Skip to content
Part 18 of 23 in the Series Kaddarar Mutum by Mustapha Abbas

Wani yamutsatstsen tsoho ya fito daga cikin garken dabbobi yana ranƙwafawa da ƙyar don ya fi tshohuwar tsofewa nesa ba kusa ba.
Waɗannan tsofaffi sune kakannin Asma’u wato waɗanda suka haifi mahaifiyarta, tsayawa kawai namijin tsohon ya yi da sandarsa yana kallonta, can ya ce, “Asma’u ke ce? Ikon Allah.” Hawaye suka tsiyayo daga idanun Asma’u ta ce, “Ni ce Kaka.”

Kafin wani lokaci ciki da wajen gidan ya cika taf da mutane, kasancewar wasu tun a hanya sun ganta, wasu kuwa biyo ta suka yi don ganewa idonsu inda baƙuwar Balarabiyar za ta shiga, tuni dai labari ya karaɗe ko ina yau ga ɗiyar Hauwa da mai gari Nuhu ya kora aka neme ta aka rasa ta dawo daga binni. Abinka da ƙauye duk ƙanƙantar sirrinka kowa sai ya sani.

Tsofaffin nan suka rasa inda za su saka ta don murna, ita kuwa kuka kawai take yayin da Innaro ma ta biye ta suka haɗu suna ta yi. Bayan sun nutsu tsohuwa Innaro ta ce, “Ina shi wannan abu da ya samu?” Asma’u ta san cewa cikin da ta tafi da shi take nufi ta ce, “Da aka haife shi ma bai zo da rai ba Kaka.”

“Allah mai iko! Ai Asma’u daga ke har marigayiya Hauwa kun yi wauta da kuka yanke wannan ɗanyen hukunci, ina ke ina tafiya binni kan wannan matsala? Muna raye ba sai ki zo inda muke ba tunda su waɗancan jahilcin su ido ba zai bar su su fahimci ƘADDARA ba, sai bayan kin tafi muka samu labari.”

Tshoho Arzuka ya ce, “Wato wannan kaxai ishara ce ga mai garin yamma, ko dama shi da sakaran wazirinsa suna can suna girbar abin da suka shuka, shi kuwa yaron ma da ya yi miki wannan aika-aika yana nan ya haukace tuburan, bayan ya tona asirin kansa, mu kam sai dai mu gode Allah da ya dawo mana da ke lafiya.

Asma’u ta share ƙwallar idanunta.
“Tabbas haka ne Asma’u, sai bayan rasuwar Hauwa abubuwa suka yi ta bayyana, Waziri ya fi kowa gwada rashin imani, shi da ya sa wancan yaron ya bi dare ya keta miki haddi kawai saboda Muntari ɗan mai gari ya ce babu wadda yake so sai ke, shi kuwa ya ci burin aura masa ɗiyarsa Ramatu, wanda yanzu haka anyi auren babu yadda yake, saboda dama aure ne da aka gina bisa son zuciya, ke dai da ba ya so ya aura suka samu suka yi sanadin da kika sa ƙafa kika bar Somayin, sai dai fa shi dama sharri ɗan aike ne, mai shi yake komawa.

Haka ce ta faru ga Waziri, domin har yanzu bai samu abin da yake so ba. Bayan tafiyarki Muntari shi ma ya shiga duniya, ƙauyen Somayi sun tsinci kansu cikin nadama da dana sanin abin da suka aikata miki, yanzu kowa ya san gaskiya, an gane makircin Waziri da uwar ɗakin mai gari ita mahaifiyar Muntari.”

Yana faɗin haka ta gane Tasallah yake nufi, ko dama can ta san Tasallah ba ta ƙaunarta, bare a ce ɗan da ta haifa ya mato a soyayyarta, dole ta yi komai don ta musguna mata, ita kam sai abin da ta ji daga bakin tsofaffin. Innaro ta tashi ta kawo mata ƙwaryar fura da nono, ta sha ta ƙoshi tana tuna baya, rayuwar ƙauye.

