Skip to content
Part 5 of 10 in the Series Kaddarata Ce by Fatima Dan Borno

A hankali ya ɗago fuskarta, har yanzu idanunta a rintse suke, duk da hakan sai da hawaye suka dinga sintiri a fuskarta.

Sosai ya kafeta da ido, yana jin wata kasala tana sake rufe shi. Fitowarsa Office kenan ya ci karo da ita. Ya rasa yadda zai yi ta rabu da jikinsa.

“Suhaila.”

Ya kira sunanta da wata murya, wacce yasa ta buɗe idanunta. Bata da ƙarfin janye jikinta daga nasa, sai sake rintse idanun ta yi da ƙarfi tana Salati.

Hannayensa yasa ya ɗauke hawayen ya sake ta kawai ya wuce da sauri. Sabuwar kuka ta sake sawa tana jin damuwa na sake lulluɓeta. Bata jira ta kammala ɗaukar lectures ɗinta ba ta fice daga Makarantar gaba ɗaya.

  Momi da Daddy suna falo suka ganta ta shigo a firgice. Daddy ya fara tashi cikin damuwa yana dubanta,

“Lafiyarki ƙalau kuwa?”

 Ta yi dabarar ɗauke ƙwallar ta haɗiye wani abu da ya taso mata ta ce,

“Daddy kaina ne kamar ya tsage, shi ne na biya na siya magani nasha, na dawo gida inɗan kwanta.”

Daddy ya girgiza kansa cikin damuwa,

“Sannu maza ki je ki kwanta. Allah ya ƙara sauƙi.”

 Da sauri ta haura sama, ta faɗa gado tare da rushewa da sabon kuka. Bata son rabuwa da Sulaiman amma tana ji a jikinta lokacinsa ya yi.

  Ummi ta shigo gidan a hargitse, a lokacin Farouk yana zaune suna tattaunawa da Daddy, bata kula da Farouk ba ta faɗa jikin Daddy ta fasa kuka.

“Daddy ban ga Suhaila ba, na duba ko ina banganta ba.”

 Daddyn ya yi murmushi, shi kuwa Farouk sai ya mayar da kansa kan tv, a gefe guda yana jin gabansa yana faɗi wanda ba zai iya cewa ga takamaiman dalili ba, ƙila kuma ba zai rasa alaƙa da maganar Ummi, na rashin ganin Suhaila ba.

Daddy ya shafi kanta ya ce,

“Daina kukan, ta dawo bata jin daɗi, shiyasa bata tsaya jiran Driver ba. Ni kuma bansan bata gaya maki ba.”

Ummi ta saki ajiyar zuciya ta ce,

“Daddy ina sonta, kamar yadda nake son Ya Farouk.”

 Farouk ya ɗago da sauri kaman zai kalleta, sai kuma ya ƙara mayar da kansa ga tv. Daddy ya yi dariya ya ce,

“Dubi nan.”

 A hanzarce ta ɗago, tana ganin Farouk ta ruga da gudun gaske ta haura sama. Daddy shi kaɗai ke murmushinsa, shi kuwa Farouk ya nausa wata duniyar mai cike da tunani kala-kala, akwai amsoshin wasu tambayoyi da yake da buƙata, sai dai yana jin ya fi ƙarfin ya tsaya bin diddigi. Daddy bai yi mamakin yadda Farouk ya sauya zancen da ci-gaba da maganar da ta kawo shi ba, kasancewar yasan halinsa tun yana ƙarami.

 Ummi tana faɗawa ɗaki ta sami Suhaila ta fito daga wanka ɗaure da tawul, idanun nan sun yi ja saboda kuka. Ummi ta ɗauki filo tana bugunta alamun ta ɓata mata rai, Suhaila ta riƙe filon, sai kawai ta fashe da kuka ta rungume Ummi.

 Tuni Ummi ta ɗagota, a lokaci guda ta jawota bakin gado suka zauna,

“Sis me ya saki kuka? Gaya min.”

  Suhaila ta kasa gaya mata, sai kanta da take nuna mata alamun yana mata ciwo. Dole ta kawo mata magani tasha sannan ta kwanta.

  Washegari ta tashi babu ciwon kai, suna ta sauri kasancewar yau Farouk zai yi masu test, duk da shi babu abin da ya dame shi idan ya gadama yana gama karantar da su zai ce a ciro takarda test. Ko alama ba sa wasa da duk abin da ya shafe shi.

