Skip to content
Part 12 of 18 in the Series Kaddarata Ce by Fatima Dan Borno

Kamar wani abu ya ce Suhaila ta shigo ɗakin, ta same shi hannunsa a wuya ga kumfa yana bin gefen bakinsa. Gabaɗaya ta ruɗe ta gigice, ta ƙarasa ta tallabo kansa, sai dai ta gaza riƙe shi saboda yadda ransa yake ƙoƙarin fita. A hankali tasa bakinta a kunnensa ta fara rera karatu cikin kuka. A lokacin matar ta samu ta fizge hannunta daga jikinsa, saboda irin ƙunan da take ji a dukkan jikinta. Gabaɗaya sai ya saki kamar mai barci. Sai da ta ga gumi yana bin gefen fuskarsa sannan ta sauka da sauri ta samo ruwa ta goge masa bakin, ta sake mayar da shi jikinta, wanda gabaɗaya zazzaɓi ya rufe shi.

 Da asuba ya buɗe idanunsa ya ganta tana zaune idanunta a rufe, shi kuma kansa yana cinyarta. Tausayinta ya kama shi a lokacin da ya gama dogon tunanin abubuwan da suka faru. A hankali ya sauke ƙafafunsa da nufin zuwa banɗaki. Cikin magagi ta jawo shi tana cewa,

“Wani abu yana damunka ne?”

Ya kafeta da idanu

“Babu abinda yake damuna ki tashi ki yi Sallah.”

 Firgigit ta buɗe idanunta tana dubansa. A lokaci guda idanunta suka kawo ruwa,

 “Yaya Farouk ya jikin?”

Sai da yasa ƙafafunsa a ƙasa ya yi hanyar banɗaki sannan ya waiwayo yana mata murmushi,

“Na warware sosai.”

Bai jira cewarta ba ya sa kai tare da addu’a. Tagumi ta yi tana tunanin me ya sa ta ganshi a cikin irin wannan halin? Ko dai shima ana ƙoƙarin kashe shi ne? Da sauri ta bar tunanin ta hanyar barin ɗakin gaba ɗaya.

*****

Acan Nigeria kuwa komai ya sake rincaɓewa, gabaɗaya Ummi ta raina kanta a hannun Sadiq. Sannu a hankali ya mayar da ita cikakkiyar mace a cikin ɗakin aurenta. Sai dai har gobe tunaninta yana kan Farouk, da ƙarfin tsiya sun yi alƙawarin sai sun aure shi.

Sadiq ya ɗaga waya ya kira Farouk ya gaya masa komai. Hankalin Farouk idan ya yi dubu to ya tashi, hakan yasa ya kwana cikin tunani kala-kala. Dole yana buƙatar neman shawarar mahaifinsa akan abinda zuciyarsa ke gaya masa.

Bayan ya kira Alhaji Marwan suka jima suna tattaunawa, har ya amince da ƙudirin ɗansa domin samun zaman lafiya a tsakanin Ummi da Sadiq, da kuma samar da kwanciyar hankali a cikin rayuwar Suhaila da ‘yan uwansa. Sun shirya da mahaifinsa zai dawo Nigeria zai mayar da Suhaila gidan Mama Karima zuwa ɗan wani lokaci.

 *****

Alhaji Marwan yana zaune a falo yana kallon labarai, Anti Laila da Jawaheer duk suna zaune sunyi tsuru-tsuru. Aka danna ƙararrawa, Jawaheer ta tashi ta buɗe ƙofar. Ihunta kawai aka ji hakan yasa duk suka miƙe suka nufi ƙofar. Farouk ne zaune a keken guragu, ana gunguro shi. Alhaji ya basu hanya suka shigo har falon suka ajiye shi. Anti tasa hannu akai tasa ihu ta damƙi wuyar rigar mutumin da ya shigo da shi tana zazzare idanu,

 “Uban waye ya yi wa ɗana haka? Me ya same shi? Ku gaya min me ya sami Farouk?”

  Alhaji ya dubeta fuskar nan babu fara’a, ya ce,

“Sake shi ko in saɓa maki. Ke kin isa ki hana Allah aiwatar da ikonsa akan ɗanki?”

  A tsorace ta sake shi tana ci gaba da zazzare idanu. Alhaji ya jagoranci aka kaishi ɗakinsa aka kwantar da shi sannan ya ce, “Ku fice ku barshi ya huta.”

Babu musu duk suka fice, sai dai har yanzu basu daina kukan ba. Sai a lokacin suka ji Alhaji yana waya yana maganar Farouk ya sami matsala ne a ƙashin bayansa, tashinsa sai wani ikon Allah.

