Skip to content
Part 5 of 23 in the Series Kaddarar Mutum by Mustapha Abbas

Karfe 03:35 PM

A hankali Asma’u ta buɗe idanunta, ga tarin mamakinta sai ta riski kanta a wata duniya ta daban, sannu a hankali ta fara gane komai, sannan abin da ya faru da ita ya fara dawo mata daki-daki cikin kwanyarta, ko ba a sanar da ita ba ta san nan inda take kwance gadon Asibiti ne. Ta yunƙura za ta tashi zaune ba tare da tana da dalilin yin hakan ba.

“Yauwa shi kenan ma ta farka.”

Muddin ba ƙarya kunnuwanta suka faxa mata ba muryar da ta ji muryar Hajiya Yaganah ce. Ta kai dubanta gare ta lokacin da take ƙarasowa jikin gadon.

“Ki bi a hankali yarinya, akwai drip a hannunki.”

Asma’u ba ta san me ake kira Drip ba, amma sai ta tsinci kanta da bin hannunta na hagu da kallo, inda aka maqala mata wata siririyar farar roba kamar hanji, sannan ta sake duban Hajiya sai hawaye sharr daga cikin idanunta.

“Likita ta farka fa.”

Muryar Hajiya Yaganah a karo na uku.

Sai ga Likitan ya ƙaraso gurin, ya dubi Hajiyar “Ai ke ruwan ma ya ƙare baki kula ba, bari a cire mata.” Ya kai hannu a hankali ya zare mata farar robar duk da haka sai da ta ɗan ji zafi, ya sa auduga fara tas ya liƙe wajen wanda har jini ya fara ɓullowa kaɗan.

“Sannu yarinya kin ji.” Hajiya Yagana ta faɗa cike da nuna tausayawarta gare ta. Gyaɗa mata kai ta yi kurum. “Yanzu ya kike jin jikin naki?” In ji Likita yana duban ta.

Ko kusa ko alama ba ta yi zaton za ta iya furta wani kalami ba idan ta buɗe baki amma sai ta tsinci kanta tana bawa Likita amsar tambayoyin da yake mata tiryan-tiryan.

“Alhamdulillah Hajiya, ina ganin tunda jikin nata ya yi kyau an jima kaɗan za a baku sallama, sai ta ci gaba da shan magungunan da aka siya, Ulcer ne ta mata mugun kamu. A gaskiya kuma ya kamata ku riƙa ziyartar Asibiti a kai-akai don kulawa da lafiyar abin da ke cikinta.”

“Shi kenan likita. Insha Allahu za a kula.”

Ba su ƙara awa guda a Asibitin ba aka sallame su. Hajiya ta faɗa mata da safiyar Allah aka tsince ta a cikin tasha babu yadda take, wasu sun ɗauka ma ta mutu, sannan ta ba ta haƙuri kan rashin dawowa ta tafi da ita kamar yadda ta alƙawurta mata bisa wasu uzurori da suka hana faruwar hakan.

“Babu komai Hajiya, na gode.” Cewar Asma’u dai-dai lokacin tuni sun fito daga cikin asibitin.

Sai da suka hau babur mai ƙafa uku, tafiya mai ɗan nisa ta kawo su unguwar goron dutse ƙofar gidan Hajiya Yaganah. Asma’u na biye da ita suka sa kai cikin soron gidan. Har sau uku Hajiya Yaganah na sallama babu wanda ya amsa. Ta wuce ƙofar wani ɗaki da ke kulle, ta ɗauko mukulli cikin jakarta ta buɗe ta shiga, sannan ta umarce ta ita ma ta shigo.

Ɗakin a tsare yake kuma a gyare tsaf kamar yadda wadataccen tsakar gidan yake, duk da cewa ba wasu kayan alatu ba ne na ku zo mu gani, gado ne da sif da madubi, sai ledar tsakar ɗaki mai kyau da aka shimfiɗa, amma dai Asma’u tunda take a rayuwarta ba ta tana ganin ɗaki mai tsaruwar sa ba.

Hajiya ta zuba mata ruwa ta kai mata banɗaki sannan ta dawo ɗakin ta umarce ta ta je tayi wanka. Tabbas Asma’u ta ji daɗin jikinta musamman wani irin ƙamshi da sabulun ke yi.

Bayan ta koma ɗakin ne ta tarar Hajiya ta ajiye mata man shafawa kusa da jakarta amma Hajiyar ba ta ɗakin, ta ɗauka ta fara shafawa, kai gaskiya rayuwar nan ko yaya take tafi ta ƙauyensu, wa ma zai haɗa? Asma’u ta kammala shafa man ta tashi ta buɗe ledar kayanta, ta ɗauko kayanta ta saka, sai kuma tunanin Innarta yayo mata dirar mikiya.

Hajiya Yaganah ta dawo ɗauke da kwanon abinci Indomie ce ta silala mata, ta iske ta tana faman zubar da ƙwalla.

“Yarinya mene ne sunanki ma?”

“Sunana Asma’u.” Ta faɗa mata da muryarta da ke shirin fasa kuka.

“Tashi maza ki ci abincin ki fara shan magungunanki yanzu kamar yadda Likita ya faɗa, kuma ya kamata ki cire damuwa da yawan tuna abin da ya faru da ke daga ranki kin ji?”
“Hajiya ba tunanin komai nake ba face Innata, ban san halin da take ciki ba, ta saba da ni sosai, ban ce miki za ta iya rayuwa cikin farin ciki ba tare da ina kusa da ita ba.”

