Bayan dukkaninmu mu tattaru a falo sai Fatima zarah ta fara yin bayani kamar haka;
“Muna zaman mu cikin farin ciki kawai wata rana muna zaune muka fara jin kururuwar jama’a da kuma karar bundugu ga karar fashewar abubuwa masu firgitarwa hankalinmu yayi matukar tashi muka rasa yaya zamuyi gashi lokacin mahaifinmu baya gida. Mun futo waje muka ga ana ta guje-guje hakan yasa muma muka yanke hukuncin mu gudu duk da cewa bamusan inda zamuje ba.
Muna cikin gudu ne bayan munyi nisa sosai sannan nakula da cewa su mamata batare muke dasuba nayi kokarin komawa amma saboda yawan jama,a nakasa daganan na yanke hukuncin tafiya ban tsayaba saida na tabbatar nayi nisa da unguwar sai bayan komai ya lafa nafara tunanin ta ina zan fara dubasu.
Naduba duk inda yakamata ace naduba amma bangansu ba sai daga baya nakejin labarin akwai mutanen da basu samu damar fita ba daga unguwar kuma su yan ta,addan suna tsare dasu domin kuwa sune suke rike da yankin a yanzu haka bansaniba ko suna cikin mutanen da aka tsare ko koma sun mutu.” Koda ta zo daidai nan a zancenta sai kuka ya kwace mata.
Da kyar ta samu ta dawo hayyacinta sannan ta ci gaba da cewa, “bansan ina zanjeba bansan wa zankaiwa kukana ba tadubeni tace kaine kawai ka fara fadomin a rai kuma abinda kawai nasani shine agarin kano kake dukda nasan cewa kano tana da girma bansan ta ina zanfara dubaka ba amma nataho da yakinin Allah zai hadani da kai bayan nashigo kano kwana da kwanaki ina ta yawon nemanka bansameka ba.
Shine na yanke hukuncin na namutu kawai na huta nahawo titin nan ne ina sane dan nasamu wata motar ta bigeni na mutu kozan huta amma sai Allah yaturo min kai adaidai lokacin tasake fashewa da kuka ta fada jikin mamanmu tana sani irin kuka mai karyarda zuciya nikam tuni tsananin tausayinta ya kama zuciyata musamman danaga kowa na falon hawaye yakeyi domin muma munada yan uwa a unguwar.
Saukar hawaye naji akan kumatuka na nayi saurin gogewa sannan natashi tafice daga falon nabar mama tanata lallashinsu itada kanwata halima haka aranar gidan yawuni tsit tamkar ba wata halitta mai numfashi acikinta gidan da yasaba da walwala da hayaniya saiya koma tamkar gidan makoki haka mukaita zama cikin wannan yanayi na tsawon lokaci sannan gidan yafara komawa daidai.
Akwana atashi komai yanata daidaituwa fatima zarah tazama yar gida shakuwar dake tsakaninmu kuwa ta nunku koda yaushe muna tare bacci ke rabamu da ita Komai yana cigaba da tafiya daidai har aka samo mata makaranta tacigaba da karatunta amakarantar su halima kanwata.
Wata rana ina zaune dayamma sai tazo take cemin tagani a labarai cewa an kori wadannan yan ta,addan yanzu ma gari yayi lafiya kowa yakoma gidansa da zama saboda haka tanaso taje taduba iyayenta.
Nan take naji wani irin yanayi domin kuwa banson wani abu dazai rabamu da ita koda na sakan daya dukda cewa labarin na murna ne amma nakasa nuna farin ciki dakyar na iya kakalo murmushi muryata na rawa nace Alhamdulillah wannan kyakykyawan labari ne amma tunda kinga yanzu muna tsaka da jarrabawa kibari idan mungama nanda sati biyu sai muje tare.
Takara matsowa inda nake ta rike hannayena tace dani bazan iya jiran sati biyu ba batareda naje naga halinda suke ciki ba tun bayan rabuwata dasu bansake samun bacci medadi ba kullum cikin tunaninsu nake inaso naje nagansu nasamu nutsuwa kayi hakuri idan kagama jarrabawar saikazo mudawo tare tunda nima zandawo na karasa nawa jarrabawar.
