Anty Aisha ta sauke ajiyar numfashi a hankali, ta daga ido a karo na farko cikin mintuna masu yawa ta kalli Kauthar. Ta ci kuka har ta godewa Allah, akalla ta barnatar da kwalin tissue wajen goge hawaye da matse majina.
Ranta ya cika fal da tausayin yarinyar. Ta sani, gabadaya mutanen da take rayuwa dasu basu yi mata adalci ba musamman ita da Isma'il, bayan kuma mai dungurungum din mahaifiyarta data haifeta.
Ta tashi cikin maraicin uwa da rashin sanin kaunar mahaifiya. A maimakon su iyaye su ja ta a jiki su nuna mata kaunar data kamata kuma. . .