Skip to content
Part 15 of 26 in the Series Kauthar by Hauwau Shafiu (Jeeddah)

Mutanen biyar sun hadu ne a Jami’ar Wukari dake nan cikin garin Taraba. Su dukansu sun kasance daga mabanbantan garuruwa da kabilu idan ka debe Isma’il da Aisha, kasancewarsu duka mazauna garin Abuja.

Isma’il da Nuhu abokai ne na kut da kut, sun hadu a makarantar kwana ta federal government Cikaji, bayan sun gama kuma suka samu Federal University Wukari suka tafi can. Yayinda mahaifan Nuhu suka kasance mutanene masu matsakaicin hali, Isma’il mahaifanshi suna da arzikinsu daidai gwargwado. Asalin Mahaifanshi haifaffun garin Gombe ne, Mahaifinshi soja ne wanda ya rike matakan soja masu yawa kafin ya tsunduma harkar siyasa. Siyasar ce ta kai mahaifinshi can, yana rike matsayin dan majalissa mai wakiltar Jaha. Nuhu kuma suna zaune ne a garin Kaduna kafin daga baya suka koma garin Abuja, mahaifinshi ma’aikacin banki ne.

Aisha ma mazauniyar garin Abuja din ce, iyayenta yan garin Naija ne, aiki ya kai mahaifinta Abuja wanda ya kasance shi yake rike da gidan mujallar Aminiya a wancan lokacin. Mahaifinta Banufe ne yayinda mahaifiyarta take Bahaushiya.

Adidat kuma yar garin Keffi ce dake Lafia, a wani kauye can da ake kira Yar Kadde.

Zaman daki ya hada Adidat da Aisha.

Iyayenta talakawa ne tulis, makarantar ma da kyar da jibin goshi ta iya hada kudin registration dinta. Tana karantar Economics, Aisha kuma tana karanta Business Administration.

Adidat macece mai matukar son kudi, za kuma ta iya yin komi matukar zata samu kudin in dai ta hanyar halas ce. Wannan dalili yasa suke zaman cudeni in cudeka ita da Aisha. Aisha ta dauke mata duk wani nauyi na abinci da hidimarta, ita kuma sai ta zama kamar yar aikin Aisha din. Ita zata musu girki, wanki, guga, shara, daukar ruwa da komi ma.

Hakan bai dameta ba tunda dai zata ci ta kuma sha ba tare da tunanin ta inda wani abincin zai fita ba. Kuma Aishar tana matukar taimaka mata da kudaden kashewa dana sayen littafai da text books.

Koda shekara ta zagayo suka wuce ajin gaba, Aisha sake kama musu wani dakin tayi su biyu suka cigaba da zamansu cikin kwanciyar hali. Zuwa lokacin sun zama kamar tif da taya, sun zama abokai.

A shekararsu ta biyu ne suka hadu da Nuhu a wani course daya hadasu. Shi yana karantar Banking and Finance a shekararshi ta uku.
Ba soyayya suke yi ba, kawai suna gaisawar mutunci ne dashi. Kuma ta sanadiyyarshi ta hadu da Isma’il wanda yake department daya da nata.

Duk da cewa Isma’il din ya tsere mata da shekara daya, amma suna haduwa dashi akai-akai, yana koya mata abubuwan da suka yi mata duhu. Nan da nan kuwa sai wata irin soyayya ta kullu mai matukar girma a tsakaninsu. Aisha ta fada cikin matsananciyar soyayyar Isma’il, ta kai ta kawo idan bata ganshi ba a rana bata jin dadi sam. Duk da cewa shima ta bangaren nashi haka take.