Zuciyata bataso ba amma bayadda na iya dole na hakura kashe garin ranar da sassafe fatima zarah tagama duk wani shirin da zatayi na tafiya muka fito na rakata tashar mota tun fitar mu daga gida bawanda yafurta koda uffan kawai sake sake muke azuciya jinake kamar na hanata amma banida wannan damar.
Muna tashar tsahon kusan minti talatin amma bawanda yayi magana daga nan sainaga ta ciro zoben hannunta ta mikomin sannan tace gashi ka ajiyemin nan da sati biyun idan katashi zuwa saika tahomin dashi adaidai lokacin ne kuma tamike tanufi motar da zasu tafi.
Har tashiga motar suka fara tafiya banyi magana ba domin kuwa kukana nake boyewa acikin shirun da nayi motar tana tafiya saiga wasu zafafan hawaye sun zubo akan kumatuna kayi saurin juyawa adaidai lokacin da nasa hannu ina share hawayen haka nadawo gida nashige daki inata tunaninta.
Bayan kamar awa uku ne da tafiyar tasune naji wayata tafara karar alamun kira yashigo ko dubawa banyi ba domin kuwa bana cikin yanayin da zan iya daga waya alokacin har ta katse ban dauka ba tana katsewa kuwa aka sake kira akaro nabiyu shima dai haka nabarta tagama kara harta katse amma sai akasake kira akaro na uku to daganan ne fa nadau wayar afusace dan naga wai waye wannan da yana ganin anki a amsa wayarsa amma yaki ya hakura dakira.
Ina dubawa sainaga bakuwar number cikin fushi kuwa nadauka na amsa ina amsawa ba,a bari nayi magana ba sainaji daga daya bangaren ance muna kira daga hukumar yan sanda na jahar yobe.
Akwai motar da ta tashi daga kano zuwa maiduguri asafiyar yau tayi hatsari akan hanyarta anan garin yobe mafi yawa na mutanen cikinta sun rasu wasu sunsamu munanan raunuka munsamu number ka ne acikin jadawalin number da ake karba daga gurin wanda zaihau mota saboda asamu wanda za,a kira koda wani abun yafaru akwai passenger maisuna Fatima zarah itace tabada number ka.
Kasa magana nayi inaji ata daya bangaren anata hello hello nasaki wayar tafadi kasa nayi saurin fitowa daga dakin ina isowa falo adaidai lokacin naji jiri yafara daukata naji duniyar tana jujjuyawa kawai saiji nayi kamar an bugamin katon karfe akaina nantake kuwa na sulale kasa sumamme.
Daganan bansan me yafaru ba sai farkawa nayi naganni a asibiti duk da cewa na farfado amma naga tsananin damuwa a idon mamata hakan ya tabbatar min da cewa sun samu labarin abinda yafaru da fatima zarah nayunkura zantashi sai mama ta dafe kirjina ta hanani tashi sannan tace likita yace kar abari katashi sai nanda yan awanni domin zaka iya kara faduwa domin bugun zuciyarka yakaru sosai hakan kuma zai iya jawo maka matsala azuciya katsaya ka kwantarda hankalinka domin mahaifinka yanzu haka suntafi suna hanya kuma insha Allah zasu sameta lafiya su dawo da ita.
Har aka sallamomu muka dawo gida amma dagani har mamata da kanwata Halima kowa cikin damuwa yake kawai jira muke muji daga gurin mahaifinmu munanan dai jugum jugum kamar masu zaman makoki sai wayar mamata kawai tafara ringing dukkaninmu muka zabura atare muka duba fuskar wayar aikuwa kiransane nantake naji zuciyata tayi wani irin bugawa da karfi tsoro yakama zuciyata nantake bakina yafara furta addu,oi Kala-Kala adaidai lokacinda mama tadauki awar takuma sakata a speaker ko sallama kasayi tayi gaba dayanmu mukayi shiru muna jiran muji me zai fada.
Gky naji dadin littafinnan kuma muna gdy sosae allah yaqara basirah