  Suhaila tana ta leƙe ko za ta ga Sulaiman shiru. Hakan yasa ta fara rubuta test ɗin hankalinta a tashe. Ita kanta tasan babu wani abin arziƙi da ta rubuta kawai ta yi shiru tana kallon takardar idanunta cike da hawaye.

 Wani abokin Sulaiman ya shigo idanunsa jazir saboda kuka, ya dubi Farouk ya ce,

“Sir! Na zo ne insanar Allah ya yi wa Sulaiman rasuwa.”

 Kasancewar shi ne President ɗin ajin, yasa wannan labari ya shiga kunnuwan kowa da ke zaune, wanda ya jawo tashin hankula. Sai dai kuma Farouk gani yake babu wanda ya kai shi tashin hankali. Ya fi kowa sanin kusancin Sulaiman da Suhaila, jiya ya kasa barci saboda kalaman Suhaila, yanzu kuma anzo angaya masa Sulaiman ya rasu? A take ya riƙe kansa yana tariyo maganganun Suhaila.

  Suhaila ta miƙe jikinta yana rawa,

“Salisu, waye ya gaya maka ya rasu? Jiya muna tare da shi don Allah ka gaya min gaskiya.”

 Wanda aka kira da Salisu ya sake sa kuka yana magana cikin shessheƙa,

“Lafiya lau aka kwanta da shi yau aka tashi sai dai gawa.”

  Suhaila ta dinga ja da baya tana girgiza kai. Hatta Ummi kuka take yi tsakaninta da Allah. Farouk yana nan tsaye ya rasa ta inda zai fara. Idanunsa suna kafe a fuskar Suhaila, itama shi ta kalla tana girgiza kai. A lokacin ne kuma ya kula kamar bata cikin hayyacinta. Ko kafin ya ƙaraso kanta ta yanki jiki ta faɗi a sume.

Shi kansa ya rasa abin da ke masa daɗi, gaba ɗaya ajin anmrikice da koke-koke. Yana nan sunkuye akan Suhaila ya rasa yadda zai yi. Ummi ya duba yadda take kuka ya yi magana cikin dakewa,

“Samo ruwa a yayyafa mata.”

 Kai tsaye ta amso ruwa ta kawo masa. Doguwar ajiyar zuciya ce ta ƙwace mata, ta tashi jikinta yana rawa tana faɗin,

“Ina Sulaiman ɗin?”

 Ya yi mata magana cikin faɗa,

“Ki dawo hayyacinki.”

Sai a lokacin ta lura da shi. Sunkuyar da kanta ta yi tana sake zubda hawaye. A hankali ya miƙe.

“Ku zo mu je gidan rasuwar. Waɗanda suke da abin hawa suka san gidan su shiga gaba.

 Ummi da Suhaila suka shiga motar Farouk a lokacin suka kama hanya sai gidan su Sulaiman.

 Tana ganin mutane ta duƙar da kai, tana jin wani irin jiri. A hankali ya yi mata magana kamar mai raɗa,

“Ki kula da kanki.”

Ta gyaɗa kai kawai. Suna fitowa ana fito da gawar Sulaiman. Suhaila ta kafe makaran da idanu tana tuna wasu abubuwa masu tarin yawa. Saukar hannun Farouk ta ji a bisa hannunta, ta kai wa fuskarsa kallo da har yanzu babu sauƙi, ya ɗaga mata gira, hakan yasa ta sunkuyar da kanta ta zare hannunta ta bi ayarin matan Class ɗin. Farouk ya yi ajiyar zuciya, ya koma cikin jama’a jikinsa babu ƙarfi, ya wuce inda za ayi Sallar, kasancewar baya rabo da alwala a jikinsa. Fitowarsa Office kenan ya yi alwala ya wuce cikin ajin.

  Bayan ankaishi ne ya ware kansa yana tunani mai zurfi. Dole kansa ya fara ciwo saboda zurfin tunanin da ya faɗa. Yana buƙatar yin dogon bincike akan Suhaila, amma kafin nan yau zai yi Istakhara da kansa, yana son sanin wani abu mai mahimmanci a game da matsalar Suhaila.

  Saboda irin kukan da Suhaila tasha, tuni idanunta suka kumbura suntum! Bai dubeta ba, ya kwashe su ya mayar da su Makaranta. Tunda ta dawo Makarantar ta ƙi yarda ta shiga cikin ajin, tana nan zaune ƙarƙashin bishiyar da suka zauna jiya da Sulaiman. Tunani ne fal a cikinta, ‘Sadiq ya riga Sulaiman furta yana sonta, me ya sa bai mutu ba?’

