Skip to content
Part 16 of 26 in the Series Kauthar by Jeeddah

Har dakinshi ta bishi ta sameshi tana nanata mishi abinda yake tafe da ita.
Kallonta yake cike da mamaki da tu’ajjibi, can kasan ranshi bacin raine dankare.

Yace, “kamar ban ji me kike fada bane da kyau Adidat! Dan maimaita min inji?”

Ta kara durkufawa daga can gefe da take a tsugune, yayinda shi yake zaune akan kujera mai hannu.

Ta kara yin kasa da muryarta, a tunaninta ko tana daukar hankalinshi ne, “wallahi Yaya, zuwa nayi da kokon barar ka taimaka min ka ceceni ka dubi maraicina, ka karbi tayin soyayyata. Wallahi na dade a cikin kogon sonka shekara da shekaru, nayi kokarin in boye amma abin yaci tura, nema yake ya hallaka ni…”

Ta daga ido ta saci kallonshi cike da kissa, “… ka taimaka ka bani masauki a cikin ranka koda dan kankani ne Yayana don Allah.”

Shi Isma’il kasa magana ma yayi, ya dinga kallonta kamar wata mahaukaciya sabon kamu. Idan ba hauka ba kam, shi bai ga dalilin da zai sa ta sameshi da magana makamanciyar wannan ba.

Fuska cike da wani irin kallo na kaskanci da tsana yake kallonta, yace, “kin bani matukar mamaki Adidat! Ke yanzu baki ji kunyar kanki ba? A ganina ko wani kika ji zai aikata irin wannan danyan aikin ai zaki tsawatar mishi, ballantana ki ce ke da kanki zaki yi hakan! To magana daya ita zan fada miki, bana sonki, ba zan taba sonki ba kuma. Koda matan duniya sun kare, ba zan taba daga ido in kalleki a matsayin mace ba. Don haka ki tashi ki bar nan gidan tun kafin ranki yayi mummunan baci!”

Maimakon ta tashin, sai ma ta kara zubewa a kasa har da kama kafafunshi tana roko da ahi, ita kawai ya taimaketa in ba haka ba zata iya mutuwa ta dalilin son shi!

Yace, “ki mutu din mana! Ke ba gwara mutuwar taki bama akan rayuwarki? Wannan butulcin naki ai da an rage mugun iri! Ki tashi ki tafi daga nan kada ki kara kuskuren nuna min fuskarki!”

Ta ja-ya-ja, ranshi yayi kololuwar baci, bai san lokacin daya ja ta ya fitar da ita daga dakin ba. Idan ranshi yayi dubu to a bace yake, ya zageta, ya tsine mata, haka kuma tsabar butulci irinna dan-Adam ya kara tsuma shi, sai yaji kowa ma tsoro yake bashi. Hatta da AbdulFatah sai daya fahimci hakan, don kuwa duf haka ya dauke mishi wuta.
Ita kanta Aishar a yan kwanakin sai data fahimci baya cikin nutsuwarshi, amma koda ta tambayeshi abinda take faruwa, bai iya ce mata komi ba sai kawai ce mata da yayi tayi hankali da Adidat.

Juyin duniya kuma ya ki ya fada mata irin laifin da Adidat din tayi mishi, don haka ta kyaleshi don kuwa shi mutum ne da bai cika son naci ba, ya fi bukatar ka bashi lokaci idan ya nuna baya son abu, in yaso daga baya idan yayi ra’ayi shi da kanshi sai ya fada maka.

Ta dai saka idanu sosai akan Adidat din, kuma dai bata ga wani sabon abu ba akan halayanta na da, don haka daga baya ta watsar da komi.

Har aka yi sati biyu da yin haka bai sake ji daga Adidat ba. Don haka yayi tunanin watakila ko ta saduda, don haka shima sai ya saki jikinshi, musamman da AbdulFatah ya fada mishi zai koma gida saboda ya gama gyara abinda zai gyara a makaranta.

Ranar da AbdulFatah ya tafi sai yaji shi sakwai. Da dare ya fita wajen mai shayi aka mishi hadin kauri kamar yadda ya saba da wainar kwai da biredi, ya rufe gida ya zauna yaci yayi nak! Kudirinshi shine idan ya gama yayi shafa’i da wutiri, sai kuma ya kira masoyiyarshi su raba dare suna hirar kauna abinsu.

