Skip to content
Part 20 of 26 in the Series Kauthar by Jeeddah

Anty Aisha ta sauke ajiyar numfashi a hankali, ta daga ido a karo na farko cikin mintuna masu yawa ta kalli Kauthar. Ta ci kuka har ta godewa Allah, akalla ta barnatar da kwalin tissue wajen goge hawaye da matse majina.

Ranta ya cika fal da tausayin yarinyar. Ta sani, gabadaya mutanen da take rayuwa dasu basu yi mata adalci ba musamman ita da Isma’il, bayan kuma mai dungurungum din mahaifiyarta data haifeta.

Ta tashi cikin maraicin uwa da rashin sanin kaunar mahaifiya. A maimakon su iyaye su ja ta a jiki su nuna mata kaunar data kamata kuma wadda take bukata, sai ma suka dinga yi baya da ita, suka fifita sauran uzirurrukansu a kanta.

Duk da dai Isma’il yana tutiyar cewa saboda mahaifiyarta ne da kuma yadda idan ya kalleta yake tunawa da mahaifiyarta da abubuwan da suka gudana, ya kuma fi bada karfi ga cewa kulawa tana ga ita Aisha din wadda ta fi zaman gida. Amma kowa yasan cewa hakan ba komi bane sai excuses kawai da neman kare kai. Tunda dai itama Aishar ba mazauniya bace, kasuwancinta take yi wadda ta ma fi wani namijin yawo a titunan garin Abuja da kuma kasashen waje. Tunda suma yaran nata data haifa a cikinta, Allah na tuba ta yaya ta rainesu ne? Yawanci su Kauthar din da Fahima sune suka rainesu sai kuwa yan aiki.

To su kenan ma, ina ga mahaifiyarta data tsuguna ta haifeta? Ta iya dagawa ta tafi shekara da shekaru ba tare data waiwayeta koda sau daya ba? Ita kuma tace me?!
Tun tasowarta, babu wani zabi game da rayuwarta ko freedom da suka taba bata. Karatu ma su suka zaba mata fannin da zata yi, duk da cewa dai ita Anty Aisha tayi duba da abinda tafi kwarewa a kaine ta zabar mata, amma duk da haka, ba ita ta daga baki tace musu ga abinda take so ta karanta ba. Bugu da kari ma, suka kuma kara jibga mata wani lodin na auren wanda bata so. Kodayake, ko a nan ma Anty Aishar tayi duba da zuciyar Kauthar dinne. Tunda kuwa duk duniya babu wanda ya fita sanin Kauthar din ciki da wajenta. Tasan abinda take so, tasan abinda bata so, ta san sirrin dake cikinta, ta san har abinda ita Kauthar din bata sani ba a game da kanta. Ta kuma san cewa duk duniya, babu wata halitta da take -bayan Anty Ummy- wanda ya wuce AbdulMalik. Wanda watakila ita Kauthar din bata san da hakan bama.

Aunty Aisha ta gama sanin akwai wani abu a tsakanin Kauthar din da AbdulMalik tun ma kafin su din su sani, musamman ita Kauthar din. Wanda daga fari tana mishi kallone da kauna tsantsa irinta dan’uwa, daga baya kuma ta tashi ta koma ta abokin shawara shakiki. Su dukansu basu san lokacin data tashi daga wadannan abubuwa ba ta koma so da kauna irin wanda baki ba zai iya furtawa ba.

Wanda ita a shirmen Kauthar hakan ba komi bane face girmamawa kawai da mutunci, shi yasa data fara jin canji a tattare dashi da abinda take ji a game dashi, abu na farko data fara yi shine kokarin fara ja baya dashi da kuma karyata kanta da zuciyarta. Yayinda daga gefe guda Anty Aisha take karantarsu.

Da ba don rasuwar Fahima data je musu kai tsaye ba, to da da kanta zata bukaci ayi hadin auren AbdulMalik din da Kauthar, kuma tasan ita kanta Fahima din zata yi na’am da farinciki da hakan.

Don hakane ma bayan babu ita ta sake kokarin tayar da maganar hadin auren.
Amma duk da hakan, wannan ai ba excuse bane game da yadda suka dinga tafiyar mata da rayuwa.