Zuciyarta ta ankarar da ita wannan bayanin. Sai dai bambancin ɗaya ne, Sadiq ba ita ya samu ba, saɓanin Sulaiman da kai tsaye ya sameta. Ji ta yi andafa kafaɗarta. Ta waiwayo a hankali suka haɗa idanu da Ummi, da itama tasha kukan.

“Sis ki daina kukan hakannan.”

 Suhaila ta ce,

“Ummi ki tashi mu tafi gida.”

Babu musu Ummi ta miƙe, tana sake danna lambar Driver.

“Kinga tun ɗazu nake neman lambar Driver bata shiga. Ya zamu yi?”

 Suhaila ta kamo hannun Ummi suka fara tafiya,

“Mu fita waje mu nemi abin hawa.”

Babu musu suka ci gaba da tafiya, kowacce da irin damuwarta.

Sun kusa Gate kenan, suka ji ƙarar mota a bayansu, hakan yasa suka matsa ba tare da sun waiwayo ba.

“Ku shigo mu tafi.”

Suka ji saukar muryarsa. Dukkansu suka ɗago suna dubansa. Mamaki ya kama Suhaila lokacin da ya sauya kaya. Ta buɗe ta shiga baya Ummi ta shiga gaba.

 Duk ɗago idanun da Suhaila za ta yi sai ta haɗa ido da Farouk, sai dai irin kallon da yake mata, kallo ne na tuhuma. Ita kanta ta yi tunanin zuwan wannan ranar. Dole ta sunkuyar da kanta. Ya ɗan dubi Ummi ya ce,

“Sulaiman ɗinnan dama bai da lafiya ne?”

“Lafiyarsa ƙalau Yaya. Jiya ma na gansu da Sis Suna hirarsu.”

  Ya sauke sassanyar ajiyar zuciya, ya ɗan kwantar da kansa gefe guda gaba ɗaya lissafi ya ƙwace masa.

  Yana ajiye su, ya figi motarsa da ƙarfi, yana ganin kamar gidansu ya yi masa nisa.

 Suhaila tana shiga ciki ta faɗa banɗaki ta rufe, ta sake rushewa da kuka.

“Yaushe zan daina kuka? Yaushe mazaje za su fara mutuwa a dalilina? Me ke faruwa da ni ne ni Suhaila?”

 Ta sake fasa kuka, ta zame kawai ta kwanta a ƙasa, ba tare da la’akari da inda take ba, tana jin kanta kamar zai rabe biyu.

****

Ƙarfe ukun dare ya buga, a mafi kyawun ɗakin. Kaf cikin ɗakunan babu ɗaki mafi shahara da kyau kamar ɗakin Farouk. Zaune yake bisa tattausar dardumarsa, yana ƙara jaddada yabo da godiya, ga Allah da Manzonsa. Ya kasance duk abin da yake nema a duniya Allah ya bashi. Duk da ɗan adam har ya mutu baya taɓa daina dogon buri. A yanzu burinsa guda ne, Allah yasa kada ya ba iyayensa kunya ya amshi Ummi a matsayin matarsa. Yana da irin kalar matar da yake da buƙatan aure. Ummi ta cika haske, haka abin da ya kula haskenta sirki ne da man ƙara haske. Duk da a yanzu anɓata komai na zamani, hatta Shower Gel sai ka ci karo da mai sanya haske. Amma na Ummi ya yi yawa. Sannan Ummi bata iya girki ba, yana son mace mai iya girki. Ummi kuma ‘yar shagwaɓa ce, bata da bambanci da ƙanwarsa Jawaheer. Farouk yana ganin yadda yake fari, bai kamata ya auri farar mace ba, ya fi son baƙa mai sirkin fari, wato Choculet Colour.

  Banɗakin ya koma ya sake yin Alwala, kasancewar tun sha biyun dare yake zaune bisa Sallayarsa.

  Ya yi Sallah raka’a biyu, bayan ya sallame, ya karanto wasu addu’o’in sannan ya ɗora da addu’ar Istakhara, yana ambaton sunan Suhaila, wanda shi kansa bai san dalilin irin wannan bin diddigin da yake yi akanta ba. Ko ba komai abin da ya ji ta furta masa, da kuma faruwar lamarin ya zama dole yasa ko waye a cikin shakku. Ta hannun dama ya kwanta cikin kyakkyawar shiga, tare da tsarkake zuciyarsa, ya cire duk wani tunani, ya ci-gaba da addu’a a cikin zuciyarsa har barci mai daɗi, ya ɗebe shi ya jefa shi a wata duniya.

