Skip to content
Part 4 of 18 in the Series Kaddarata Ce by Fatima Dan Borno

Sai yamma likis, Jawahir ta kwashe su a mota, ta daidai saitin gidan Faruq ta rage gudu. Ummi ta dubi gidan ta ce,

“Jawahir wai har yanzu ba ki sato mana makullin Gidan bane?”

Jawahir ta mayar da kai akan tuƙin da take yi, a lokacin kuma ta wuce gidan tana murmushi,

“Kinsan Allah? Ko Anti ba ta san inda Ya Faruq ya ɓoye key ɗin gidan nan ba. Ki bari kawai har sai mun kawo ki. Wayyo za ayi biki irin wanda ba a taɓa yi ba a garin nan.”

Duk suka kwashe da dariya. Ita dai Suhaila sai ta sunkuyar da kanta a lokacin da take jin zazzaɓi yana neman rufeta.

***

Yau gidan ya cika da girke-girke saboda dawowar rai ɗaya, wato Faruq. Suhaila aka bari a kitchen ɗin, don haka ita ta haɗa dukkan nau’ikan abinci, ta koma ɓarayin zoɓo. Su Ummi sun tafi gyaran jiki, don haka daga ita sai masu aiki sai kuma Anti suke ta shirye-shirye.

  A lokacin da ta kammala komai ta faɗa banɗakin Jawahir ta yi wanka, sannan ta fito ta ɗan kwanta. Ummi ta ɗaka mata duka,

“Ki tashi mu je filin jirgi taro Ya Faruq.”

  Suhaila ta sake komawa ta kwanta.

  “Sai kun dawo na gaji da yawa.”

  Babu musu duk suka fice, gidan ya rage babu kowa sai ma’aikata.

 A hankali barci ya kwasheta, ba za ta iya sanin adadin lokacin da ta kwashe tana barcin ba.

A hankali yake takowa fuskarsa cike da annuri. Yana da sassanyar kyau, irin kyan da ke ruɗin mata da yawa izuwa gare shi. Ummi ta kafe shi da idanunta tana jin kamar ta je ta rungume shi saboda so. A gefen damansa wata mace ce suke takowa tare, ita kanta ba baya ba. Duk cikinsu Jawahir ce ta kasa haƙuri ta ƙaraso har kusa da shi. Ta so ƙwarai ta rungume shi, sai dai irin kallon da ya watsa mata yasa ta ja burki tare da kama hannayensa. Wacce ke gefensa ta ƙaraso har gaban Anti ta durƙusa ta gaida ta cike da kunya. Hakan yasa annurin fuskar Ummi ya ɓace ɓat! Farouk yana kula da yanayinta, hakan yasa ya dubi Anti ya ce,

“Wannan wata abokiyar karatuna ce, da daɗewa bamu haɗu ba sannan karon. Sunanta Amrah.” Ya dubi Amrah ya ce,

“Amrah ga mahaifiyata, ga ƙanwata, wancan kuma ita ce matar da zan aura insha Allahu.”

Haba sai rawar kai ya motsa. Ummi aka ƙaraso cike da iyayi. Amran ta dubi Ummin, ta ɗan yi yaƙe. Anan wurin suka raba hanya. Farouk ya fara hango Sadiq babban abokinsa, da baya haɗa shi da kowa. Rungume juna suka yi kowanne yana nuna jin daɗin ɗan uwansa. A motar Sadiq suka kama hanya, wanda har suka taho babu wanda ya yi maganar da ya fice uku zuwa huɗu.

Suhaila tana barci ƙarfin hayaniyarsu yasa ta buɗe idanunta. Ummi ce ke zaune kusa da ita,

 “Ke yau dai anyi babu ke, mun taro babban Yaya har sun gama cin abinci shi da abokinsa. Yanzu ki yi sauri ki tashi ki je ki gaishe shi yana falon Anti suna ganawa.

  Suhaila ta ɗauki niƙaf ɗinta, Ummi ta ƙwace tana harararta.

“Idan kika je wa Anti da wannan abun ai sai kin sha faɗa.”

  A natse take takowa zuwa falon Anti kanta a ƙasa, a lokacin da shi kuma yasa kai ya shige wani ɗan ƙaramin ɗaki ya murza key.

  Suhaila ta ƙaraso, a lokacin ta haɗa idanu da matashin da ke zaune kamar magana suke yi da Anti. Ummi ta ƙaraso cike da fara’a ta ce,

 “Yaya Sadiq ga sisterna Suhaila. Anti ina Ya Farouq ɗin bai gaisa da Sis ba?”

  Anti ta yi magana cikin ƙasaita,

“Kinfi kowa sanin halin Yayanku, yanzu haka ya shiga ɗakin Karatunsa idan kika kasa kunne za ki ji Qira’a na tashi. Ba zai fito ba, sai ya ji kiran Sallah. Ya ce dai abinci ya yi masa daɗi, zoɓon ma bai taɓa shan irinsa ba. Sannu da ƙoƙari Suhaila.”