Anti ta gigice ta ruɗe ta fita hayyacinta. Gani take yi shikenan ta rasa ɗanta mafi soyuwa a cikin ranta. A take ta kira Hajiya Asiya ta sanar mata. Babu jimawa sai gata da Ummi sun zo. Dukkaninsu babu wanda baya kuka. Alhaji yana zaune yana kallonsu, da ya ga za su dame shi ya tashi ya shige ɗakinsa ya rufo ƙofa.

Kwanaki biyu kenan ko muryar Farouk sun kasa ji, Anti ta fita hayyacinta duk ta susuce. Alhaji ya dubeta sama da ƙasa, ya ce,

“Tunda kin raba shi da matarsa sai ki yi masa aure ki kawo wacce zata kula da shi, domin yana buƙatar kulawa daga iyalinsa.”

Damuwar Anti ya ninku, dole babu shiri ta tafi gidan Hajiya Asiya suka kulle kansu suna tattaunawa.

“Hajiya yanzu ya za ayi Ummi ta fito daga gidan mijinta a samu ta auri Farouk ɗin? Zata fi bashi kulawa tunda dai ita ‘yar uwarsa ce.”

Hajiya Asiya ta zaro idanu ta dafe ƙirji, tana ganin tunda take bata taɓa ganin mace mai son Zuciya kamar Laila ba, ta yaya mutumin da aka ce ba zai warke ba sai wani ikon Allah ta ce kuma wai ‘yarta ta fito daga gidan miji ta aure shi? Ai wannan ba abu bane mai yiwuwa. Ummi bata da wurin rufin asiri da ya wuce gidan mijinta Sadiq. Duk da Farouk ɗin yana yaron yayanta, ba zata taɓa yarda da irin wannan muguntar ba.

A fili kuma sai ta yi yaƙe ta ce,

“Yanzu zuwa anjima zan kira Ummin sai mu ji hanyar da ya kamata mu biyo.”

Anti Laila ta saki ajiyar zuciya, domin da farko ta yi zaton Asiya juya mata baya zata yi dan matsala ta sami ɗanta. Haka suka rabu kowa da irin tunaninsa.

Tana isowa gida ta shiga ɗakin Farouk ta zauna tana kallonsa, tausayinsa ya tsirga mata duk da har yanzu yana nan da kyansa jikinsa bai lalace ba.

“Farouk ka kwantar da hankalinka kaji? Naje mun tattauna da Asiya insha Allahu Ummi ce zata zama matarka, har kuma ta yi jinyarka. Ai ranar naka sai naka. Idan ma Suhaila ce ina tabbatar maka guduwa za ta yi ta barka, tunda dama dukiyarka suke yi mawa.”

Gaban Farouk ya faɗi da ƙarfi, yana jinjina anya Sadiq ya ji maganarsu Momi da kyau kuwa? Ya gaya masa Momi da Ummi sun fi son dukiyarsa fiye da komai, yanzu kuma ga Anti tana bashi tabbacin za su iya zama da shi. Ko da yake mai son dukiyarka ko yaya kake in dai zai iya samu zai amince ya zauna.

Wata zuciyar tace ‘A’a babu macen da zata amince da zaman jinyar da babu ranar gamawarsa, in dai ba sonka take yi tsakani ga Allah ba.’ Wannan karon yana buƙatar ya gane shin waye mai sonsa tsakani ga Allah wacce zata iya zama da shi a ko wane irin hali?

Hajiya Asiya ta kama hanya sai gidan Sadiq, tana shigewa ya laɓe yana jin su.

“Kin ji Laila da son zuciya, yana da lafiya bata tayamu yaƙin samo shi ba, sai da yanzu ya zama mara amfani a duniya. To idan kika aure shi ta yaya har zai iya yi maki ciki bare har ki tsira da gado? Yayana ke da dukiyar nan amma kina ganin ya kwashi komai ya sa sunan Farouk, to shima Farouk ɗin gashi yadda ya zama. Gara ki zauna a gidan Sadiq kawai zai fi maki kwanciyar hankali, tunda shima ba laifi ba talaka bane, ko me kika gani?”

Ummi ta yi ajiyar zuciya ta ce,

“Momi in auri nakasasshe ince na auri wa? Gaskiya ni kyansa da ajinsa sun fi rinjayata akan sonsa, to yanzu duk babu su. Ni Gara inyi zamana inyi wa Sadiq biyayya kawai mu shirya kanmu, ba zan iya zaman jinyar ƙaton namiji kamar Ya Farouk ba. Tab! Ta ina ma zan fara? Yanzu sai ki ga duk na tsofe duk irin gyaran da zan yi kuwa.”

 Hajiya Asiya ta ce,

“Ashe kina da fahimta? Yanzu ta bayan gida zamu biyo mata kada ma ta fahimci mun gujeta ne.”

