Skip to content
Part 12 of 26 in the Series Kauthar by Jeeddah

Adidat Morisola Shehu!

Ta san wannan sunan kamar, ko ma fiye, da yadda tasan sunanta. Sunan mahaifiyarta ne fa.

Sai dai ba kamar yadda ta yi tsammani ba daga farko, ba musayar kalamai bace ta soyayya ko gaisuwa ko wani abu makamancin haka tsakaninta da Alhaji Isma’il, a’ah, sakonnine na zagi da rashin kirki sosai, daga baya ma sai tuhuma da threats da black mailing ya fara biyowa baya.

Kamar a wani sako da aka ce,

“Wato kai girman kai da dagawa ko? To ina mai tabbatar maka da cewa idan har baka janye matakan daka dauka ba, to ka kuka da kanka akan duk abinda zai biyo baya!”

“Isma’il na fada maka fa baka isa ka muzanta ni ba wallahi, kayi kadan! Na rantse da Allah sai na sa kayi dana sani!”

“Ka turo mun da naira miliyan daya da rabi yanzu-yanzu, ni kuma zan rufa maka asiri. Idan ba haka ba kuma…!”

“Tunda kace kaji ka gani, na dauki Kauthar, zan tafi can wata duniyar inda baka sani ba. Duk ranar daka shirya bani abinda na bukata, sai ka dawo min da amsar sakona!”

Anan sakonnin suka kare.

Ji tayi kanta da gabadayan jikinta ma suna wani irin juyi da wulwulawa, kamar wadda ake spinning.

Me yake faruwa ne? Me kuma take gani?

Mahaifiyarta? Blackmailing? It can’t be! Ko kuwa dai?

Ko kuwa wannan shine dalilin daya sanya Daddy ya sha gargadinta akan ta fita harkar mahaifiyarta? Ya sha fada mata nemanta ba alkhairi bane a gareta? Dalilin da yasa Anty Aisha take fada mata ta yi hankali, kada taje ta tono abinda zai binneta da ranta? Ko kuwa ba shi bane?

Bata san lokacin data sanya hannunta da yake rawa ta janyo wayarta ba. Sam ta manta da cewa Anty Aisha bata kasar, sai data kira lambarta taji a kashe. Gashi bata da layinta na can, don da su Lukman kadai take gaisawa.

Ta lalubo sunan data dorawa layinsu ta danna kira. Duk wani kara da shiga kunnenta, sai ta ji bugun zuciyarta ya kara yin sama, kanta yana wani yuuu…

Sai da ta yi kamar zata katse ba a daga ba, sannan aka daga. Ta yi saurin katse Mahmoud daya daga wayar da kwaratsi, tana tambayarshi ina Mommynsu? Yace, “Gata nan!”

Kafin ma ta iya cewa wani abu, ta ji sallamarta tana ratsa mata dodon kunne. Ta amsa sallamar a gaggauce, ta fara watsa mata ruwan tambayoyin da suka sanya ta kirata.

Cewa ta yi, “Anty Aisha wasu sakonni na karanta a tsohon sim card din Daddy, na kuma ci karo da wasu irin sakonni wadanda basu da ma’ana ko madafa. Ki fada min, wacece mahaifiyata? Tana ina? Kuma wane daliline ya sanya Daddy ya dinga hanani kusantarta?”

Anty Aisha shiru ta yi cikin mamakin ta yadda aka yi har ra iya lalubo wannan katoton sirri da suka rufe suka adana, amma idan tayi la’akari da wacece Kauthar, yarinyar da idan ta sanya ranta akan abu ko za ayi me sai ta ga bayanshi, ba abin mamaki bane. Don haka bata ga abin boye-boye ba ko kuma pretending.

Tace, “Kauthar, wannan magana ce wadda babu ta yadda za a yi ta yiwu a waya, saboda bana tunanin zaki iya fahimtata ko ma ki yarda dani kwata-kwata. Don haka kiyi hakuri, ki bari har sai mun dawo, ni kuma nayi miki alkawarin fada miki duk abinda kike son ji!”

Murya na rawa cike da karaya, hawaye sun cika mata idanu take rokonta, “don Allah, ko yaya ne, ki sanar dani wani abu! Zuciyata ba zata iya jure har sai kun dawo ba!”

“Kiyi hakuri har zuwa lokacin da zamu dawo din Kauthar!”

Abinda ta iya ce mata kenan, ta kashe wayar.

Iyaka tashin hankali da bacin rai Kauthar ta shiga har kololuwarshi. Ta dafe kai tana jan salati a cikin ranta.

Lambar ta sake dannawa kira, amma har ta katse ba a daga ba, ta sake kira, nan ma shiru. Wayar ta daga gabadayanta ta yi jifa da ita. Ta hadu da bango ne ko kofa? Ko daga kai bata yi ba lokacin da kara ya shiga kunnenta na faduwar abu.

