Kamar wata barauniya, haka ta bude kofar dakin. Kai ta zura a hankali, a ranta tana addu'ar Allah Yasa ya riga yayi barci yadda zata sadada ta kwanta ba tare daya san da zuwanta ba.
Cikin rashin sa'a sai suka hada ido dashi. Zaune yake akan kujera yana sipping din green tea, da jarida a hannunshi yana karantawa. Ya daga kai yana kallonta.
Bata da zabi wanda ya wuce ta karasa jan jikinta ta shiga dakin tare da maida kofar ta rufe.
Ta ki yarda su hada ido dashi. Ta taka a hankali kamar mai tsoron taka kasa. . .