_Ka damu da sanin matsalar Suhaila ko? Tabbas tana cikin matsaloli da yawa. Amma mahaifinta shi ne silar komai. Idan kana son zuciyarka ta rage wannan tunanin da damuwar, da shiga waswasi. Ka amince a tsaida aurenka da Ummi. Ina tabbatar maka ranar bikinka da Ummi komai zai zama ƙarshe. Wannan ɓacin ran da kake yawan kwana a ciki zai yaye. Duhu zai bar rayuwarka haske zai mamayeka da dukkan zuri’arka._

_Kada kayi tunanin don ka kasance cikin tsarki baka yi wa Allah kuskure, ku ‘yan adam kullum sai kun aikata kuskure, sai dai ka gode Allah kana da yawan neman tuba. Za ka shiga cikin jarabawa a sanadiyyar aurenka, za ka yi tunanin kamar duk duniya baka da masoyi, daga baya haske zai mamaye dukkan ganinka, zaka kasance cikin wani irin matsayi mai girma, domin kuwa zaka yi taimakon da babu mahaluƙin da zai iya aikata shi sai kai, za ka amince ka sa ƙafafunka a cikin wuta bayan kana kallo da idanunka wutan ne, hasalima kafi kowa sanin tsananin zafin wannan wutan. Tashi ka tafi rayuwarka tana cike da nasara._

Farouk ya yi ƙoƙarin tsaida tsohon amma yaƙi waige. Binsa kawai yake da gudu yana cewa,

_’Baba ka taimakeni ka tsaya. Binciken da nake yi akan Suhaila ne ba akan aurena da Ummi ba. Na sani duk duniya babu abin da zai iya hana aurena da Ummi sai idan ɗayanmu ne ya mutu. Amma rayuwar Suhaila nake son sani, me mahaifinta ya aikata da ake hora ‘yarsa da shi? Ka gaya min addu’ar da zanyi mata don Allah Baba._’

Tsohon ya waiwayo ya dube shi, ya jefe shi da murmushi, sannan ya ɓace ɓat!

  A lokacin ya farka daga irin barcin da ya kwashe shi. Gaba ɗaya ya jiƙe sharkaf! Yasha yin Istakhara, bai taɓa ganin abu ba, sai dai Allah yakan aiko masa da wani sanadi da zai san abun, ko kuma ya cire masa son abin idan babu alkhairi a ciki. Amma me ya sa na yau ya sauya?

  Ya riƙe kansa da ƙarfi. Wato dole sai ya auri Ummi. Haka kawai yake jin zuciyarsa tana danasanin wannan Istakharan da ya yi. A lokaci guda ya yi tunanin yin cilli da mafarkinsa. Sai dai hakan ya gagara, duk wani motsi idan ya yi sai mafarkin ya faɗo masa a rai. Yana son samun Daddy da magana akan Suhaila, don ya ji wasu abubuwan, sai dai kuma ina ruwansa? Kowa yasan shi baya shiga abin da babu ruwansa.

  Da sassafe Sadiq ya zo gidansu, a lokacin Farouk yana shirin tafiya Office, akwai aikin da zai yi. Ya yi mamakin ganinsa.

 Sadiq ya dube shi da ruwan lipton ya yi murmushi ya ce,

“Malam mu dage muyi aure wannan shekarar. Yanzu haka zuwa na yi, ingaya maka zan bar ƙasar, amma ina dawowa su Alhajina za su je nema mini auren Suhaila, ina son yarinyar nan da gaske.”

A take ya tuna kalaman Suhaila ana gobe Sulaiman zai mutu. Ya ɗan yi shiru, kafin ya ce,

 “Allah ya dawo da kai lafiya. Ka dage da addu’a wajen neman alkhairin auren.”Har suka rabu Farouk bai daina zazzafan tunani ba. Idan Sadiq ya tayar da maganar aurensa da Suhaila ƙila shi ma a matsa masa akan nasa auren. Anya kuwa ba zai bi shawaran tsohon nan ba?

‘Zaka faɗa cikin jarabawa kala-kala, zaka yi tunanin babu mai sonka ne kaf duniya.’

Farouk ya girgiza kai yana ware idanunsa,

“Hakan yana nufin har Anti da ba na haɗa soyayyarta da kowa za ta iya juya min baya? Ni kuwa wani irin kuskure zan iya aikata masu haka? Kai a’a bana jin zan iya faɗawa halaka ina gani, kuma da idanuna. Iyayena sune farin cikina ba zan taɓa son abin da suke ƙi ba.

<< Kaddarata Ce 4Kaddarata Ce 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×