Allah cikin ikonSa kuma sai kafin ya ma gama cin abincin sai yaji wata irin kasala ta dabaibayeshi, jikinshi ya saki gabadaya, ko yatsarshi baya iya dagawa. Jikinshi wani irin yammm! yake mishi babu dadi, ya rasa abinda yake mishi dadi.
Zuwa can kuma bayan dan lokaci sai yaji wani abu yana faruwa da jikin nashi wanda ya kasa bambance ko menene.

Cikin wannan halin yaji ana taba kofa, duk da yasan cewa a rufe ya bar kofar gidan, amma ya kasa yunkurin tashi yaga ko menene yake faruwa da gidan, said kawai ya zubawa sarautar Allah ido.
Aikuwa ba a dauki lokaci mai tsayi ba sai ganin mutum yayi a kanshi, ya daga idanunshi da suka yi mishi nauyi sosai, dusu-dusu yake gani har baya iya bambance ko wanene.

“Wa…. wa…”
Kadai bakinshi yake iya furtawa, ya ma kasa hada kalmomi masu ma’ana.
Motsi yaga an fara yi, ana tunkararshi. Kafin kuma yayi kokarin matsawa, an cim masa.
Bai ma kara sanin abinda ke faruwa ba ko inda kanshi yake sai da gari ya waye tangararas.

Ya bude idanunshi da suka yi mishi nauyi sosai, hasken rana yana shigarshi ya rufe idon da sauri saboda jin yadda kanshi yayi mugun sarawa.
Ya jima a hakan kafin ya sake yunkurin bude idanun nashi a hankali, a dakinshi yake akan katifa a kwance. Sai dai iskan da yake kadashi ne ya kasa fahimta.

Jin jikinshi yake kamar wanda trailer ta bi ta kanshi saboda tsabar nauyin da yayi mishi. Cikin rawar jiki ya kai hannu yana shafa jikinshi, sai yaji wayam! babu kaya!

Hankalinshi ya dugunzuma matuka gaya. A hankali ya juya yana kallon gefenshi. Yadda kasan saukar aradu haka yaji kirjinshi ya dauka yana bugawa.

Ba jinin daya gani akan katifarshi faca-faca bane ya fadar mishi da gaba, Illa wadda ya gani. Cikin tsananin firgici da daurewar kai ya furta sunanta, “Adidat kuma?!”

Ya waiga cikin dakin, ya juya, ya rasa yadda zai yi da ranshi, kai tsaye ma yaji wani irin kuka na shirin zo mishi, yayi dakiya irinta da namiji ya danne.

Da kyar da kame-kame ya samu ya tashi zaune. Wani makoko ya kawoshi wuya daya kara kallon Adidat wadda duk wannan bidirin da yake yi bata sani ba. Ya gyada kai ranshi idan yayi dubu a bace, ya riga ya gama hango abinda ya faru, ya kuma san tuggun data shirya mishi. Shi ai ba sakarai bane, yasan ruwa baya tsami banza. Amma zai nuna mata shi ba kanwar lasa bane, sai ta bambance tsakanin aya da tsakuwa sai kuma ya sanyata dana sanin wannan danyen aiki data aikata. Ya lalubi dogon wando a kusa dashi ya saka, ko riga bai iya dauka ba saboda yadda yake jin jikinshi da zuciyarshi na daukar wani irin zafi.

Daddagewa yayi da duk karfinshi ya falla mata kyawawan mari har biyu a kumatu, amma bata motsa ba. Abinda ya kara bata ranshi kenan. Ya kuwa mike tsaye yayi kwallo da ita can gefe ta hadu da bango.
A gigice tayi firgigit ta tashi tana kwala ihu. Suna hada ido sai ta kara sautin ihun nata.
Ya jefa mata harara, “annamimiya wadda Allah da mala’ikunSa suka tsinewa, ni zaki tarawa jama’a bayan ta’addancin da kika aikata min?”