 Suhaila ta sunkuyar da kanta tana murmushi. Sadiq ya kafeta da idanu Yana Jin wani abu yana huda jikinsa.

“Suhaila kinyi ƙoƙari gaskiya. Dole zamu baki tukuici ni da abokina.”

  Anti ta dubi Sadiq ta ce,

“Yauwa Sadiq ka ajiye su Ummi a gida, saboda kaya da za ta kaiwa Mominta.”

  Sadiq ya amsa tare da miƙewa yana yi wa Anti Sallama. Suna fitowa Suhaila ta ɗaura niƙabinta ta fito. Ya dubeta, yana jin shigar nan ma ta burgeshi.

 Sai da ya shiga har wurin Momi suka gaisa sannan ya wuce.

  Bayan Farouq ya kammala karatun Alqur’aninsa, kai tsaye ya wuce banɗaki ya sake watsa ruwa ya tsane jikinsa da tawul. Bayan ya dawo Masallaci ya sami iyayensa a falon mahaifinsa suna zaune gabansu farfesun bindin sa, suke sha cike da farin ciki.

  Farouq ya ƙaraso har gaban mahaifinsa, ya gaida shi, sannan ya gaida Anti. Alhaji ya dube Shi ya ce,

“Sadauki ya kamata ko anjima ne da daddare ka shirya ka je gidan Mominku ka gaidata.”

  Sai da ya gutsiri Apple ɗin sannan ya ce,

  “Ina da ninyar hakan Alhaji. Ɗazu Sadiq ya kirani a waya, ya matsa min wai ya ga wata yarinya anan gidan na kasa gane wacce yake nufi.”

 Alhaji ya yi dariya ya ce,

“Suhaila ce ‘yar wajen Alhaji Sambo.”

Anti ta yamutsa fuska,

 “Shi kuma me zai yi da ‘yar talakawa likis? A zatona ma yadda yake da Jawahir ita zai ce abashi?”

Alhaji ya ɗaure fuska kamar bai taɓa dariya ba,

“Kin ga bana son shirme da shiririta. Sai ki nuna min bolan talakawan akai su. Ke kin mance yadda muke da?”

  Anti Laila ta yamutsa fuska kawai ta haɗa rai. Ba banza ba ta ji yarinyar ta ƙi shiga zuciyarta.

  Suhaila suna zaune a falon suna kallo, aka ƙwanƙwasa ƙofa, kasancewar ta fi kusa da ƙofar, ta miƙe. Jikinta doguwar riga ce mai bin jiki, kanta babu ɗankwali. Bata tsammaci ganin baƙo a irin lokacin ba, don haka ta miƙe ta ƙarasa bakin ƙofar.

  Daga shi har ita gabansu ya yi wani irin faɗiwa, da ƙarfi. Idanunta ta zuba mashi, tana godiya ga Allah da ya ƙagi wannan halittar. Sun kafe juna da idanu, na wasu ‘yan daƙiƙu yana sanye da ƙananan kaya, ya ɗora baƙar rigar sanyi wanda jikinta duk gashi ne kamar gashin mage. Fuskarsa babu fara’a. A lokaci guda jikinta ya kama kyarma, ya ɗora hannunsa abisa handle ɗin da take riƙe da shi, kamar ta yi masa katanga da shigowa falon. Taushin hannunsa ya taimaka wajen saukar mata da kasala, har sai da ta lumshe idanunta ta sake waresu akansa. Shi ya fara janye hannun, a lokacin da ta ji muryar Momi tana cewa,

“Kin duba kin ga waye?”

 Ta yi firgigit ta ja da baya tana sunkuyar da kai. Cikin siririyar muryarta ta ce,

“Bansan waye ba.”

 Faisal yana ƙoƙarin ta shi ya duba, Farouk ya ratsata ya wuce. Momi ta faɗaɗa fara’arta tana cewa,

 “Ɗazu duk irin girkin da kuka zo kuna koɗa min kunyi masa, ashe baki ma ganshi ba? Farouk baƙon turai.”

 Ummi tana jin sunan Farouk ta fito cike da farin ciki. Suhaila ta ɗan durƙusa ta gaida shi, tunda ya amsa sau ɗaya ya kauda kansa zuwa kallon tv. Bai sake waiwayowa inda take ba.

  Ta kama hanya jiki asanyaye zata shige ciki, Momi ta ce,

“Kawo masa tuwon da kika yi mana nasan ma’abocin son tuwo ne.”

  Suhaila ta nufi kitchen a lokacin Ummi ta biyo bayanta.

“Sis ya kika ga mijina?”