Yawan tsokanar da Adidat take mata game da sayayyarta da Isma’il, yasa itama sai ta hadata da Nuhu. Cikin ikon Allah kuma sai suka fara soyayya, duk da cewa dango-dango ce, tana rawa a sama. Shi dai Nuhun tsakaninshi da Allah sonta yake yi ba da wasa ba, ita kuma ta kasa gano abinda ke cikin ran Adidat din. Kullum ta mata magana idan sun samu wata matsala ko kuma ta mishi wani rashin kirki kamar yadda ta saba, sai tayi ta kawo mata uzirurruka, har daga karshe dai ta share maganar ta kyalesu.

Suka cigaba da karatunsu da soyayyarsu ita da Isma’il dinta babu kama hannun yaro abinsu.
Kwatsam sai watarana Adidat ta gabatar musu da AbdulFatah. Tace dan uwanta ne, shima kuma karatun yake yi amma a shekararshi ta karshe yake yana karantar Accounting.

Ba tare da wani zuzzurfan bincike ba suka karbeshi da hannu bi-biyu. Su biyar din dai suka zama kamar tsintsiya madaurinki daya.

Abu daya da yake shiga tsakanin Adidat da Aisha a zamantakewarsu shine roko. Sam-sam Adidat bata da kunyar roko, bata kuma da jin nauyin daga baki ta roki mutum. Ta ishi Nuhu da bani-bani, sai ya zamana har nema ta dinga yi ta maida hidindimunta da dawainiyarta kanshi.

Aisha tana yawan yi mata magana game da hakan. Ta kan ce, “ki dinga la’akari da halin rayuwa da halin da shi kanshi Nuhu din yake ciki mana. Wasu al’amuran kawai baya fada ne, amma shi ido ai ko da ba mudu bane, yasan kima. Sai ki dinga sassauta mishi tunda dai yanzu baki zama dolenshi ba”
Sai ta gyada kai kamar gaske, tace, “hakane!”
Amma hakan ba shi zai sa ta sake lalaubarshi ba idan bukatar hakan ta tashi.

Duk kuwa lokacin da tace ya mata kaza ya ki yi, ta dinga mita kenan da fadace-fadace. Abin ya dinga batawa Aisha rai har ta dinga danasanin hada su din da tayi.

Dadinta ma da Nuhun ya kasance mutum mai saukin hali da kuma rashin dorawa rai. Idan ya ga zai iya yi mata abu zai yi, wanda ba zai iya yi ba zai fada mata ba zai iya ba, sai kuma ya koma gefe ya zubawa sarautar Allah ido.

Tayi fushinta na kwana da kwanaki, daga baya kuma ta dawo da wata sabuwar tsirfar.

A haka dai suke ta lallabawa har Allah Yasa suka sake shiga wani ajin. Su suna aji uku, Nuhu da Isma’il suna shekarar karshe, yayinda AbdulFatah ya kammala nashi karatun amma ya cigaba da zama a makarantar saboda maimaicin wasu darussan daya samu.

A cikin hakan ne aka aiko musu da rasuwar mahaifin Nuhu. Dama mahaifiyarshi ta jima da rasuwa. Ya ji rasuwar kwarai da gaske. A ranar kuma ya tattara ya tafi Abujar.
Suma anyi hakan da kwana biyu suka tafi su duka hudun wajen gaisuwa.

Bayan sun isa Abujar, suka je gidansu Nuhu wajen gaisuwa. Wanda tun daga kallon yanayin unguwar tasu Adidat take ta tabe baki, suna ta zabga yare ita da AbdulFatah. Duk da dai bata san me suke cewa ba amma ta san bai wuce na yanayin gidan da suka tarar bane. Gidane na haya, kuma na masu karamin karfi tulis wanda ya ga jiya ya ga yau.

Adidat din bata yi kasa a gwiwa ba sai data furta maganar bayan sun fito daga gidan gaisuwar.
Take cewa Aishar wai, “ashe ma su Nuhun ba wasu masu kudi bane har yake yiwa mutane wani takama da dagawa?”

Ita kuwa bata yi wata-wata ba tace, “ehh, amma dai yana cikin wadatar zuci da godiyar Allah, kuma baya hangen abinda ke hannun wani, sannan kuma baya mu’amalantar wani saboda yana da wani abu.”

