Subhanallah! A cikin toilet jini ya ɓallewa Asma'u kai ka ce akuya aka yanka. Duk da Doctor K.B ya tabbatar mata bayan zubar jinin cikin zai fita hankalinta bai kwanta ba, ga tsananin azaba sai dauriya kawai take. Ruƙayya na tsaye a kanta har jinin ya tsaya, ita ta gyara ta ta taimaka mata suka fito. Dr. K.B ya sha mamaki lokacin da ya duba ta ya tabbatar cikin yana nan bai fita ba. Ya ja dogon tsaki. Ruƙayya ta ce, "Yaya dai Honey?"
"Duba duk abin da aka yi cikin nan yana nan bai. . .