Dawowarshi kenan cikin ofishin, karar ya ziyarci kunnenshi. Ya juya ya kalleta a nutse, zuciyarshi na mintsilinshi, me ke damunta ne? So yayi ya daure kawai yaje ya cigaba da gudanar da ayyukanshi, musamman ganin da yayi yan kwanakin a sama take, amma ya kasa.

A hankali ya taka zuwa kofar ofis din nata, knocking yayi a hankali tare da tura kofar ya shiga.

Ta daga kai ta kalleshi da idanuwanta da suka rine sosai da kwalla ta bakin ciki da takaici, kuka take so tayi, amma tana daurewa ranta saboda bata so dauriyarta ta gaza tun daga nan.

Murya a sanyaye yake tambayarta, “lafiya? Mene ne yake faruwa?”

Ta ciza baki, “Babu komi.”

Kallonta yake da wannan kallo nashi dake sanyaya mata gwiwa, taji diyan hanjinta na motsawa ita kuma ba mai jin yunwa ba. Ya kalli inda tayi wurgi da wayarta, ya kara kallonta.

Yana kokarin sake jefa mata wata tambayar, tayi saurin rufe idanunta tana girgiza kai,

“Kaina ciwo yake yi sosai, ina so in dan kwanta in huta.”

Ganin dai da gaske ba zata fada mishi ko menene ba, yasa ya gyada kai cikin saddakarwa, ya juya ya fita.

Bakin aikinshi ya koma yana yi, amma rabin hankalinshi a kanta yake.

Yafi minti goma da barinta, amma ko motsawa daga inda take zaune bata yi ba. Daga karshe ma sai ta tashi tayi freezing glass din ta yadda babu wanda zai dinga hangota.

Har aka tashi bai kara ganin giccinta ba. Lokaci yana yi kuwa yayi zumbur ya warci jakarshi, ya nufi ofishinta kamar wanda yake da niyar balla mata kofar.

Kafin ya kai ga yin knocking, an bude kofar, ta fito. Tayi composing kanta sosai fiye da dazu, yadda ma kasan ba ita bace hargitsattsiyar nan ta dazu ba.

Suka jera su duka suka fita waje, ma’aikata na ta musu sallama da daga musu hannu har suka karasa wajen motarshi.

Tafe suke akan titi yana tuki a nutse, amma rabin hankalinshi a kanta yake. Ita kam sam bata ma kula dashi ba, ta yi nisa ta lula a cikin duniyar tunani da kwata-kwata abubuwan da suke faruwa a kusa da ita suka bacewa gani da jinta.

A hankali ya kai hannu ya kamo nata hannun data sarke tana murza yatsunta da jansu cikin alamu na zullumi da tunani.

Tausassan hannun nashi ya wadatar mata da wani irin dumi da comfort, da yasa ta kasa kokarin kwace nata hannun. Ta jingina kanta da kujera cikin dogon tunani, zuciyarta na kissima mata abubuwa kala-kala har ta rasa wani kalar zare zata kamo.

Strangely, rikon da yayi mata kadai yasa taji ta dan fara nutsuwa, har ma zaren tunaninta ya fara barin kan al’amarin data tunkudowa kanta, ya koma kan lallausar fatar hannun AbdulMalik, kamar bata namiji ba saboda yadda take da taushi, ta fara gangarawa zuwa ga lallausan, baki-sidik din sajenshi da ko a lokutan baya ta sha fadi, yana daya daga cikin charms dinshi. Ga wannan siririn dogon hancinshi. Siraran lebban bakinshi wadanda suke su ba a cike ba, kuma ba a sirance ba…

Bata san cewa ta bude idanunta tana kare mishi kallo ba sai a lokacin. Ta zabura ta warce hannunta ta kudunduneshi a cikin kayanta, ta kuma juya kanta can daya barin guda.

Bata kara waiwayawa ta kalleshi ba har suka karasa gida. Suna zuwa kuwa ta warci kayanta tayi ciki a sukwane kamar zata tashi sama saboda sauri.

Shi kuwa ya yi sararo yana binta cikin mamaki da tu’ajjibin wannan iko na Allah.

*****

Da dare kin bari su hadu ma tayi. Kafin ya dawo daga masallaci har ta ci abinda zata ci, ta shige daki ta kulle. Ya bita har dakin nata ya dinga knocking amma ta ki budewa, dole ya kyaleta ya koma yaje ya ci nashi abincin.

A gajiye yake tilis, jin jikinshi yake kamar wanda aka sameshi aka mishi dukan tsiya. Hakan ba shi ya hana shi lalubar doguwar kujera ba ya zauna ya hau aikin daga sakonni da maida amsa ba. Bai san lokacin da gajiyar ta ci karfinshi ba, ya bingire anan kan kujerar yana barci mai nauyi.