Muryar Kauthar ta shake, ko fita bata yi yadda za a fahimceta. Tace, “me ya faru bayan nan kuma?”

Anty Aisha tace, “Allah Yasa Isma’il yayi gaggawar sanar da yan sanda halin da ake ciki bayan ya samu sakon Adidat, ya kuma bincika an duba ba a ga Kauthar a gida ba da kuma yanayin yadda ta bar bangarenta. Kafin gari ya gama wayewa bincikensu ya kaisu ga dan karamin kauyen da hatsarin ya faru. Kasancewar sun yi nisa da gari, kafin a kai ga inda hatsarin ya faru Adidat ta riga ta tsere da abubuwan data dauka.

Mutanen da suka dauki Kauthar suka kaita dan karamin asibiti anan kauyen, su suka bada shaidar cewa lallai wata mota da take bin bayan daya motar da tayi hatsari, ita ta tsaya ta dauki matukin motar da akwatu a bayan motar. Wannan daliline yasa suka yi zaton ko yan satar mutane ne, amma kuma kafin su kai tuni motar tayi nisa, dole suka tsaya ceton yarinyar.

Kauthar kam ta samu matsala, duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata. A take suka dauketa aka maidata babban asibitin kudi anan Abuja. Ga karaya, ga raunuka, ga rashin kunne.

A satika biyu da suka biyo baya, bata ma san inda kanta yake ba. Duk wani waje da kokarin tunbudo inda Adidat take a cikin Nigeria, anyi amma babu nasara. Daga karshe ma aka tabbatar musu da cewa tuni ta haura kasar Togo ita da mutumin da aka tabbatar da AbdulFatah ne…”

Anty Aisha ta kalli Kauthar, “sauran abubuwan da suka biyo baya kuma kin sani. Aurena da Isma’il da tafiyar Umma Hadiza Makkah wanda daga nan ta koma can da zama ma, tarewarmu da komawar Faheema hannuna da zama”

Ta gyada kai, zuwa lokacin tuni hawayen fuskarta sun kafe. Zuciyarta tayi mata wani irin nauyi da tauri irin wanda bata taba ji ba.

Uwar data tsuguna ma ta haifeta, wadda ta dauki cikinta wata tara, ta yi nakudarta, ta raineta, ta gujeta dare daya ba tare data taba waiwayarta ba, to ina ga mutanen da basu san zafinta ba? Anya a duniya akwai sauran mai sonta ma kuwa? Duk da hakan, sai data kara tambayar Anty Aisha,

“yanzu tana ina?”

Ta muskuta ta gyara zama, “tana Keffi, acan take da zama. Amma Kauthar, kiyi hakuri da abinda zan fada miki, bincikenan cikin sirri nayi shi saboda ke. Bana so mahaifinki ko wani ya sani. Saboda…”

Sai kuma tayi shiru tana kallonta. Kauthar ta kalleta, tuni zuciyarta ta gama dakewa, bata tunanin kuma akwai sauran wani abu da zai kara bata mamaki game da Adidat. Ya wuce guduwar da tayi ta barta a halin mutuwa da rayuwa?

Anty Aisha ta nisa, “sai bayan tafiyar Adidat din ne Isma’il ya samu labarin ashe ita da AbdulFatah sun nemi bashi a bankin da Nuhu yake aiki, miliyoyin kudi suka amsa kuma suka sanyashi as their guarantor.”

Kauthar ta dafe kirjinta da take ji yana wani irin luguden daka cikin tsananin tashin hankali. Ashe abinda take ji game da Adidat ba kome bane. Lallai wannan mata ta wuce duk inda mutum yake tsammaninta!

Murya na rawa tace, “kenan… hakan yana nufin Baban AbdulMalik shi ya biya kudin data ara?”