Saboda zuwa lokacin Aisha ta gama fahimtar Adidat din tana tare da ita ne kawai saboda abin hannunta da alherin da take yi mata. Wannan dalilin ne ma yasa ta yanke shawarar shekara mai zuwa kawai zata raba mazaunine da Adidat din. Saboda ta tsani munafunci ita. Tana zaune da ita da zuciya daya, ita kuma tana zaune da ita saboda wani dalili.

Bacin rai sosai ta nunawa Adidat game da maganganunta akan halin da suka samu gidansu Nuhu. Adidat data fahimci hakan nan da nan sai tayi kalar nadama, ta yi kasa da kai ta hau bata hakuri. Dama kuwa akwai ta da ladabin dan kunama. Har dai ta samu Aisha din ta dan sassauta.

Daga nan sai suka wuce gidansu Aisha saboda gidansu Nuhu ba zai zaunu ba balle ayi maganar kwana. Isma’il kuma ya wuce da AbdulFatah gidansu ya kwana tare dashi.
Wannan shine karo na farko da Adidat taje gidansu Aisha. Ita kuwa Aisha ta taba zuwa garinsu Adidat din, ta kuma ga yanayi na rashi da suke ciki lokacin da kanwar mahaifiyarta ta rasu. Duk da cewa ma wai ba can cikin kauyensu suka shiga ba. A garin Keffi suka tsaya.

Adidat ta ware ido sosai tana kallon gidansu Aisha kamar bata taba ganin gida mai kyan shi ba. Duk da cewa zata iya yiwuwa hakan take.

Suka yi masauki a dakin Aishar, bayan sunyi wanka sun huta, aka gabatar musu da abinci da abin sha suka ci suka yi nak dasu suka hau barci.

Kwanansu biyu anan kuma kullum sai sun je gidansu Nuhu wajen gaisuwa. Aisha ta kula da halin da Adidat take nunawa Nuhu, duk da hakan yana bata mata rai, amma bata nuna mata ba. A ranta ma sai ta raya gwara su rabu kawai, saboda a yadda take nunawa a haka, idan ma suka yi auren ai ba lallai zaman yayi dadi ba. Don haka ta kyaleta.

Tun zuwansu basu kara haduwa da Isma’il ba, saboda a lokacin waya bata wadata ba, sai tarho, kuma basu cika yin waya ta nan ba.
Sai ranar da zasu tafi sannan suka je gidansu Aisha din, bayan sun gaisa da mahaifanta, kuma suka dunguma gidansu Isma’il don su gaisa da nashi iyayen.

Ita kanta Aishar bata taba zuwa gidansu ba sai ranar. Su duka sun kidima da ganin gidansu Isma’il din. Gidane gari guda, lullube da masu tsaro sahu-sahu.

Adidat ta sake baki ta dinga santi da zabga kauyanci, tun Aisha na tsawatar mata tana dan kwabarta, har dai ta hakura ta kyaleta.

Mahaifiyarshi ta karbesu hannu bibiyu, duk da cewa sai da suka ci abinci a gidansu Aisha, amma haka ta sake shakesu da kayan ciye-ciye da shaye-shaye.

Yadda Adidat ta kasa boye zakwadinta game da irin dukiyar dake shake da gidansu Isma’il abin ya matukar kunyata Aisha, kuma ya bata haushi sosai. Ta yi ta kokari dai tana dannewa.

Da yake mahaifiyarshi ta san da soyayyar dake tsakaninsu, da zasu tafi haka ta shake jaka da abubuwan bukata ta ba Aisha. Itama Adidat din ta bata.

Mahaifinshi kuwa dubu goma-goma haka ya basu su duka. A wancan lokacin kuwa dubu daya ma kudi ne ba kadan ba balle dubu goma. Adidat fa ta dimauce iya dimaucewa. Wadannan kudadene da bata taba ganin kamarsu ba balle tace nata ne, taga kuma su sun daukesu ma kamar ba a bakin komi ba.

