Har dakinshi ta bishi ta sameshi tana nanata mishi abinda yake tafe da ita. Kallonta yake cike da mamaki da tu'ajjibi, can kasan ranshi bacin raine dankare.
Yace, "kamar ban ji me kike fada bane da kyau Adidat! Dan maimaita min inji?"
Ta kara durkufawa daga can gefe da take a tsugune, yayinda shi yake zaune akan kujera mai hannu.
Ta kara yin kasa da muryarta, a tunaninta ko tana daukar hankalinshi ne, "wallahi Yaya, zuwa nayi da kokon barar ka taimaka min ka ceceni ka dubi maraicina, ka karbi tayin soyayyata. Wallahi na dade a cikin kogon sonka. . .