Hajiya Yaganah ta girgiza kai, “Wannan hasashenki ne, bai zama lallai ya faru ba, ke dai ki dogara ga Allah, ki yi ta mata addu’a. Da izinin Allah babu abin da zai same ta, ki zauna nan tare da ni da ‘ya’yana har Allah Ya taimake ki haife abin da ke cikinki kamar yadda Innarki take so, kar ki sake ki wofantar da kyautar da Allah Ya ba ki kin ji?”

Asma’u ta goge hawayen fuskarta tana tuna quncin da aka jefa rayuwarta, ita ba a gida ba, ita ba a daji ba, sannan ita ba budurwa ba, ita ba bazawara ba, da wane suna ma za a kira ta ne?

***
Satinta uku cif ta gama fuskantar yadda rayuwar gidan nan take. Hajiya Yaganah kasuwanci take, kasancewar akwai shagon mijinta da ya rasu a kantin kwari, babban ɗanta ke zama a shagon yayin da ita kuma take jigila da wasu kayan tsakanin garuruwa, har ƙasashe irin su Nijar. Duk wani abu da take yi tana yi ne don rufuwar asirin junansu tare da ‘ya’yanta, da alamu babu wanda ke tallafa musu ita da marayunta.

Sauran ‘ya’yanta huɗu duk mata ne kuma kowa da halinsa. Nasir shi ne babba zai kai kimanin shekaru ashirin da takwas, yana da kirki tamkar mahaifiyarsa sannan akwai Zuciya da ƙoƙari wajen neman na kai, tabbas ya san abin da yake.

Zubaidah ke bi masa ita ma babu laifi tana da kirki dai-dai nata don ita ta fara janta a jiki, ba ta fiye zama a gida ba, duk da Asma’u ta san makaranta take zuwa sai dai ai makaranta tana da lokacinta, ga ƙawaye barkatai. Innarta kuma ta taɓa faɗa mata yawan tara ƙawaye ba alkhairi ba ne, mafi akasari ta nan ake samun gurɓatar halaye da tarbiyya, baya ga haka ma tana ganin yadda Hajiya ke yawan mata faɗa kan halayen nata.

Ummita ce ke bi mata kusan kansu ɗaya a tsayi, sai dai ana saurin gane Zubaidah ce babba a duban farko, miskila ce ajin ƙarshe, tana da son nuna isa da ɗagawa ga dukkan lamuranta, sam Allah bai haɗa jininta da na Asma’u ba. Ita ta fara yi wa Hajiya ƙorafin kwaso musu Asma’un gidan da ta yi. Firdausi wadda suke ɗibar kama sosai ita ma ba ta da kirki ko kaɗan, ga fitsara da raina yayyunta. Ƙararamar cikinsu ita ce Maryam, cikin ɗan lokacin ta karance halayyarsu don ba sa ɓoyewa ko kaɗan.

Zubaidah da Ummita ɗakunan kwanansu daban-daban, akwai wata irin rashin jituwa ta faɗan saƙo tsakaninsu, ba wuya ka ji sun hautsine da zage-zagen juna. Wani lokacin har da dambe. Maryam da Firdausi ɗaki guda suke kwana, zuwanta Hajiya ta haɗa su suka zama su uku.

Cikin su duka biyar ɗin nan Hajiya Yaganah ba ta yarda ta sanar da ko wannen su komai game da Asma’u ba, ta dai ce musu daga ƙauyen su Hajiya Balaraba ta ɗauko ta mijinta ne ya rasu. Sai dai Zubaidah da yake wayayyiyar gaske ce ba ta kuma gamsu da zancen Hajiyar ba, cikin hikima ta ja Asma’un a jiki har sai da ta ji abubuwan da suka kamata ta sani game da ita, amma dai ba ta yi gigin faɗawa sauran ‘yan uwanta ba, don ta san Hajiyar ta su ba ta so.

Tun Asma’u ba ta sakewa cikin gidan saboda irin kallon ƙasƙanci da tsangwamar da su Ummita suke mata har ta saba, domin daga baya ta gane raina komai nata suka yi musamman irin sutturun da ta zo da su take sawa. A cikin kwanakin Zubaida ce kaɗai ta taɓa mata kyautar kaya cikin nata da suka mata kaɗan.

Asma’u ba ta da ƙiwa ko kaɗan, zage wa ta ke ta cire duk wata ragowar ganda da ke jikinta tana musu bautar aiki, ita ce kama musu wanki, wanke-wanke, girki da sauran ayyukan da Hajiya ta ɗora musu. Wannan dalilin kaɗai ya sa suka fara shiga sabgarta. Duk wulaƙancin Ummita sai da ta sassauta mata ta wannan fannin, don Allah Ya yi ta da shegen son jiki.

Son samunta a ce ta wuce ajin wanke-wanke a gidan tunda ga su Firdausi nan, amma sam Hajiyar ta ƙi fahimtar ta, a ganinta me suke tsinana mata? Makaranta ce kurum, banda ita sai kwanciya da yawon su na babu gaira ba dalili. Tilas dai a zauna kan tsarin da Hajiyar take so idan wannan ta yi yau, gobe waccan ta yi.

<< Kaddarar Mutum 4Kaddarar Mutum 6 >>

3 thoughts on “Kaddarar Mutum 5”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.