Skip to content
Part 17 of 26 in the Series Kauthar by Jeeddah

Wani irin daci ya dabaibayeta, ji take kamar ta shake kanta ta mutu. Wannan bakin ciki da takaici da me yayi kama?

Wata irin kunyar kanta ta kamata, ji take yi kamar kasan wajen ta tsage ta shige ciki kawai ko ta huta.

Anty Aisha tayi gaggawar kamo hannunta ta rike cikin nata, kai ta girgiza mata,
“ba haka bane Kauthar, ba haka bane! Ki nutsu, ki saurareni da kyau. Ba abinda kike tsammani bane!”

Ranta ya dan nutsu, amma bata gama gamsuwa da kalaman Anty Aishar ba. Duk da haka sai tayi kokari ta nutsu din kamar yadda tace, ta goge hawayen fuskarta tana kallon Anty Aisha din wadda taci gaba da bayaninta.

*****

Tunda Isma’il yake, bai taba shiga tashin hankali ba kamar na ranar. Sai yaji ashe abinda yaji ranar daya tashi ya tsinceshi a kusa da Adidat din sharar fage ne kawai akan abinda yake ji a yanzu.

Ya juya da sauri yana kallonta, bakinshi ya shiga rawa da karkarwa, ya daga hannu a matukar gigice, dimaucewa da tsabar mamakin wannan al’amari suka kamashi.
Yace, “karya take yi Baba… Baba wallahi sharri take yi mun. Ta yaya..!”

“Dakata!”

Mahaifin nashi ya tsayar dashi daga maganar da yake yi a birkice, “…dakata nace malam!”, yayi shirun kamar yadda aka umarceshi, amma bai daina kallon Adidat din ba cikin tsananin mamakinta.

Babanshi yace, “ka rantse min tsakaninka da Allah cewa babu wani abu daya taba shiga tsakaninka da wannan yarinyar balle har ka hada alaka da cikin da tayi ikirarin cewa naka ne, ni kuma a yanzu a take zan koreta daga nan gidan!”

Sai ya ma rasa bakin magana, yace, “Baba wallahi… amma… Baba… tsautsayine wallahi… Wallahi Tallahi ban ma san me ya faru ba… Wallahi….!”

Adidat ta dora hannu aka ta kara dargwaza kuka, ta dukufa a gabansu tana kuka da rantse-rantse, “Baba wallahi karya yake yi, fyade ya min ba da son raina ba, kuma ya hanani magana, yace idan na fadawa wani sai ya sa an kasheni. Har sojawa ya dinga aikawa suna min kashedi, shi yasa na gudu na buya saboda tsira da raina. Bani da yadda zanyi ne, nayi barin cikin daya fara bayyana a jikina, wannan dalilin yasa iyayena suka koreni daga gida, dangina kuma babu wanda ya amsheni suna ta ala-wadai dani, ban san ya zanyi ba, bani da kowa yanzu sai Allah, sai kuwa ku! Ku bi min hakkina don Allah don Annabi!!”

Gaba daya suka kwashi salati su duka daga iyayen har dan. Isma’il ya dafe baki da hannunshi yana raba kallo tsakanin Adidat da mahaifinshi da gabadaya jikinshi ya dau tsuma alamun ya kai karshen bacin rai. Auna ta yadda zai damkota kawai yake yi, yana kuma tsoron abinda aikata hakan zai ja mishi a wajen mahaifinshi.

Babanshi ya kai gwauro ya kai mari, ya ma rasa me zai yi ya hutar da zuciyarshi, ya juya ya kai wa kayan ado da aka kawata dakin dasu kafa, suka watse a take, na fashewa ya fashe, na tsagewa ya tsage. Sai da yayi kaca-kaca da wajen sannan ya juya yana kallonshi idanu jawur.

Kowa a wajen ya sha jinin jikinshi. Ita kanta Adidat sai da jikinta yayi wani irin sanyi, ta takure a waje daya cikin rawar jiki.

Hannu yasa ya damko wuyan Isma’il ya ciwo kwalarshi, ya bashi wasu lafiyayyun maruka biyu, ya sakeshi ya zube kasa yaraf cikin rashin kwarin jiki.

Yace, “ka bani kunya Isma’il! Sakamakon da zaka min kenan? In aikaka karatu, amma kaje ka na bata yayan mutane? To wallahi kayi kadan! Kana jina? Kayi kadan ka bata min suna da martabar dana dauki shekaru ina ginata, tun ma kafin asan da wanzuwarka. Sawunka a likkafa, kafin ma kowa yaji zamu binne maganar nan. Don haka na yanke shawarar aura maka ita sai dai ka aureta a hakan!”