Ummi ta zumɓuro baki,

“Gara ki fito kai tsaye ki gaya mata, idan ba haka ba damunki za ta yi ta yi.”

Sadiq ya saki ajiyar zuciya, ya fice tare da kiran Farouk ya kwashe komai ya gaya masa. Farouk ya rintse idanunsa, ya jima bai ji maganar da ta tarwatsa dukkan tunaninsa ba kamar wannan. Sai da ya ji wani mugun jiri ya ɗibe shi, ya rintse idanunsa ya buɗe su jajir,

“Sadiq ‘yan uwana Kenan na jini sun gujeni saboda ance ina ɗauke da lalura. Yanzu kana ganin ita kanta Suhailar ba zata gujeni ba? Zata iya guduna itama muddin ta ji hakan. Wallahi zan gwada ‘yan mata da yawa, muddin duk suka gujeni, ina tabbatar maka zan ƙare rayuwata babu wata ‘ya mace a kusa da ni, zan cigaba da tsanarsu irin tsanar da baka taɓa jin labarinsa ba.”

 Sadiq ya furzar da huci Mai zafi ya ce,

“Bana jin ko da kowa zai gujeka Suhaila zata fara aikata hakan, ko da kuwa zata tsufa a wurin kula da lafiyarka. Kayi mata irin halaccin da duk duniya babu wanda zai iya yi mata.”

Haka suka gama tattaunawa cike da ɓacin rai suka kashe wayar. A ranar ya nuna masu ya fara magana. Anti Laila ta yi farin ciki, har ma ta kira Hajiya Asiya ta gaya mata. Ta ce ai tana nan zuwa.

Farouk da kansa ya kira Amrah da ta maƙale idan bashi ba sai dai ta mutu babu aure, ya gaya mata komai akan matsalarsa da kuma neman amincewarta ta aure shi, amma abin mamaki sai ta yi fuska ta fito masa da asalin muryarta ta gaya masa anyi mata miji su haƙura kawai. Anti Laila kuwa ƙaryarta ta soma ƙarewa, ko a dangi kowa yaƙi amincewa da wannan kasadar, Hajiya Asiya kuwa kai tsaye ta ce mata ta yi haƙuri Ummi ta ce yanzu tana son mijinta, hakan yasa suka yi kaca-kaca har Jawaheer ɗin, da ƙyar manya suka sasanta su, sai dai ba kamar da ba.

Alhaji ya tara su, ya ce lallai Suhaila zata dawo domin ta ci-gaba da duba lafiyar mijinta. Babu wani mai bakin yin musu kowa ya amince. Anti kuwa mamaki take yi a ina suka samo inda Suhaila take? Bata da damar tambaya dole ta ja bakinta ta yi shiru, tana jiran ganin ikon Allah. Don tasan babu yadda za ayi ‘yan uwanta ba su iya zama da shi ba sai wata Suhaila.

 Washegari duk suna zaune a falon suna karyawa Farouk yana zaune a Wheel Chair ɗinsa yana kurɓar tea a hankali. Ada can baya idan mace ta ce tana sonsa sai ta bashi tausayi, saboda yana girmama kalmar So, amma a yanzu duk macen da ta furta kalmar nan ya fi yi mata kallon mayaudariya wacce bata san menene so ba. Shi so gaba ɗayansa sadaukarwa ce.

Suhaila ta turo ƙofar gabanta yana tsananta faɗuwa, gaba ɗaya a tsorace take, zamanta a London ya fiye mata kwanciyar hankali, ko kuma a gidan Hajiya Karima, fiye da zama a cikin dodannin nan. Ko da yake tana da tabbacin Alhaji ba zai taɓa bari ta zauna a cikin gidan ba, duk da riƙe take da kayanta kamar yadda Alhaji ya bada umarni.

Idanunta fes akan Farouk, wanda kwana da kwanaki mafarkinsa kawai take yi. Sai dai ta kasa fahimtar dalilin ganinsa a Wheel Chair don haka ta ƙara so a ruɗe, gabaɗaya ta mance da idanun su Anti Laila. Ta dafa keken hawaye cike da idanunta,

 “Yaya Farouk me… Me ya same ka? Don Allah ka tashi babu kyau zama a irin abin marasa lafiya.”

Alhaji ya yi gyaran murya ta yi saurin waiwayowa ta dube shi ya nuna mata wurin zama. A ƙasa ta durƙushe ta zauna jikinta babu inda baya kyarma.

Alhaji ya zayyane mata lalurar Farouk ya tambayeta ko za ta iya zama da shi? Gabanta ya faɗi da ƙarfi. Ta lumshe idanunta domin baiwa hawayen idanunta daman zubowa.