Wajen karfe daya da rabi ta farka, makoshinta a bushe kamas kamar wadda ta kwana ta yini a cikin sahara. Ta lalubo wayarta ta bude cikin fatan Allah Yasa ta samu amsar tarin sakonnin data turawa Anty Aisha da suka fi a kirga, amma bata ga komi ba sai sakon MTN. Ta saki tsaki, zuciyarta na kara cushewa.

Dira tayi daga kan gadon, ta sanya silifas ta fita daga dakin. Kai tsaye ta wuce kicin ta bude firjin ta dauki robar ruwa daya ta fasa, ta fara daddaka kamar wadda ta shekare ruwa bai ga bakinta ba.

Karan bude kofar ne ya tasheshi daga barci. Ya daga idanu a hankali ya bita da kallo cikin doguwar rigar data sanya ta barci. Shara-shara ce purple, marar nauyi, mai hannun spaghetti. Yadin mai santsine, rigar kuma pencil ce wadda ta bi mata jikinta kwarai da gaske. Daga gefen gwiwarta kuma zuwa kasa an yanka shi, duka kafar a waje.

Ya bita da kallo bayan ta wuceshi har ta shige kicin, ya koma cikin kujerar ya kwanta yana hadiyar yawu kamar wani tsohon maye.

Bai san ya aka yi ba sai ganinshi yayi ya mike tsaye, ya bi bayanta zuwa kicin din.

Tana tsaye ta juya mishi baya tana shan ruwa, shima ya raba ta gefenta, ya bude firjin din ya ciro ruwa mai sanyi, ya bude ba tare daya kai robar bakinshi ba.

Juyawa yayi ya jingina da firjin din suna kallon juna shi da ita.

Kallonta yake kasa-kasa, ita kuma tayi biris dashi kamar bata san Allah Yayi ruwan tsirarshi ba.

Sai shine yayi gyaran murya, yace mata, “gabadayan yau you seem off, akwai abinda yake damunki ne Kauthar?”

Ta dan yamutse fuska, “ban gane ba? Dama yanayin rayuwa ta yau da kullum, dole ne sai mutum ya kasance a cikin farinciki ne a koda yaushe?”

Ya girgiza kai, “ba haka nake nufi ba, kema kuma kinsan da hakan. Abinda nake nufi shine, na kula kamar kina cikin damuwa ne, shine nake tambayarki ko menene damuwarki.”

Idanunta suka yi rau-rau, amma ta dake ta kawar da kanta daya gefen, “Damuwata ba taka bace, don haka ka kyaleni, ka kuma daina tambayata!”

Ta dire robar ruwan akan slab din kicin da karfi, ta juya zata fita. Caraf! ya riko hannunta.

Yayi nasarar tsayar da ita a waje daya, amma bata juya ta kalleshi ba. Ya zagaya gabanta yana kallonta idanunshi dauke da tausasawa da tausayawar da suka sanyata taji kamar ta zube a wajen tana kwasar kuka.

Murya a sanyaye, kuma cike da nutsuwa da alamun kwantar da hankali yake ce mata, “dama ba wai nace damuwarki dole tawa ce ba, all I’m saying is that, wasu lokutan, fadawa wani damuwarka kan rage maka zafi da radadin damuwar. Ko mutum bai yi maka maganinta ba, zai tayaka alhini da addu’a. Ina kuma so ki sani, ina daya daga cikin mutanen dake yi miki addu’a da tayaki alhini sosai da sosai Kauthar!”

Sai taji gwiwarta tayi mata sanyi. Fadan ya fita daga jikinta fit, kamar an zare mata shi. Tana ji ya ja ta cikin jikinshi ya rungume, yana shafa bayanta a hankali cikin alamun lallashi. Kanshi ya nutsa a cikin gashin kanta yana shakar daddadan kamshin da take fitarwa.

Hakan yayi mishi, bai kuma ki ace sun kasance a haka ba har gari ya waye.

Har kara riketa ya dinga yi lokacin data fara kokarin zamewa, amma ta silale ta kwace. Ta daga kai tana kallon saman kanshi ba tare data bari sun hada idanu ba saboda wani nauyinshi da taji ya dirar mata.

Murya a sarke, mai cike da in-ina, tace, “am okay now, na gode!” Ta juya a hankali tana tafiya, ya bita da kallo.

Daki ta koma ta kwanta, amma sam sai taji barcin ya kauracewa idanunta. Duk sanda zata rufe idanunta, sai ta dinga jiyota a cikin jikin AbdulMalik. Ko ta tsinto hannunta a cikin nashi. Barci ya kaurace mata kwata-kwata, tunanika suke zuwar mata iri-iri, shin dama wannan shine kawa zucin da take jin mutane da suke a cikin soyayya suna fada? Ka dinga tunanin mutum da duk wasu abubuwa da suka danganceshi har su kai ga hanaka barci?