Ya zabura yayi wajen mahaifiyarshi a sukwane ya kama kafafunta yana ihun kuka, yace, “Ummah don Allah ki mishi magana. Wallahi bana sonta, kin dai san wadda nake so har anyi maganar aurenmu. Kuma wallahi karya take yi min, wallahi sharri take yi min!”

Babanshi ya kara fusata, ya sa hannu a aljihu ya zaro hotuna ya watsa mishi a fuska, “wani sharri kake magana anan munafuki? Ni zaka rainawa wayo Isma’il?”

Hannu na rawa ya daga hotunan, sai ya koma rigijif ya zube jikin Hajiya Hadiza wadda tunda ake abun ta kasa yin magana sai idanu da suka yi jazur cikin kunan rai da takaici da take bin kowa dashi.
Shi dinne kuwa a jikin hotunan da Adidat din, a hotuna guda biyar da aka dauka, dambe suke da ita yana kokarin cire mata kaya, ita kuma tana kokarin kare kanta.
‘Shikenan, ta faru ta kare!’
Abinda ya ayyana kenan a cikin ranshi.

Babu ma ta yadda za ayi ya wanke kanshi, saboda babu wanda zai ga hakan yace wai shirine aka yi.

Ya fashe da wani irin kuka mai cike da daci da kuna. Tunda ya girma yayi wayon kanshi, ba zai taba cewa ga ranar daya koka da idanunshi ba. Duk wani gata da jindadi na rayuwa babu irin wanda iyayenshi basu nuna mishi ba. Kasamcewarshi da daya tallin kwal da suka taba haifa, yasa suka mishi gata irin wanda ba kowane da yake samu a wajen iyayenshi ba. Bayan kasancewar mahaifin nashi mai tsananin zafi da tsayawa akan magana da akida daya, watakila da sai dai a tashi a lalace. Don kuwa Hajiya Hadiza tana matukar son danta, son da har bata iya kwabarshi idan yayi wani abun. Watakila dalili kenan da yasa ta tsani Adidat anan take, saboda ta jefa rayuwar danta cikin garari.

Ya kama kafar mahaifiyarshi yana rokonta akan ta taimaka ta ba babanshi hakuri, kada a mishi wannan auren baya so. To amma ya zata yi? Wani irin mijine Allah Ya bata wanda babu wanda ya isa ya iya tankwasa shi idan ya mike sai Allahn da Ya halicce shi. Haka suka sha wannan faman lokacin da iyayenshi na da rai ita kuma tana amarya kafin ta gama karantarshi. Akwai shi da kafiya da taurin rai. Har su iyayen nashi kuwa basu isa su sanyashi yin abinda bai yi niyya ba. Shi yasa daga baya data gama karantarshi sai ta daina dorawa kanta kan lallai sai ta sanyashi canza akala. Sai dai ta bishi da addu’a kawai.

Bata iya cewa Isma’il komi ba sai hakuri data bashi ta tashi tana kokarin boye hawayen da suka cika mata ido. Don kuwa tasan aure kamar anyi shi ne an gama tunda har ya furta.

Cikin kwana biyu kuwa rak! an gama duk wani abu da za ayi. Isma’il sai daya koma kamar wani zararre. Duk wani mutum daya san mahaifinshi na ganin girma da mutuncinshi, sai daya je ya roki alfarmar a tayashi ba babanshi hakuri, amma a banza.
Sanyi daya daya samu a wajen mahaifiyarshi shine yayi hakuri ayi auren, idan yaso daga baya idan hankula sun kwanta sai a nema mishi auren Aisha. To anan sai yaji dan sanyi.

To zancen ma bai yi nisa ba sai ga sakon Aishar ta hanyar Nuhu, tace sun rabu ita dashi rabuwa ta har abada. Don kuwa Adidat har gidansu taje ta mata cin mutunci na tashin hankali. Tace mata ai dama can tun suna makaranta yake nemanta, kuma dama yace ba auren Aishar zai yi ba saboda ita yake so. Maganganu dai marassa dadin ji har zancen cikin da yayi mata.

Bayan tafiyarta ta kira Nuhu tana fada mishi ta rabu da Isma’il don kuwa bacin rai ba ma zai barta ta iya kiranshi ba. Yayi iyaka bakin kokarinshi wajen ganin ya tausar da ita ya kuma fahimtar da ita, amma taki bari hakan ya yiwu.

Jiki a sanyaye ya isar da sakonta a wajen Isma’il. A take ya nufi gidansu, sai dai yana zuwa aka ce tana gidan Yayarta, da yaje can kuma tayi fir ta ki ya ganta.

A haka dai aka rurruma aka daura wannan kaddararren aure. Babu doki ko na anini daga bangaren ango sai na amarya.

