Skip to content
Part 9 of 14 in the Series Ba'indiya by Haiman Raees

Ga Kangana Ranaut shugabar duk ‘yan gagara

Ba kya son raini ke ɗin kuma yau kin shahara

Ba kya ɗaukar wulaƙanci gashi yau kin faskara

Jajircewarki ta sa ki ga shi yau kin gagara

Karfin zuciyarki ta sanya yau kin wuce hantara

Ah! Mai girma Kangana ga waƙarki yau tana jira.

*****

Kyakkywar jaruma doguwa mai ƙirar damisa

Duk wani tsuntsu da ya ganki dole ya haura bisa

Ƙwararrar jaruma mai taƙama ko da babu busa

Maƙiyanki gaba ɗaya kin yi musu ƙusa

Zafi ko barkono sai dai ya yi miki tausa

Me jiji da kai kin zarce ayi miki ƙusa Kangana

*****

Ko da an ƙi ko da an so kin yi musu nisa

Komai girman ƙato ke ɗin ba kya jinsa

Macen farko a Bollywood da ba ta kissa

Ga Darakta ko jarumi domin ɗaukar fansa

Kin yi mun gani ke ce uwar sambisa

Cau! Cau! Cau! Cau! Cau! Cau! Cau! Cau! Ina yi miki jinjina

*****

A daka, a raya, a raba sai kalwa

Wani naman kai dai malam je ka gun giwa 

Wani labarin in ka na so ka je wajen kurma

Wani tarihin in kana so ka je garin bama

Wani al’amarin dai ganinsa sai a fagen fama

Shege shi ka fasa ɗan halas sai dai ya mutu yana fama.

*****

Jamilu ne katibin nan ke yi miki jinjina

Dakyau jaruma bango da ke aka jingina

Watarana matan Bollywood da ke za su dangana

Ko yanzu in kana so jeka ka tambaya

Ita ce ƙwal kowa ya sani ba ma zancen fariya

Na barki lafiya Kangana uwar ‘yan kangara.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Ba’indiya 8Ba’indiya 10 >>

2 thoughts on “Ba’indiya 9”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.