“Alhaji zan ƙare rayuwata domin tattalin lafiyarsa, zan iya dauwama da shi a haka. In dai Yaya Farouk zai iya taimakona a cikin dubban jama’a da sharewa mahaifina hawayensa me zai hanani share hawayen nasa mahaifin?”

Ta fashe da matsananciyar kuka. Farouk ya kafeta da idanunsa yana jin wani sanyi yana tsirga masa. Zai so ya jawota ƙirjinsa ya lallasheta domin hawayenta suna ɗaga masa hankali.

Da ƙyar ta sassauta da kukan bayan sun kammala karyawa duk suka watse suka barsu a falon. Ya dubeta sosai sannan ya ce,

“Ki kaini ɗakina ina son kwanciya.”

Da sauri ta tashi ta dafa bayan keken tana tura shi har cikin ɗakinsa. Tana ƙoƙarin ɗaga shi ta sanya a gado ya yi murmushi yadda take faman nishi, ya ɗan taimaka mata sai dai gaba ɗaya suka zube akan gadon ta danne shi. Zubawa juna idanu suka yi cike da wani yanayi mai wahalar fassarawa. A lokaci guda ya lumshe idanun yana jin daɗin haɗuwar jikinsu wuri guda. Da ƙyar ta janye kanta, ta gyara masa kwanciyar tasa masa filo sannan ta jawo masa bargo. A gefensa ta zauna ta ɗauki Qur’aninsa tana karantawa cike da natsuwa. Tun yana saurarenta yana jin daɗi a ransa da natsuwa wacce rabon da yaji irinta tun suna London. Har barci ya kwashe shi. Ta miƙe a hankali ta shiga banɗakin ta fara gyara ko ina.

 Anti Laila ta dubi Jawaheer wacce a yanzu ita ce abokiyar shawararta ta ce,

“Abin da ya bani mamaki, a ina suka ganta? Kuma ai Farouk ya saketa, a mayar da auren ne?”

Jawaheer ta ce,

“Bata gama iddarta ba dole dai a cikin kwanakin nan zata gama tunda yanzu a wata uku kaɗan ne babu da rabuwarsu.”

Anti Laila ta yi shiru tana jinjina kai, idan lissafin da take yi daidai ne sun cinye wata uku tuni.

Kafin wani lokaci Suhaila ta tsaftace masa ko ina, ta turara ɗakin da turaren wuta. Kai tsaye banɗakin ta sake komawa ta wanke masa ƙananan kayansa ta shanya, sannan ta fice zuwa kitchen. Duk abunda take yi Anti Laila da Jawaheer suna maƙale suna kallonta cike da mamaki. Duk da irin wannan abubuwan da take yi hakan baisa tsanarta ta ragu daga cikin zuciyoyinsu ba. Da gaske suke yi sun tsaneta musamman da ta kasance talaka, uwa uba wacce mazajenta suke mutuwa.

A gurguje ta haɗa masa faten arish wanda ta wadata da busasshen kifi. Tuni gidan ya ɗume da ƙamshi. Na Alhaji ta fara ɗauka ta kai masa har falonsa, sannan ta dawo ta ɗauki na Farouk ta kai masa ta ajiye a gefe.

Zama ta yi a gefensa ta zuba masa idanu. Bata san ta inda aka fara ba, ta dai san zuciyarta ta kamu da wani abu mai tsananin wahala ayayin fassara shi. Hannunta ta tura cikin kansa, tana yi masa susa. Wani yarr!! Ya ji har cikin ƙafafunsa, da sauri ya kama hannun ya jawo shi har cikin rigarsa wanda hannunta ya shafi wani tattausan gashi, hakan yasa itama ta afka irin halin da ya rigata afkawa, cikin sauri ta janye hannunta. A lokaci guda ta janyo Ayatul Qursiyu ta tofa masa. Har zai tashi sai kuma idanunsa suka hasko masa keken guragunsa, lallai da ya tonawa kansa asiri. Duk da ya yi wasu abubuwan amma cikin ikon Allah bata fahimta ba. Ya yi ajiyar zuciya ya fara ƙoƙarin tashi, ta yi saurin dakatar da shi. Ɗago kansa ta yi, ta jinginar a jikin filo, sannan ta ɗauko abincin ta yi Bismillah ta kai masa bakinsa. Sai da ya lumshe idanu saboda daɗin girkin sannan ya buɗe idanun akanta. Ta sunkuyar da kai tare da goge masa bakinsa. A hankali ya yi maganar da ya sanyata zura masa idanu,

“Na gode. Allah ya yi maki albarka.”

<< Kaddarata Ce 11Kaddarata Ce 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×