Da yake cikin kurarren lokaci aka yi auren, a nan cikin gidansu aka ware bangaren da zasu zauna kafin ya kammala nashi ginin.

Shi kuwa mahaifinshi yayi hakanne domin gadin Adidat. Siyasarsu tana ta matsowa, ya kuma san motsi kankani yan adawa da makiyanshi suke jira su kadashi, shi yasa ma ya gaggauta yin auren saboda kada wadannan hotuna suyi kuskuren shiga hannun da bai dace ba.

Shi a karan kanshi yasan bai kyautawa Isma’il din ba, kuma kamar yadda Hajiya Hadiza tace, “idan da gaske fyaden yayi mata, me ya kaita gidanshi da dare, kuma ta yaya aka dauki hotunan idan ba sharri ba?!” ya yarda sharrin ne. Amma babu yadda ya iya don kuwa mutane ba zasu fahimci hakan ba. Yadda za ayi su kada shi kawai suke nema. A wancan lokacin babu abinda ya kai kima da martabar iyali matsayi da tsada wajen dan siyasa.

A ranar da aka kaita ya shiga dakin da aka mata masauki, babu fara’a ko dis akan fuskarshi balle ayi zancen kazar amarya a hannunshi.

Ya coge a bakin gado yana jefa mata mummunan kallo, hannu ya daga yana nunata da yar allinsa, yace, “ki bar ganin kin ci nasara kin shigo cikin gidannan kiyi tsammanin komi ya wuce. Wallahi, Adidat sai na sanyaki kinyi dana sanin aikata duk abubuwan da kika aikata a gareni. Zaman aure ko? To bismillah, ga ki ga shi, sai ki mike kafa daya, don kuwa na miki alkawarin ba zaki taba dandanar dadi da zakin aure ba!”

Ya juya ya fita a dakin. Ita kuwa ta mike tana karkade jikinta, ko kadan kashedinshi bai shigeta. Tunda dai tayi nasarar rabashi da Aisha, ta kuma yi nasarar aurenshi, ai an gama komi. Sauran abubuwan ma da sannu zasu biyo baya.

Dakinshi na da a cikin gidan, nan dai ya cigaba da kwana baya ko kallon bangaren da take. Duk wani abu daya danganceta sai dai ta aika a fada a cikin gidansu idan tana da bukatar wani abu, a kai mata. Ta so tura jikinta wajen Hajiya Hadiza, ita kuma ta ki ta bata kofar hakan. Ko taje bangarenta bata samun komi a wajenta face idan ta amsa mata gaisuwa kuma ta sanyata a gaba tana kallo, maganar duniya sai dai ta dinga binta da uhm ko uhm-uhm. Da taga babu ci sai ta koma wajen Mahaifin nashi, zuga da kara akan rashin kula lamuranta da Isma’il din baya yi babu kalan wanda bata kai mishi. Shi kuwa a lokacin da yake siyasa ta dau zafi, zabe ya gabato iyaka ya bata hakuri yace zai mishi magana. To da yake ba zaman gida bama ya cika yi, sai haduwarsu da Isma’il din tayi karanci.

A haka suka yi bikin Nuhu amarya ta tare a gidanta. Cikin ikon Allah a satin sai ga gayyatar aiki daga wajaje har biyu, daya anan Abuja daya kuma a Lagos. Babu ma zancen shawara ko tunani ya amshi tayin na Lagos din, don kuwa gabadaya garin ya mishi zafi. Aisha ta gujeshi tun karfinta, har lokacin bai gajiya ba da nemanta amma hakanshi ya kasa cimma ruwa. Bata ma yarda ko maganar fatar baki ta hadasu balle ayi zancen doguwar hira.

Ya tattara ya tafi birnin Ikko. Tunda ya tafi, bai waiwayi gida ba sai da yaci rabin shekara.

Hajiya Hadiza ce data kirashi wani lokaci cikin sanyin jiki da alamun damuwa a tattare da ita, tace, “shikenan yanzu Isma’il saboda mahaifinka ya maka abinda ba dai-dai ba sai kayi fushi har ka hada dani? Ko babu komi a matsayinmu na iyaye, mu ci daraja da Girma irin na iyayen mana! Mata da aka dauka aka baka, me yasa ba zaka yi hakuri ka yarda da kaddara ka amsheta ba? Allah kadai Yasan a inda alkhairi da albarka suke… Sannan ni meye nawa a ciki da zaka kwashe wata da watanni ba tare dana ganka ba? Anya kayi min adalci Isma’il?!”

Sai jikinshi yayi sanyi. Yaji tabbas kam bai kyauta mata ba. Idan ma da adalci, bai kamata ya dauki fushi ya dorawa ranshi akan iyayenshi ba, tunda sun cancanci ya musu wannan adalcin. Ko ba don komi ba, ko don irin so da kaunar da suka nuna mishi, yakamata ace ko dan kare suka bashi a matsayin abokin zama ya amsa da hannu biyu.