Kafeta da idanu ta yi, kafin ta ce,

“Yana da kyau. Allah yasa muna raye ya kaimu lokacin.”

 Ummi ta rungumeta tsam tana cewa,

“Sis ina sonsa, akan son Ya Farouq zan iya mutuwa.”

 Sai hawaye sharr! Jikin Suhaila ya ƙarasa mutuwa, ta ɗagota tana murmushi,

“Ba zaki mutu ba, za ki zama matarsa insha Allahu.”

 Ta sa hannu ta goge mata hawayen. A diririce ta kai masa abincin da komai ta haye sama. Rigingine ta yi, tana sake hasko hotonsa. A hankali ta fara jin sanyi da wani irin zazzaɓi suka taru suka rufeta. Dole ta jawo bargon bakinta yana kyarma, kafin wani lokaci idanunta sun ƙafe, bata ji bata gani.

  Ummi ta shigo ɗakin ta bubbugeta, shiru babu alamun motsi. Tana duba fuskarta ta fasa ƙara ta yi ƙasa da gudu,

“Momi, ki taimakeni  Suhaila ta mutu.”

 Tunda yake a duniya bai taɓa jin kalmar da ta buge shi kamar irin wannan ba. Kusan ya riga Momi tashi ya nufi sama ba tare da yasan ina ne ɗakin da take ba. Ɗakin da ya gani a buɗe ya sanya kansa, a lokaci guda ya hau kan gadon, ya jawota gaba ɗaya jikinsa yana taɓa wuyanta.

A lokacin Ummi da Momi suka shigo. Ya dubi Momi da duk ta ruɗe, ita kuma Ummi kawai kuka take yi.

“Kawo ruwa, sumewa ta yi. Ina ganin wani abu ne ya firgitata. Me ya sa za ku dinga zama babu Qira’a?”

 Ya faɗa yana mai jin tarin damuwa a zuciyarsa. Da kansa ya shafa mata ruwan a fuska. Dogon ajiyar ta sauke a lokacin kuma ta ɗan buɗe idanunta. Kafe juna suka yi da ido, ya ɗan kauda idanunsa ya ce,

“Momi mu je kawai babu komai. Ke kuma jeki kitchen ki kawo min ruwa intofa mata wasu addu’o’i.”

  Momi ta fice daga ɗakin, Ummi ta wuce kitchen. Ɗakin ya rage da ga shi sai ita.

 “Gaya min abin da ya razanaki.”

 Idanun ta sake warewa ta ɗan girgiza kai,

“Nima bansani ba.”

 Ta yi maganar cikin shagwaɓa kamar za ta yi kuka.

“No kada ki yi min kuka Please. Ku daina sakaci da ibada.”

 Duk suka sake yin shiru. Sai yanzu ta fahimci a jikinsa take, ta yi yunƙunri raba jikinta da nasa, ya dubeta. Shi kansa bai san har yanzu tana jikinsa ba. Yasa hannu ya goge mata hawayen da ke zuba ta gefen idanunta. A lokacin Ummi ta dawo da ruwa a kofi ya tofa mata ya bata ta shanye, sannan ya miƙe kawai ya fice. Shi kansa ciwon kan yake fama da shi, dole ya yi wa Momi Sallama ya wuce gida.

Gaba ɗaya Ummi ta kasa motsawa ko nan da can, tana kulawa da Suhaila. A lokacin Daddy ya shigo yana tambayarta jikinta. Ta miƙe da fara’a a fuskarta ta ce,

“Daddy na sami sauƙi.”

Tun daga wannan ranar Suhaila bata sake sanya Farouk a idanunta ba. Shi tuni ya mance da rayuwarta ya kama wata sabgar. A lokacin Daddy ya shirya masu zuwa Ikara su yi kwana biyu.

Sun iso cikin farin ciki, aka tarbe su, Suhaila ta dinga jin komai yana dawo mata rayuwarta, mutuwar Adnan da Suraj yasa ta ji ƙwalla sun zubo mata. Inna ta dubeta da fara’a ta ce,

“Kin ga yadda kika yi kyau kuwa? Ko dai ‘yar Hafsisina za ta bi ku ne? Ƙila daga nan ta sami mijin aure.”

  Abba ya dubeta ya ɓata rai,

“Babu inda za ta je.”

 Inna ta haɗe rai kamar bata taɓa dariya ba. Da za su fita Suhaila ta sanya niƙaf ɗinta. Ummi ta dubeta ta ce,

“Sis me ya sa kike son niƙaf ne?”

  Ta yi murmushi ta ce,

“Ba za ki gane ba.”

Kwanaki biyu suka yi sannan suka koma. A lokacin ne suke samun labarin Sadiq ya zo ya dage sai Daddy ya bashi izini agun Suhaila. Ya so Farouk ya shige masa gaba, amma sai ya nuna shi bai da lokacin irin wannan shirmen. Daddy cike da zullumi ya ce ya dakata tukuna su fara karatu kada a raba masu hankali.

