Wani yamutsatstsen tsoho ya fito daga cikin garken dabbobi yana ranƙwafawa da ƙyar don ya fi tshohuwar tsofewa nesa ba kusa ba.Waɗannan tsofaffi sune kakannin Asma'u wato waɗanda suka haifi mahaifiyarta, tsayawa kawai namijin tsohon ya yi da sandarsa yana kallonta, can ya ce, "Asma'u ke ce? Ikon Allah." Hawaye suka tsiyayo daga idanun Asma'u ta ce, "Ni ce Kaka."
Kafin wani lokaci ciki da wajen gidan ya cika taf da mutane, kasancewar wasu tun a hanya sun ganta, wasu kuwa biyo ta suka yi don ganewa idonsu inda baƙuwar Balarabiyar za. . .