Aikuwa sai ta dargwaza wani sabon ihun har da dora hannu aka, tace, “Allah Ya isa tsakanina da kai Isma’il! Ka cuceni ka rabani da budurcina abin alfaharina! Wallahi ba zan taba yafe maka ba, wallahi hukuma ce kadai zata raba tsakanina da kai!!”

Ya kuwa fusata irin fusatar da bai taba yi ba, yayi kanta gadan-gadan kamar namijin zaki yana huci, ya sanya hannu ya damko wuyanta ya fara falla mata mari kashi-kashi, ihu take da Hankoron a ceceta, bakinta kuma yaki yayi shiru, zaginshi take tana aika mishi da alkaba’i iri-iri, amma a banza. Sai daya mata lilis, ya kara mata wani jina-jina din ta tafi yaraf ta zube a jikin bango kamar kayan wankin da suka gama jigewa.

Yayi tsaye a kanta yana nunata da dan yatsa, “kafin nan da cikar sakan biyar, ki tattara komatsanki ki bar nan gidan. Hukuma kuma kada ki damu, duk gidan dan iskan da zaki shiga yau sai sun tunkudoki sun kulleki a cell! Ke kinyi zaton kin ci a banza ma kenan? Ha! Lallai kina da sauran aiki!”

Bai kara cewa komi ba ya juya ya fita, bandaki ya shiga.

Sai a lokacin daya debi ruwa da niyar yin wankan tsarki sannan yaji karyewar zuciya da bacin rai wanda ba a kwatantawa ya ziyarceshi. Wata kwalla mai tsananin zafi ta zubo mishi, ya rufe bakinshi da hannunshi, yana yunkurin danne kukan dake tunkaroshi.

Abinda bai taba aikatawa ba, abinda bai taba tunanin aikatawa ba! Wai yau sai ga shi shine yake wankan tsarki a dalilin ya kusanci matar da ba tashi ba, wadda ba muharramarshi ba. Matar da baya so, kusancin da baya so!

Ai sai yaji wani zafin zuciyar yana kara lullubeshi. A zafafe ya karasa wankan, ya fita daga bandakin yana cire belt din jikin wandonshi. Niyarshi yaje ya mata bugun da kawai zai kasheta ya huta da bakin ciki. Zuwa zai yi ya nuna mata lallai shi rainin sojawa ne.

Sai yayi turus ganin dakin wayam babu kowa. Bai yi tunanin zata iya tashi ba ko motsi ganin irin bugun daya mata.

Kai ya sake jinjinawa, a ranshi yana ayyana garin Taraba ai ba bakonshi bane, ciki da waje babu inda bai sani ba. Ko cikin kwararo ko cikin kwata ko cikin rami, Allah Yasa kasa ta biyu zata shige, sai ya sa an lalubota ya mata abinda ko sunanshi aka ambata sai taji gabanta yana faduwa.

Zanen gadon da aka bata ya yaye, yana gani takaici yana kara kamashi saboda daga gani kai kasan jinin bana mutum bane kuma ba daga jikin mutum ya fita ba.

Mamakin abin kama shi yake yi matuka. Ya rasa abinda take so ta cimma da har zata aikata abu makamancin haka don kawai wani burinta can da aka gina bisa son zuciya.
Ya samu leda mai girma ya jefa zanin gadon da sauran tarkacen abubuwanta data bari, ya kulle ya jefa a kwata.

Sallah yayi, kunyar Ubangiji tana kamashi duk da yasan cewa ba laifinshi bane. Rabon daya tashi gade-gade haka ranar tana kallonshi yana kallonta da niyar wai zai yi sallar asubahi har ya manta.

Kafin kuma ya gama sallar wani irin zazzabi ya rufeshi mai zafi, da kyar ya karasa, ya ja bargo mai nauyi ya rufa amma duk da haka jikinshi bai daina rawa da karkarwa ba. Zuwa can kuma wani irin amai ya yunkuro mishi, ya kwasa da kyar ya iya kai kanshi waje, ya dinga kelaya wani irin amai ruwan dorawa shar, da kyar ya iya komawa daki.
Yinin ranar cur haka ya yini. Sai can da yamma ya samu karfin jikinshi har ya bude gida ya fita.

