinning, alamun da ke nuna rikicin na su ya kai babu wanda ya saurari abincin, ta shige ɗaki tana wassafa abin da ya faru.

Yau Asma’u ta tabbatar Ma’aruf ba ya ƙaunar hulɗar matarsa da su Ruƙayya kamar yadda ita ma da ba a bakin komai take ba a gidan abun ke ɗaɗa ta da ƙasa, tana da yaƙinin Hajiya ma ba za ta so ba, me zai hana Zubaidah ta zubar da shaiɗanun ƙawayenta tunda har ran mijinta na ɓaci kan tarayyar ta da su?

Da tana da iko da ta ba ta shawara kan haka, duk namiji mai kishin matarsa ba zai so alaƙarta da ire-iren Suwaiba Fashion ba, yanayinta a fuska ma ya isa gamsar da kai tsabar gogewarta a harkar bariki, sam babu kuskure ka siffanta ta ko kira ta da ‘yar ƙwaya.
Kusan kwanaki uku zaman ma’auratan kadaran-kadaham, sai su zauna a guri ɗaya su ci abinci su tashi ba tare da ɗaya ya kula ɗanuwansa ba, taƙamar Ma’aruf ai ba Zubaidah ta girka abincin ba.

Ita kuwa Zubaidan ma ko a jikinta wai an tsikari kakkausa, ƙoƙarinta kawai ta nuna masa ta ji haushin abin da ya yi mata, tana kuma so ta ƙwaci ‘yancinta na ci gaba da tarayya da duk wanda ta so gami da watayawa irin yadda take so, tunda ai ita ba irin matan da za a aura a kulle ba ne.

Miji da mata sai Allah, a cikin satin kuma Ma’aruf da Zubaidah suka shirya, suka koma suka ɗinke kamar da ko ma fiye da haka, don yanzu wani salo suka tsiro da shi na nunawa junansu so a bainan nasi, duk da sun san cewa Asma’u na gidan, rayuwar soyayyar su suke yadda suka ga dama kamar da gayya, wannan ya ƙara wa Asma’u yawan zaman cikin ɗaki.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kaddarar Mutum 13Kaddarar Mutum 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×