A hanya ta duka tana yiwa Aisha gulmar kudin da irin tsadaddun kayan sawa da mayukan shafa da Hajiya Hadiza mahaifiyar Isma’il ta ba Aisha. Harara Aishar ta jefa mata tana jan tsaki, tace, “wai ke don Allah baki iya gani ki kyalene?”

Bata sake kulata ba har suka karasa Taraba.
Kasancewar jarabawa zasu fara ta karshen zango, Nuhu bai dauki dogon lokaci ba ya dawo.

Aisha bata yi mamakin jin cewa sun rabu da Adidat ba don ta gama lura da take-takenta. Bata ce komi ba sai fatan Allah Yasa hakan shi yafi alkhairi. Sayayyarta da Isma’il kuwa a lokacin kamar ana zubawa shuka ruwa saboda yadda take kara bunkasa kullum.

Su Nuhun suna ta shirye-shiryen fita da zana jarabawarsu ta karshe, Isma’il ya sayi sabuwar wayar salula ya ba Aisha. A wannan lokacin ko cikin wane da wane ma rike waya bata karamin mutum bane. Shi kuwa yayi hakan ne saboda idan sun gama karatu sun tafi bautar kasa babu ta hanyar da zasu dinga jin muryar juna.

A wannan lokaci maganarsu tayi nisa, don kuwa har an tura gidansu Aisha din, daya dawo daga bautar kasa za a daura musu aure lokacin itama ta gama nata karatun. Don haka abin ba a cewa komi sai son barka.

Wata sabuwa inji yan caca, maimakon halin Adidat su ragu ba sai abu ya karu ba? Sai gata wai tana bin Isma’il tana rokonshi. Ita Aisha bata san komi ba, sai da suka gama jarabawa da komi, sun shirya su duka ukun zasu tafi Abuja rana daya tunda su sun gama komi da komi, ita kuma sun samu hutu.

Washegarin zasu tafi kawai sai Isma’il ya bata dubu biyu akan ta ba Adidat. Wai ta rokeshi ya bata kudin motar zuwa gida.

Abin ya bata mata rai sosai. Saboda a yadda suka yi da ita, cewa tayi ba zata je gida hutu ba. Zata zauna ne anan makaranta tunda suna da sauran kayan abinci kafin Aisha din taje ta dawo. Bata san niyyar da Aishar tayi na raba musu daki ba. Sai lokacin Nuhu yake fada mata yadda Adidat din ta damu Isma’il da bani, yau kudin littafi, gobe na magani, jibi na abinci. Don har cewa tayi ya saya mata waya itama, yace ta dan dakata.

Aisha ta jinjina kai cike da mamaki, saboda bata san da wannan maganar ba, ko da wasa Adidat bata taba fada mata ba.

Data koma daki ranar, sai bata ce mata komi ba. Ta dai dauki kudi ta bata tace inji Isma’il.
Inda jikin Adidat ya fara yin sanyi shine da taga Aisha tana hade kan kayanta gabadaya tana kullewa. Don kuwa bata taba yin hakan ba. Ko zata tafi gida sai dai ta dauki iyaka abinda zata yi amfani dashi acan kawai.

Aisha ta gama hada kayanta tsaf, wasu ta barwa Adidat, wasu kuma ta kyautas, sauran kuma sai gani tayi an je an kwashe ba tare data san inda za a kaisu ba.

Ranar da zata tafi lafiya-lafiya suka yi sallama da Adidat, bata ce mata komi ba, itama haka. Ta tafi ta barta anan.

Kwananta goma da tafiya, lokacin bai fi sati ba su koma, sai ga Adidat din ta dira gidansu Aisha kamar daga sama. Ta nuna murnarta sosai, nan da nan ta ja ta dakinta, suna shiga kuwa ta nemi waje ta zube akan gwiwoyinta, ta dora hannu aka ta dargwaza kuka.