Kafin ta kammala ta haɗa mata ruwan wanka, duk da kasancewar ruwan jajir da shi haka ta shiga ta wanke kanta tas, to ai shi ne asalin ruwan da aka wanke ta tun dirowarta duniya, ta fito ta sauya kayan jikinta.

Daga lungu-lungu, saƙo-saƙo ake zuwa ganinta Asma’u domin ta fita daban, ma’ana babu irinta a cikin ƙauyen. A zahirin gaskiya wannan ita ce ainihin rayuwarta, ba waccan rayuwar da ta baro ba, ko ba komai yanzu tana tare da waɗanda suka zama dolenta, ba kuma za su taɓa korar ta ba.

Ma’aruf Kano

Duk inda yake tunanin zai samu Asma’u a gidan ya je bai ganta ba, idan har ba ta kitchen to tana ɗakinta, idan kuwa duka ba a same ta a nan ba sai makaranta wanda ita kuma makaranta tana da lokaci, muddin ba jarrabawa suke ba ƙarfe ɗaya da rabi a gida take mata, bai kawo komai a ransa ba kasancewar a wasu lokutan Zubaidah kan aike ta gida musamman ranakun weekend, yanzu ma abin da ya tsammana kenan, to amma kuma misalin ƙarfe biyu da rabi na yamma da ya kira wayarta sai ya ji a kashe.

Wasa-wasa ƙarashen wunin ranar duka ya yi shi ne yana gwada lambar Asma’u amma ba ta shiga har washegari, a ƙalla kwanaki biyu kenan, don haka da dare suna cin abinci ya kasa jurewa ya tambayi Zubaidah.
“Honey wai ina kika aiki yarinyar nan ne?”

Ta dube shi da wani irin zargi a qwayar idonta, wato abin nasu har ya kai haka? Lallai maganar Ruƙayya ta tabbata, kuma gara da ta kaɗa Asma’un ta ta tafi
“Wace yarinya kake nufi ne wai?” Ta faɗa cikin nuna halin ko in kula.

“Ban gane ba, wace yarinya zan tambaye ki da ta wuce Asma’u, yau kwana biyu ban ganta a gidan nan ba, ko tana gidan Hajiya?” Ya rufe tambayar tashi da kallon cikin idonta.
“Ba ta gidan Hajiya, ta tafi garinsu.”

Cak Ma’aruf ya tsaya da cin abincin riƙe da cokalin da ya ɗebo shinkafa yake shirin kai wa baka ya kafe ta da ido.

“Garin su kuma ana makaranta? Me ma zai sa ta tafi garin su, bayan abin da ya faru a zuwan da suka yi da Hajiya? Zubaidah faɗa min gaskiya me kika aikata ne?”

Sam Zubaidah ba ta iya ƙarya ba, me ma zai sa ta yi masa ƙarya kan hukuncin da ta zartar take ganin shi ne dai-dai, babu yadda za a yi ta bar hakan ta faru.

“Na sallame ta Ma’aruf, so what?” Ta faɗa da ‘yar ɗaga murya don ta fara tunzura.
Tsam Ma’aruf ya ajiye cokalin, ba tare da ya ɗauke ido daga kanta ba, “Kin sallame ta da izinin wa?”

“Da izinin wa kake so in sallame ta, nifa na kawo ta gidan nan.”

Ture filet ɗin abincin ya yi gefe yana karkaɗa ƙafarsa guda ɗaya fuskarsa kuma ta canza zuwa yanayin ɓacin rai, sai dai kuma dole yana buƙatar sassauta zuciyarsa, jim kaɗan kamar ba zai yi magana ba, can kuma sai ya ce, “A kan me kika sallame ta?”

“Zamanta a gidan nan ne ya ƙare, wai ko ba ni da ikon yin hakan ne?

