Mutanen biyar sun hadu ne a Jami'ar Wukari dake nan cikin garin Taraba. Su dukansu sun kasance daga mabanbantan garuruwa da kabilu idan ka debe Isma'il da Aisha, kasancewarsu duka mazauna garin Abuja.
Isma'il da Nuhu abokai ne na kut da kut, sun hadu a makarantar kwana ta federal government Cikaji, bayan sun gama kuma suka samu Federal University Wukari suka tafi can. Yayinda mahaifan Nuhu suka kasance mutanene masu matsakaicin hali, Isma'il mahaifanshi suna da arzikinsu daidai gwargwado. Asalin Mahaifanshi haifaffun garin Gombe ne, Mahaifinshi soja ne wanda ya rike matakan soja masu yawa kafin. . .
Lallai wannan matar ma ba kunya a lamarinta
Hummn. Ki bari kawai