Fachankan wani K'auye ne dake k'aramar hukumar Jigawa, rayuwar K'auyan abun sha'awa ce, sai dai suna da k'arancin addini harda ma na boka, bawai babu Makarantun ba, a'a sunfi ba sana'arsu mahimmanci, da yawan y'an matan garin talla suke yi, sai kaga budurwa tana tallar abinci da dai sauransu, sana da kin kai shekara sha uku ko hud'u za'a fara shirye-shiryen aurar dake, da yawansu suna durkusar da yaransu, sai kiga yarinya k'arama ta tsufa da wuri, gara ma mazan garin idan suka dage suka gama secondary, tofa. . .