Ta jinjina kai a hankali, “shi da Isma’il, yes. Su biyun suka biya, in kuma zauna ina fada miki wahalar da suka sha wajen biyan kudin nan ma bata baki ne. To gaskiya abinda ya kara bata ran Isma’il ma kenan. Har a yanzu kuma nasan yana neman dalilin da zai hada shi da ita. Don haka ban san me zai faru ba idan yasan da cewa kin nemeta da kanki, abinda yake ta kokarin hanawa”

Kwalla ta cika mata idanu. Sai lokacin ta iya furta tambayar data jima tana mata yawo a kai, “kenan, saboda abinda Mahaifiyata ta aikata mishi, shi yasa ni yake hukuntani da laifinta? Bai taba daga ido ya kalleni da sunan so ko kauna da tausayawa irin ta d’a da mahaifi ba? Hajiya Hadiza ma har take kasa boye kiyayyata a yawancin lokuta? Duk akan laifin da bani da hannu akan shi?!”

Anty Aisha ta daga baki zata yi magana, tayi saurin katse ta ta hanyar daga mata hannu tana girgiza kai, tana so ma tayi magana amma ta kasa. Don haka kawai ta lallaba ta tashi akan kafafunta da suka dauketa da kyar, ta shige dakinta ta kulle.

Ranar tayi kuka irin wanda bata taba yi ba a rayuwarta. Bata taba jin she’s worthless ba sai a lokacin. To mutum duk kyawunshi da kudinshi, matukar mahaifiyar data haifeshi bata sonshi, ai bashi da wani alfanu.

Tana jin wayarta tana vibrating alamun ana kiranta. Data gaji da vibration din ta daga da niyar kashewa, sai taci karo da tarin missed calls da text messages daga AbdulMalik rututu, sai kuma na Anty Aisha da su Lukman.

Bata san me ya kamata tayi ba. A irin wannan lokacin ne take matukar bukatar Anty Ummy. Saboda ita zata bata shawara akan abinda yakamata tayi da yadda zata fuskanci al’amarin.

Sai ta kara jin komi ya rincabe mata, data tuna yanzu tunda babu Anty Ummy lallai ita kadai ta rage anan duniyar.

Kamar wanda ya shiga cikin ranta, taji vibrating alamun shigar sako, tana dubawa taga AbdulMalik ne dai, *’you are not alone Kauthar, I’m and always will be with you. Don Allah ki bude kofa ko ki amsa kirana!*’

Wasu hawayen suka zubo mata sharr! Kawai sai ta kashe wayar tayi jifa da ita.
Ta koma ta kwanta lamo, kamar mara laka, koda yake ba lakar take da ita ba.
Ta dauki lokaci mai tsayi tana ta saka da warwara. Daga karshe dai ta koma jan hailala da istigfari a cikin ranta. A haka barci yayi awon gaba da ita.

Taso ta ji alamun shigar mutum cikin dakin, har aka ja comforter aka kara saya mata jiki, da kuma jin tattausan kamshin nan da bata taba mantawa. Sai kuma jin alamun saukar tausasan lebuka a saman goshinta, da kumatunta da kuma lebukanta.

Ta tashi zaune tana ganin lokaci, karfe biyar ta kusa, lallai ba karamin barci ta shaka ba. Duk da dai bata yi mamakin hakan ba saboda a daren jiyan ba wani barci tayi ba na azo a gani, kuma taji dadin yin barcin yanzu, ko babu komi taji kanta ya dan warware da kuma jikinta. Gajiya da nauyin da suka mata rubdugu duk sun ragu.

Tayi shiru tana kallon abin rufa mai taushi da aka rufe mata jiki dashi, bayan ita kuma tasan bata rufa da komi ba. Sai ta dinga tuno abubuwan data ji lokacin da take a barci. Ga sauran kamshinshi nan, wannan unique and masculine kamshi wanda baya bacewa, har lokacin yana lingering akan fatar jikinta inda ya taba. Wasu cunkusassun abubuwa suka dinga mata yawo a cikin cikinta. Alamun kenan ya samu ya bude dakin ya shiga lokacin da take barci.

Sauka tayi daga kan gadon, ta fada bayi. Wanka tayi da ruwa mai dumi wanda ya kara sanyawa taji karfin jikinta.

Ta fito tana goge jikinta da karamin tawul. Kaya ta saka marasa nauyi, tayi sallah. Zama tayi akan abin sallar tana jan carbi har aka yi magriba.