  Ita kanta Ummi ganin Farouk ya yi mata wahala, bare kuma Jawahir da ta rantse masu rabon da ta ganshi har ta mance.

 Hakan ya sa Ummi a cikin damuwa. Yau Suhaila tana barci take jin shessheƙar kuka, mamaki yasa ta buɗe idanu tana duban Ummi.

“Baki da lafiya ne?”

 Ta fara goge hawayenta ta ce,

“Sis Yaya Farouk baya sona, bai damu da ni ba, ina shan wahalar rashinsa amma ya kasa gane hakan.”

 Ta sake rushewa da kuka. Suhaila ta yi shiru tana jin wani abu yana yawo a cikin ƙwaƙwalwarta.

“Ummi da kukan nan da kike yi, da tashi kika yi kika sanar da mahaliccinki da hakan ya fi.”

Ummi ta goge hawayenta ta sake rungume wayarta, wacce hotonsa ne akan fuskar wayar, tun ranar da yana cin abinci ta ci sa’a ta ɗauke shi bai sani ba. Haka suka kwana Suhaila ta gaza gane abin da ke mata daɗi.

  ****

Cikin ikon Allah sun rubuta Jamb sun sami irin makin da suke buƙata, kai tsaye suka sami Admission a NOUN, Makarantar da Farouk yake koyarwa. Da biyu Ummi take son Makarantar, gashi fannin English suka ɗauka, saboda tasan anan yake.

  Tunda suka fara Makarantar ba su taɓa haɗuwa da su ba, har sai da suka shiga mataki na biyu. Dukka ajin babu wanda yasan akwai wani karatu da zai ɗauke su, kawai rayuwarsu suke yi cikin farin ciki a cikin ajin. Suhaila kuwa tana magana da wani wanda jininsu ya haɗu matuƙa a cikin ajin.

 Jin shiru yasa duk suka ɗago, a lokacin ta haɗa idanu da shi ya kafe su da ido, fuskar nan kamar anyi gobara. Ummi tana ta zungurinta amma bata ji ba. Ya jima anan bai iya cewa komai ba. Da ƙyar ya buɗe baki cikin turancinsa ya fara magana,

“Sai kun dage, bani da wasa. Ina da ƙa’idoji duk lokacin da wani ya ƙetare ɗaya zan kore shi a cikin Class ɗina. Idan kuka zama masu hankali zamu iya shiryawa.”

  Babu wanda bai shiga taitayinsa ba, kasancewar sun sami labarinsa tun kafin ma su san zai ɗauke su a wannan zangon.

Haka ya gama karatunsa cikin ɗaure fuska ya fice. A ranar cikin zazzaɓi Suhaila ta kwana, ta bar Ummi tana ta kwarmato ɗinta.

Yau ma kamar kullum Suhaila tana zaune da Sulaiman suna tattaunawa akan karatu, a lokacin ta ji muryar Sulaiman yana cewa,

“Wallahi Suhaila na jima cikin sonki, don Allah ki taimakeni ki aureni.”

 Tuni jikinta ya fara karkarwa, ta ɗago ta zuba masa idanun da suka sake rikita shi.

  “Sulaiman kada kayi gangancin afkawa cikin matsala. Ka gaggauta ƙaryata kanka don Allah. Ka bari mu gama karatun nan lafiya.”

  Ya girgiza kai,

“Da gaske nake yi maki. Nima bansan lokacin da na yi nisa a cikin sonki ba, kuma da gaske nake yi. Zan turo iyayena su nema min izinin zuwa gurinki.”

Suhaila ta miƙe tana ja da baya, bata san lokacin da ta kwasa da gudun gaske ba. Gaba ɗaya ta kiɗime, don haka ta dinga bin ta cikin lungunan azuzuwa tana ƙarawa da gudu. Wasu mutanen sukan juyo su dubeta, su ci-gaba da hulɗarsu.

A jikin wani ta faɗa, hakan yasa ta ƙara ƙanƙame shi tana magana cikin rawar baki.

“Ka taimakeni, ya ce yana sona, Wa..Wallahi mutuwa zai yi. Ka taimakeni bana son inrasa Sulaiman, yana da ƙoƙari shi kaɗai ya rage wa iyayensa, zai iya mutuwa daga nan zuwa ko wane irin lokaci.”

Farouk da ya yi ninyar kwasa mata mari, ya ja ya tsaya, yana sauraren bayanin siririyar muryarta cikin ruɗu da rawan baki. Kalamanta sun bashi mamaki, sun sa yana buƙatar ganin fuskarta, shin mutum ce ko aljan?

<< Kaddarata Ce 3Kaddarata Ce 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×