Wani irin daci ya dabaibayeta, ji take kamar ta shake kanta ta mutu. Wannan bakin ciki da takaici da me yayi kama?
Wata irin kunyar kanta ta kamata, ji take yi kamar kasan wajen ta tsage ta shige ciki kawai ko ta huta.
Anty Aisha tayi gaggawar kamo hannunta ta rike cikin nata, kai ta girgiza mata, "ba haka bane Kauthar, ba haka bane! Ki nutsu, ki saurareni da kyau. Ba abinda kike tsammani bane!"
Ranta ya dan nutsu, amma bata gama gamsuwa da kalaman Anty Aishar ba. Duk da haka sai tayi kokari ta nutsu din kamar yadda tace. . .
Masha Allah