Hankalin Aisha yayi kololuwar tashi, ta dafeta tana tambayarta lafiya?

Cikin sheshhekar kuka ta hau bata hakuri tana cewa ita bata san laifin da tayi mata ba har take son ta raba muhalli da ita, amma tana rokonta da koma menene tayi hakuri ta yafe mata. Tunda dai taga duka-duka shekara daya ta rage musu, tayi hakuri su karasa zamansu tare. Ita idan ma kudi ne sai su raba kudin dakin, amma idan tace zata raba musu wajen zama ita sai dai ta hakura da karatun kawai. Saboda dama ai saboda ita kadai take zaune a Taraba tana karatun, tunda kuma ta juya mata baya to gwara ta bar karatun kwata-kwata!

Aisha tayi mamakin jin hakan duk da dai tasan ta fada ne kawai.

Da dadin baki da kisisina sai da Adidat ta samu ta shawo kan Aisha ta hakura.
Nan ta samu waje gidansu Aisha din ta karasa hutunta.

Kafin su koma har an gama musu komi tun daga registration har wajen da zasu zauna an kama musu.

Su Nuhu kuma an tura su bautar kasa. Cikin sa’a Isma’il an barshi anan Taraba, Nuhu kuma an tura shi Bayelsa.

Saboda haka ko bayan komawarsu basu rabu da juna ba shi da Aisha, kusan koda yaushe suna tare, idan ba tare ba, to suna manne a waya.

Wata makarantar firamare aka tura shi a can yake koyarwa. Saboda haka a waje yake da zama amma duk da haka saboda kawaici da alkunya irinta Aisha, bata san wajen da yake zaune ba.

Ranar nan sai suka hadu da AbdulFatah a cikin jami’ar, yayi mamakin ganinshi kwarai. Bayan sun gaisa, suka matsa daga gefen hanya yana tambayar AbdulFatah din bayan rabuwa. Sai AbdulFatah din yake ce mishi ai ya jima anan garin saboda har lokacin ba a bashi result dinshi ba, ga shi kuma yana cikin yanayin rashin wajen zama dana abin yi.

Isma’il ya tausaya mishi kwarai da jin haka, har yayi mishi tayin zama tare dashi saboda gida guda ya kama, kuma shi kadai yake zaune a ciki. Da farko dai ya nuna kamar ba zai karbi tayin ba, amma Isma’il din dai ya matsa, don haka a ranar ma ya koma wajenshi tunda dama dai ba wasu kayane na azo a gani ba yaje dasu Taraba din.

Suna zaune kadaran-kadahan, basu cika samun zama bama balle su hadu, don haka kowa harkar gabanshi kawai yake yi.

Ranar nan kwatsam ba sai ga Adidat taje gidanshi ba? Yayi mamaki daya dawo daga makaranta ya samesu ita da AbdulFatah a gidan suna hira ita dashi, don tsabar samun waje ma har ta dafa musu abinci sun kuwa yi rashe-rashe suna dibar gara.

Abin ya girmamashe mishi da yawa, musamman data kalleshi da fara’arta tana yi mishi sannu da zuwa. Murya a sake take ce mishi, “Yaya sannu da zuwa, yanzu nake cewa shiru yau baka dawo da wuri ba!”
Yayi jimm, yana kallonsu cikin wani yanayi, kafin kawai ya jinjina kai zai wuce.

Bata damu da shirun daya musu ba ta sake ce mishi, “ga abincinka fa dana ajiye maka”
Ya girgiza kai, “a’ah, a koshe nake. Na gode da tayi dai!”

Ya wuce daki abinshi ya barsu anan.
Yini guda sur Adidat tana gidan, bata tashi barin gidan ba sai can da yamma. Sai da zata tafi ne sannan ta gabatar mishi da kudirin daya kaita gidan.

<< Kauthar 14Kauthar 16 >>

2 thoughts on “Kauthar 15”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×