Ba ita ta fita daga dakin ba sai bayan da aka yi isha’i. Shima ba a son ranta ba sai don kugin da cikinta yake mata, da kuma su Mahmoud da Lukman da suka dameta da bugun kofa suna kiran sunanta.

Gabadaya kunyar kanta da ta su Anty Aisha take ji, ji take yi kamar kawai kasa ta tsage ta shige ciki ta huta. Idan ta tuna mahaifiyarta, uwa a gareta, da irin abubuwan data aikata ga su Anty Aisha da AbdulMalik, sai taji kamar kawai ta kalli gabas tayi ta gudu har sai tayi nisa dasu.

Haka nan dai ta daure ta dake, ta fita bayan ta kora paracetamol saboda taji kanta ya kara daukar zafi, ga jikinta da shima yake kokarin daukar wani zazzabin.

Su dukansu suna zaune akan dinning, hira suke yi akai-akai. Anty Aisha tana ta fama da waya da lissafi kamar yadda ta saba, su Lukman kuma suna magana da AbdulMalik. Duk suka dakata da abinda suke yi suna kallonta. Anty Aisha ta ajiye waya, AbdulMalik yayi gefe da plate din fruit salad dake gabanshi, Mahmoud kuma ya sauka da sauri daga kan kujera ya tareta. Rungumeta yayi, ta rungumeshi itama, saboda a hakikanin gaskiya ita ce, tana bukatar comfort a wannan lokacin.

Yace, “Addah ina kika shiga, ina ta nemanki?”

Ta shafa kanshi tana murmushi, “sorry Mudi, kaina yake ciwo sai na sha magani na kwanta.”

Ya turo baki, “Adda ni dai ki daina ce min Mudi Allah bana so!”

Yar dariya tayi tana jan kujera a tsakanin AbdulMalik da Lukman ta zauna. Lukman ya mika mata hannu suka yi musabiha, shima kallon Mahmoud yake, yace, “sunanka kenan ai Mudi, shi yafi dacewa da kai saboda kai acici ne, ko Adda?”

Ya tambayi Kauthar, ta gyada kai tana murmushi, “kwarai kuwa Luku-luku”
Shima ya tabe baki yana yatsina fuska. Su duka saki yar dariya.

AbdulMalik ya tura mata plate din abinci gabanta dana fruit da kuma zobo da aka hada, ta kalleshi kawai ta danyi murmushi ba tare data ce wani abu.

Ta kara daga kai ta kalli Anty Aisha, itama kallonta take yi fuska cike da alamun tambaya. Ta dan jinjina kai kawai, ta dauki cokali ta fara cin abinci.

Lukman da Mahmoud su suka sanyata gaba da hirararraki iri-iri, nan da nan ta ware, suka hau hirarsu cikin annashuwa har bata san lokacin data cinye plate guda na abinci ba.

AbdulMalik da wuri ya musu sallama ya shige daki. Su Lukman ma da wuri suka kwanta saboda a washegari zasu koma Abuja. Ita Kauthar dai ta musu alkawarin next weekend zata je musu hutu.

Ta koma dakinta tayi shirin barci cikin kayan barci riga da wando masu kauri da taushi, saboda jin sanyi yana dan kadata.

Anty Aisha tana zaune kan kujerar gaban madubi tana waya da Alhaji Isma’il, Kauthar ta tura kofar ta shiga.

Ta bita da kallo tana cigaba da wayarta har ta zauna a gefen gado. Itama shiru tayi tana sauraren wayar tasu, mafi akasarinta game da kasuwancinsu ne da calculation na yadda za a mayar da kwabo ta koma kwandala. Kauthar ta tabe baki a ranta tana gulmar irin wannan rayuwa ta iyayen nata. Kafin a tambayi juna ya aka tashi da yadda aka yini, sai an fara tambayar nawa ta shigo kuma nawa ta fita? Ita fa bata tunanin zata iya yin irin wannan rayuwar auren. To ma menene zaman auren idan ma’aurata basu tattali juna ba suka kuma kula da juna? Kodayake dai gwara ma nasu auren akan wani auren sau dubu.

