Sai yamma likis, Jawahir ta kwashe su a mota, ta daidai saitin gidan Faruq ta rage gudu. Ummi ta dubi gidan ta ce,
"Jawahir wai har yanzu ba ki sato mana makullin Gidan bane?"
Jawahir ta mayar da kai akan tuƙin da take yi, a lokacin kuma ta wuce gidan tana murmushi,
"Kinsan Allah? Ko Anti ba ta san inda Ya Faruq ya ɓoye key ɗin gidan nan ba. Ki bari kawai har sai mun kawo ki. Wayyo za ayi biki irin wanda ba a taɓa yi ba a garin nan."
Duk suka kwashe da dariya. Ita dai. . .