Don haka a cikin satin ya shirya ya tafi Abuja. Ba kuma wai don yana shirin karbar Adidat a matsayin mata ba, sai don iyayenshi kawai.

Irin farincikin da Hajiya Hadiza ta nuna kuwa da ganinshi sai daya sanya shi zubar da kwalla. Ya rungumeta a jikinshi yana furta ta yafe mishi don yasan ya bata mata.

Ta girgiza kai kawai taja hannunshi suka shiga bangarenta inda aka hada mishi duk wani abu na ci da sha wanda yafi so.

Mahaifinshi baya gidan, don haka ya saki jiki sosai ya ci abincinshi suna hirar yaushe gamo da mahaifiyarshi.

Yana cikin cin abincin Adidat ta shiga falon cikin shiga mai kyau da daukar hankali. Ba laifi tayi haske ta washe ba kamar da ba.

Nan da nan ya hade fuska murtuk kamar bai taba yin fara’a ba! Itama ganin ba fuska yasa ta tsaya daga gefe, ta durkusa har kan gwiyoyinta tana mishi sannu da zuwa. Ko kai da baka wajen.

Ya kalli mahaifiyarshi fuska a cune, “Ummah bari in shiga ciki in watsa ruwa in kwanta in huta.”

Fara’ar fuskarta ta dan ragu, “har ka gama cin abincin ne, ba fa ka ci da yawa ba?”
Girgiza kai yayi cikin dacin rai, “ai na koshi, sai dai zuwa anjima kam.”

Ya sabi jakarshi ya koma dakinshi na samartaka.

Itama jiki a sanyaye ta koma nata bangaren. Tana shiga ta zaro waya ta kunna, ta danno lambar AbdulFatah zuciyarta tana ta tafarfasa da kuna. Lallai-lallai sai tayi gaggawar taro bakin wannan al’amari kafin ya kwabe mata. Har ita da namiji zai nemi ya gasawa gyada a tafin hannu? Lallai yayi kadan! Zai kuma gane bambanci tsakanin aya da tsakuwa!!

Koda Alhaji Abdullahi ya dawo, lafiya lau suka gaisa har yana tambayarshi game da wajen aikinshi da abokanan aikinshi.

Ya dauko mishi zancen ya dace idan ya gama wannan tenure din tashi, ya ajiye aikin nashi ya tsunduma harkar siyasa kamar yadda yake so.

Isma’il kai kawai ya dan jinjina yana murmushi, amma tuni ya gama yankewa kanshi shawarar shi da siyasa sai dai idan ana yi a lahira.

Da dai kam, harkar tana burgeshi, kuma yana da sha’awar yi, amma yanzu da yaga irin influence din da take dashi a wajen wadanda suka dilmiya cikinta, sai yaji ma abin ya fita a ranshi sam.

Sai daya gama cin abincin dare, ya tashi da niyar tafiya daki ya kwanta. Sannan Baban ya sanar mishi an dauke kayanshi an maidasu sashenshi, ya kuma buga mishi kashedin kada ya kuskura ya sake kwana a inda ba bangaren da matarshi take ba, matukar ba bacin rai yake son gani ba.

Rai a matukar bace ya kwasa ya tafi. Ya kuwa sameta taci uwar kwalliya har ta gode Allah tana ta zuba kamshi, bai ko bi ta kanta ba bayan kallon farko daya mata, ya fada dakinshi ya manna sakata da makulli.

Wannan dalili yasa ko karasa iya adadin kwanakin daya so yi bai yi ba ya koma. Musamman da yaje gidan Nuhu ya ga yadda irin zaman mutunta juna da nuna kauna da suke yi shi da matarshi, Amina, wadda lokacin tana manne da karamin cikinta watanni hudu. Duk sai yaji komi ya dagule mishi. Tsanar Adidat ta kara shigarshi sosai.
Sai dai koda ya koma bai kara daukar wani lokacin mai tsayi bai je musu ba amma har aka dauki lokaci mai tsayi baya kula Adidat.

Tayi kwalliyar, tayi adon, tayi kwarkwasar, tayi kissar, ta koma bin malamai, ta binne laya, ta jika magani, ta dafa ta turara, duk a banza. Ko a jikin Isma’il wai an tsikari kakkausa. Ta dawo tayi magiyar, tayi ban hakurin amma a banza. Har zuwa wannan lokacin ko kurar data kwasota Isma’il baya kalla da mutunci balle ita.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kauthar 16Kauthar 18 >>

1 thought on “Kauthar 17”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×