Kai tsaye babban asibitin garin yaje na kudi. Yana ganin likita ya mishi bayanin abinda ya faru a takaice, aune-aune ya tura aka mishi.

Sakamako ya fita da cewar kwaya ce aka zuba mishi cikin abinci ya ci mai tsananin karfi wadda ta gusar mishi da hankali. Nan aka bashi gado aka mishi allurar da zata yi flushing duk sauran abinda ke jikinshi. A takaice dai sai washegari ya bar asibitin.

Yana fita, ya dira wajen wani abokinshi, soja ne. Bataliya guda ta sojawa da karin yan sanda haka suka hada, suka shiga neman Adidat cikin wannan garin. Ya kudiri niyar batar da ita a duniya ma gabadaya daga ita har wanda yake goya mata baya wanda yasan bai wuce AbdulFatah.

Sai dai sama ko kasa, aka nemesu aka rasa. Yini guda cur suna nema amma shiru, Aisha kam koda aka tambayeta Adidat rasa abin cewa tayi. Don kuwa ta kwashe kimanin sati bata sanyata a cikin idanunta ba.

Ita yanda taga Isma’il din ma a hautsine duk ya wani firgice shi yafi daga mata hankali kan neman da yaje yana yiwa Adidat wadda tasan babu wani abu da yake a tsakaninsu.
Ta tambayeshi yafi sau nawa akan abinda yake faruwa, amma yaki fada mata, yace ta jira zata ji a hankali. Abin har ya bata haushi, ta cika ta batse, tace, “sai kaje kayi ta yi ai, zurfin ciki babu abinda zai tsinana maka sai dana sani!” ta juya abinta.

Binta yayi da kallo, kamar ya bi bayanta, sai kuma shima ya kada kanshi yayi gaba.

Kusan kwana biyu suna neman Adidat amma sama da kasa sun rasata ita da AbdulFatah din. Wanda ya gansu ma basu gani ba, don haka ya dan tsakaita da neman duk da dai bai daina ba.

Cikin wannan watan za ayi discharging dinsu, don haka yana ta shirye-shiryen komawa gida.

Itama Aisha suna ta shirin fara jarabawarsu ta karshe, wadda da alama kuma ba da Adidat za a yi ta ba don kuwa sama da kasa an nemeta an rasa kamar wata aljana.

Haka suka cigaba da lallabawa shi da Aisha din, yau dadi gobe babu. Don kuwa har lokacin shi dai ya ki sanar mata da abinda ya shiga tsakaninshi da Adidat, ita kuma ta kasa hakuri da rashin fada mata din da yayi.

A haka har ya kammala bautar kasarshi ya koma gida. Ita din ma ba za a rufa wata guda ba zata kammala, sai ayi maganar aure wanda a cewarshi sati biyu kacal za a saka.

Ranar daya koma gida a ranar suka hadu da Nuhu. Canjin daya gani a tare dashi ya bashi mamaki, ya zama babban mutum da alamun hankali da ilhama a tattare dashi. Sai a ranar Nuhun yake bashi labarin sun hadu da wata a can yar Kaduna ce, kuma sun shirya kansu har manya sun shiga zancen don kuwa aure ma watanni biyu masu zuwa za ayi.

Babanta yana aikine da CBN, kuma da taimakonshi ne ma har ya samu aiki da bankin First Bank anan Abuja din, sun bashi gidan da zai zauna, ga kuma albashinshi mai tsoka.

Isma’il ya ji dadin jin hakan sosai, don kuwa yasan wannan samun aikin da Nuhun yayi, zai tallafawa yan’uwanshi sosai da sosai.

Cikin hirarrakin da suke yi ne na yaushe gamo, ya bashi labarin duk abubuwan da suka faru tsakaninshi da Adidat. Nuhun ya jima bai yi magana ba, kafin ya kalleshi, yace, “ai ko marar hankali yasan hassada ce da kyashi da kishi a cikin al’amarin Adidat wanda ni tuntuni na gano hakan, shi yasa naga rabuwarmu shine mafi a’ala kawai duk da cewa Allah Ya gani ina sonta. Kuma wallahi wannan shirun da kaji, ka tabbatar ba na Allah da Annabi bane. Ina da tabbacin ba zata taba barin maganar nan a haka ba bayan bata kai ga cimma manufarta ba. Musamman in dai suna tare da AbdulFatah dinnan, don kuwa shine yake dorata akan komi”

Isma’il yayi shiru cikin tunani, kwarai kuwa hakane. Don kuwa da can ai ana zaune lafiya ne da ita kafin haduwarta da AbdulFatah din.