Sun dan jima suna wayar har sai data fara gajiya, musamman da hirar tasu ta fara komawa personal kuma. Ta zame aid dinta daga kunne ta yadda bata jin maganar tasu sai sama-sama, ta fara dan susar kunnen cikin kosawa, har ta fara tunanin kawai ta tashi ta tafi washegari sai su hadu. Sai kuma taga ta kashe wayar ta ajiye gefenta. Don haka ta maidashi ta makala a kunnen nata.

Ta juya ta kalli Kauthar din tana dan murmushi, “ya aka yi ne Kauthar?”

Duk yadda taso ta maida mata martanin murmushin kasawa tayi, babu wani sabo da sakewa a tsakaninsu, musamman a yanzu data kara sanin muhimman abubuwan da a da bata sani ba.

Tace, “ina so ki fada min a inda zan samu mahaifiyata, ina so in ganta!”

Anty Aisha shiru tayi tana kallonta. Tasan zuwan Kauthar wajen mahaifiyarta is inevitable, amma abin tambayar anan shine, ita Kauthar din da Adidat, are they ready? Kuma wane irin outcome haduwar tasu zata kawo?

Tana so ta hanata, saboda tsakaninta da Allah, har cikin ranta, tana tsoron abinda hakan zai haifarwa Kauthar. What if Adidat din bata yi maraba da ita ba? What if bata bukatar Kauthar din a rayuwarta, duba da irin shekarun da aka dauka amma koda wasa bata taba waiwayarta ba? Bata son Kauthar ta kara fuskantar shariya da rashin so daga mahaifiyarta a karo na biyu. Don kuwa tasan hakan zai matukar bugunta ba kadan ba. Sai dai duk yadda taso ta kare Kauthar daga wannan, ba zata iya ba. Tunda duk daren dadewa, dole zata nemeta in one way or another. Kuma ba a canzawa tuwo suna. Watakila da ana hakan, da tuni ta canzawa Kauthar mahaifiyarta, don kuwa bata cancanceta ba sam.

A sanyaye tace, “me zai hana ba zaki bari muje tare ba ni da ke?”

Kai ta girgiza, “no, nagode. Amma ina so in yi wannan abun ni kadai, ba tare da tallafawar wani ba. Ko babu komi, mahaifiyata ce ai!”

Anty Aisha ta gyada kai, “haka ne Kauthar, haka ne. Amma don Allah ina rokonki Kauthar, koma me zai faru, kiyi hakuri, ki kuma sanya a ranki cewa duk rintsi, muna tare dake a koda yaushe, kuma muna sonki!”

Ganin wasu hawayen na barazanar sake zubo mata yasa ta kawar da kanta gefe daya. Da gasken duk rintsi suna tare da ita, tunda su din su suka cigaba da zama da ita bayan mahaifiyarta ta yakitar da ita, ta nunawa kowa karara cewa bata sonta. Har ma suka dinga kokarin boye mata gudun irin bacin ran da zata ji ta dalilin haka.

Rai a matukar jagule ta yiwa Anty Aisha sai da safe. Saboda tunawa da dimbin halacci da matar da danginta suka yi mata. Hakika ita din ta daban ce, ta kuma san ba lallai kowace irin mace bace zata iya aikata hakan, ciki kuwa har da Adidat.

Ta riketa kamar yadda ta riki yayan cikinta, haka daidai da rana daya, bata taba daga ido ko baki ta furta wani abu game da rashin da’a da Kauthar din ta dinga aikatawa a gareta ba. Idan ta tuna rayuwarta dalla-dalla tun daga farko, sai taga me ma Anty Aisha din ta taba aikatawa a gareta mummuna? Ko mutum yaki Allah da manzonSa, ba zai ce ga wani abun ki data taba nufar Kauthar din dashi ba.

Cikin wannan tunani da zullumi ta koma dakinta. Ta kashe wuta ta hau gado tayi addu’ar barci. Sai data kwanta, har barci yaso ya fara surarta, sannan ta tuna da alkawarin data daukarwa Anty Aisha. Ta bude idanun tar cikin duhun dakin, tana barar-rabi a cikin ranta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kauthar 19Kauthar 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×