Adaidai lokacinda muka tattara dukkan nutsuwarmu muna jiran muji abinda mahaifin namu zai fada sai mukaji ya fara maganarsa kamar kaha "uhm mun sameta a raye amma akwai babbar matsala amma zuwa gobe idan yansanda sun gama nasu aikin zamu taho da ita saimusan yadda zamuyi."
Wannan kalma ta matsala da Abban mu ya ambata ya matukar tayar mana da hankali fiye da yadda muke a baya inata sake-saken wacce irin matsala ce wannan? Haka na kwana da abun araina, kashe gari da misalin karfe goma sha biyu na rana sai ga Abban mu ya shigo gida muna zaune. . .
Naji dadin wanna labari sosai Allah ya Kara basira