Yace, “oho, su dai suka sani. Ni dai bata isa tayi galaba da akai na ba. Duk kuma ranar data kuskura nayi arba da ita, to wallahi kashinta ya bushe!”

Nuhu yar dariya yayi, ya kalleshi, “amma dai kasan yakamata ace ka sanarwa da Aisha wannan al’amarin ko? Kaga dai aure zaku yi, bai kamata ka rufeta ba. Don kuwa nasan duk nisan kwana, watarana maganar nan sai ta fita!”

Jikin Isma’il yayi sanyi, yace, “nasan da hakan wallahi, da da yadda zanyi, zan so ace har in mutu bata ji wannan labarin ba. Amma ba yadda na iya, in Allah Ya yarda da zaran ta dawo zan fada mata komai da komai”
Nuhu yace, “yauwa, hakan dai zai fi”
Da haka suka bar maganar suka kama wata.

Yana ta dakon zuwan ranar da Aisha din zata dawo. Ranar data dawo da yamma, shi kuma ya shirya da dare da niyar ya nufi gidansu. Ya kama hanya akan mashin dinshi zai fita daga gidansu, sai yaji ana kwala mishi kira.
Ya juya yana kallon security din gidan cikin alamun tambaya, wanda ya shaida mishi cewa mahaifinshi ne yake nemanshi da gaggawa.

Cike da mamaki ya kashe mashin din ya juya suka runkufa zuwa bangaren da iyayenshi suke, kasancewar nashi bangaren daban.

Yayi sallama a nutse ya shiga, sallamar ta kakare mishi a makoshi sakamokon wadda ya gani a falon, ya zabura yayi kanta a sukwane da niyar ya damko wuyanta ya karasa aikin da bai karasa ba ranar nan… “Uban me ya kawoki nan gidan? Ko kuwa kin zo ne ki kara cutata, munafuka algunguma?”

“kai!!!”

Mahaifinshi ya daka mishi gigitacciyar tsawa data nutsar dashi a take. Mutum ne shi mai tsananin zafi da rashin daukar wasa, shi yasa ko a tasowarshi, sun fi sabawa da mahaifiyarshi nesa ba kusa ba akan mahaifin nashi.

Sai lokacin ya kula da cewa mahaifin nashi a tsaye yake kyam a falon, ya sarkafe hannuwanshi a baya yana safa da marwa, alamun an sosa mishi rai, ya kuma san abune da ran kowa sai ya baci idan takaleshi, don haka yayi ladab. Ya samu waje a gefen Ummanshi ya zauna yana jefawa Adidat harara.

Tayi wani fata-fata da ita kamar mabaraciya, kaya sun kode, fuska ta kwarmashe, idanuwanta sun shige ciki sunyi zaro-zaro, fuska zane da shatin hawaye da tunda taje gidan take zubar dasu har zuwa lokacin kuwa basu daina zuba ba.

Babanshi nuni ya mishi da ita, murya a kausashe yake tambayarshi, “kasan wannan?!”

Ya daga baki yace, “makaranta daya muka yi da ita kuma kawar Aisha ce, amma Baba…”

Katseshi yayi da wata irin murya dake hauhawa da bacin rai da fusata, “shine kuma kake binta har kayi mata ciki duk da cewa kasan kawar budurwarka ce!!”

Tunda ta fara labarinta sai a lokacin Kauthar ta iya motsin kirki, cikin wata irin rawar murya data gama dakushewa har bata iya fita daga makoshinta da dadi, tace, “kenan ni din…..!!”

Ta ma kasa karasawa sai nuna kanta da take da dan yatsa, hawaye suna cika mata ido suna barazanar zubowa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kauthar 15Kauthar 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×