Ka dinga kewar mutum duk kuwa da cewa tsakaninka da shi rufaffiyar kofar daki ce kawai da taku wanda bai fi ashirin ba?

Daren ranar dai su dukansu biyun haka suka wanzu, barci yayi musu kwalele.

Shi yasa washegari duk suka tashi furu-furu dasu kamar wadanda suka sha dambarwar fada.

*****

Kwanakin da suka biyo baya, sun kasance cikin aiki tukuru a gida da ofis, saboda ayyukan wasu wuraren shakatawa da na motsa jiki da aka basu kwantiragin redecorating a can Agege. Hakan ne yasa suka zama busy sosai, lokacin zama tattaunawa game da wani abu ma yayi musu wahala.

A gefe guda kuma Anty Aisha ta toshe duk wata hanya da zata sadata dasu, hatta da su Lukman ta kai ga ta daina samun wayarsu. Wannan bai kara mata komi ba sai wani tunaninlnbda karin damuwa, a kullum idan taje kwanciya ko kuma ta tashi daga barci, tunaninta bai wuce, “wacece mahaifiyarta? Wacece ita a waje mahaifiyarta? Menene kuma sanadin da yayi dalilin rabuwar aurenta? Shin rashin so ne da rashin adalci kamar yadda mahaifiyarta ta fada mata shekara da shekaru, ita kuma ta hau kai ta zauna daram?”

Wannan weekend din da yazo baki suka yi, Na’imah da Umaimah suka je musu hutu. Cikin ikon Allah kuma taji dadin zuwan nasu kwarai da gaske. Kwanansu biyu kacal a gidan, amma sai taji kamar kada su tafi. Sun dauke mata kewa sosai, har suka sanya ta fara mantawa da abubuwan dake faruwa a tare da ita.

A daren ranar da zasu tafi, tana dakin da aka yiwa su Umaimah din masauki suna hira saboda tun da asubahi zasu tafi a washegarin.

Malika tana zaune a gaban dressing mirror, Umaimah kuma tana kwance a kan katifa tana latsa wayarta, ita kuma tana zaune a gefen katifar tana kallon Malika data dage tana ta shan hirar soyayya da Mas’oud saurayinta.

Umaimah ta kalleta tana murmushi, “ki daina wani mamakin yarinyar nan fa, idan ta fara waya da wannan dan’anacen saurayin nata, sam bata son dainawa!”

Kauthar ta danyi yar dariya, Malika kuma ta jefeta da harara tana cigaba da wayarta.

Umaimah ta juya tana kallonta, “tunda muna maganar soyayya ne, Anty Kauthar me ke faruwa ne tsakaninki da mijinki?”

Ta kalleta a kaikaice, “ban gane ba?”

Zuwansu gidan ba shi yasa ta koma dakinshi da kwana ba, amma kuma zuwan nasu ya matukar rage mata yawan zaman daki da take yi musamman a ranakun karshen mako. Ko babu komi suna yini cur suna hirarraki da gudanar da wasu al’amuran har shi AbdulMalik din.

Kafada ta daga, “Just saying. I’m sorry to say, yanayinku sam bai yi mun kama da ma’auratan da suke a cikin soyayya ba, musamman irin ta sabon aure, kin dai gane abinda nake cewa!”

Yadda tayi maganar tana daga gira ya ba Kauthar dariya duk da wani tukuki da taji yana dabaibaye mata zuciya.

Umaimah ta koma ta kwanta, “ba wai ina sanya muku ido bane ba fa, ba kuma wai don Yaya dan’uwana bane, amma seriously Anty Kauthar, ki buda ido ki ga yadda mata suke karakaina da jan layi akan shi. Kada kuma ki manta da cewa he’s a hot-blooded man. Wallahi ki tashi tsaye tsayin daka, ki rike mijinki kada kiyi wasa dashi wata ta miki sakiyar da ba ruwa fa!!”

Zancen ya isheta haka nan. Don haka ta mike babu shiri, ta musu sai da safe ta falla dakinta.

Sai dai duk yadda taso mantawa da zancen Umaimah, abin yaci tura. Maganganunta take tunawa a cikin ranta over and over….

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.7 / 5. Rating: 26

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kauthar 11Kauthar 13 >>

7 thoughts on “Kauthar 12”

    1. Fatima hala baki da subscription ne? Yanzu ba zaki samu damar karanta Kauthar ba sai kinyi subscription. Daddadan albishir kuma shine an kammala Kauthar din gabadaya 💃

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×