“Ba ki da iko Zubaidah, kuma ban san baki da hankali ba ma sai yau, a kan me za ki bar ta ta tafi wajen nan ita kaɗai?”

“Saboda ita kaɗai ɗin ta zo.” Ta ba shi amsa kai tsaye kana ta ɗora da faɗin.

“Kuma dama ai kai haka za ka gani, bani da hankali, amma ni nan da hankalina, ras nake, sannan yanzu na ƙara tabbatar da abin da ake faɗa min, cewa kana sonta kuna cin amanata a ɓoye, amma Ma’aruf ka bani kunya, kamar kai ka tsaya kan wannan tsintacciyar magen, marar asali?”

Zuciyarsa ta fara tafarfasa, ga haushin abin da ta aikata sannan tana yada masa maganganu kamar wani wanda ta haifa, ya maimaita kalamin da ta faɗa a ransa sannan a fili ya ce, “Wa ya faɗa miki cewa ba ta da asali? Wataƙila ta fi ki asali ma, ki kula da abin da kike faɗa.”

A fusace ta miƙe tsaye, manyan idanunta suka ƙara girma sosai a kansa, “Ma’aruf ni kake jifa da waɗannan kalaman kan waccan ƙasƙantacciyar yarinyar?”

Murmushin takaici ya yi, duk kalma guda da za ta fito daga bakinta ƙara tunzura shi take ji yake tamkar ya sa mata duka saboda haukan da ta yi ya ce, “Babu daɗi kenan, ke yanzu me kika gama faɗa kan ta?”

“Amma ai ni matarka ce, ya dace ka faɗa min haka?” Ta tambaye shi.

“Kenan ke ya dace ki tozarta ta, ki kore ta daga gidan nan ba da sanin kowa ba, saboda ban isa da ke ba? To ki sani duk abin da ya samu yarinyar nan za ki biya farashinsa, don ita ma ‘yar adam ce mai daraja, ba daga sama ta faɗo ba.”

Ransa a ɓace ya tashi kawai ya bar mata gurin. Ta ji haushi sosai, ta kuma sha alwashin sai ya gane ita ya wulaƙanta.

Da fari Zubaidah ɗaukar abin ta yi kamar wasa, ba ta taɓa tunanin cewa korar Asma’u zai zo mata da irin wannan matsalar ba.

Babu inda tashin hankalin yake sai da Hajiya ta samu labari, hankalinta ya tashi, ranta in ya yi dubu ya ɓaci, har kuka ta yi don ba ta san duniyar da Asma’u za ta faɗa ba tunda ta yi imanin ba za ta koma ƙauyensu ba.

Tattaki ta yi ta zo har gidan ta sa Zubaidah a gaba da faɗa ta inda ta shiga ba ta nan take fita ba, muddin tana so su zauna lafiya ta je ta nemo mata Asma’u duk inda ta kai ta.

Rantsuwa Zubaidah take yi bakin ranta ba ta san inda Asma’u take ba, ita dai ta san ta saka ta a motar Zinder inda daga nan ne za ta kama hanyar ƙauyensu.

“Amma kin cuce ni, shin lallai ne sai kin mai da ta ƙauyen su, ko ita ta ce miki tana son tafiya can? To wallahi muddin wani abu ya samu yarinyar nan ba ni ba ke, azzaluma!”

A ranar Ma’aruf da Hajiya suka nufi Somayi. Sai dai babu inda ba su bincika ba a ƙauyen amma ba ta nan, tashin hankalinsu ya ƙaru duk da Hajiya na da kyakkyawan zato kan Asma’u ba za ta shiga duniya ba, duk inda take ita mai tsoron Allah ce, amma rashin sanin hannun da za ta faɗa shi ne babban abun tashin hankalinta, anya Zubaidah tana so ta gama da duniya lafiya? Ma’aruf ke kwantar mata da hankali har suka dawo gida.

<< Kaddarar Mutum 17Kaddarar Mutum 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.