Skip to content
Part 25 of 26 in the Series Kauthar by Hauwau Shafiu (Jeeddah)

Sai bayan sallar isha’i sannan AbdulMalik yaje ya dauketa suka karasa gidansu AbdulMalik din inda anan aka musu masauki a bangaren daya saba sauka idan yaje Abuja.

Anna, mahaifiyarshi, da su Na’imah sun taresu tarba ta karramawa sosai da sosai.

Liyafa guda aka hada musu ta abinci har sai da suka rasa me ma zasu ci. To da yake kamar sun sani dama basu ci abinci ba sosai acan gida, don haka suka saki jiki da ciki sosai suka kwashi garar abinci kamar ba gobe.

Ba wani sani na azo a gani ba ta yiwa Anna, tunda ko a lokacin da aka yi auren Anty Ummy da AbdulMalik ba kasafai suka dinga zuwa gidan ba. Kuma duk da cewa Anna din tana shiga cikin danginsu musamman idan wata sabga ta tashi, ita dai Kauthar bata shiga jikinta ba sam. Amma a dan zaman da suka yi a lokacin ta gama fahimtarta macece mai matukar kamewa da rashin sa ido akan al’amuran mutane kwarai da gaske. Ko zaman cin abinci da suka yi, tana daga can kan kujerar hutu da daga gani musamman aka kirkirar mata ita, da carbi a hannunta tana ja.

Yayinda su kuma suke sama kan teburin cin abinci.

Akwai alamun shakuwa sosai a tsakaninta da ‘ya’yanta wanda har hakan yasa suka mayar da ita kamar kakarsu, tunda duk hirar da za suke yi zaka ji suna yawan sakota a ciki, ko kaji ance, “ko Anna?” ko kuma su ce, “ko ba haka aka yi ba Annarmu?” amma fa cikin girmamawa da taka-tsan-tsan.

Wani lokacin tayi yar dariya ta amsa musu, wani lokacin kuma ta kwabesu.

Kauthar kam ta jinjina mata matuka gaskiya, yadda ta iya rainon ya’yanta suka tashi da kusanci da zumunci da kuma mutunta juna. Saboda daga ganinsu su duka babu tambaya kasan su din tsintsiya ce madaurinki daya.

Basu zauna zaman hira ba tace su Na’imah su rakasu inda zasu zauna saboda alamun gajiya daya baibaye Kauthar din, zuwa lokacin ko ido bata iya budewa sosai.

Inda aka kaisu part ne guda, kuma well furnished da duk wani tarkace da zasu bukata. Dama tun da zasu taho ma ce mata yayi ba sai ta tafi da komi ba na amfani, tunda akwai a can.

Suna shiga kuwa wanka tayi da ruwa mai dumi, ta lalubi kayan barci marasa nauyi ta zura ta lalubi gado ta zube.

Yana daga zaune yana kallonta ganin yadda tayin, wato dai a takaice tana fada mishi kada ya takurata kenan. Kai kawai ya girgiza yana murmushi shima ya tashi yayi abinda zai yi ya bi bayanta.

Washegari ma koda suka yi sallah komawa barcin tayi, ranar ko azkar din safen ma da kyar ta karasa shi. Wani irin masifaffen barci da gajiya ne suka tarar mata, ji take yi kamar ma bata yi barci ba.

Shi kuwa da bai koma barci ba, gari yana yin haske bangaren su Anna ya wuce ya gaisheta. Nan ya zauna wajenta suna tattaunawa game da abubuwan da suka dangancesu, ita kuma tana kara nusar dashi game da rayuwar aure da muhimmancin hakuri da kyautatawa iyali, kamar yadda ta saba.

Su Umaimah ma anan suka sameshi suka gaidashi. Ya amsa musu cike da nuna kauna. Suma zama suka yi aka cigaba da hirar dasu, mai matsala kuma da bukatar wani abu ta fada mishi.

Ba shi ya koma wajen Kauthar ba sai wajen karfe tara, amma duk da haka barcin dai ya tararta tana yi. Ya jinjina kai cike da mamaki, da alama dai ta kwashi gajiya da yawa ne kenan.

Sai da yayi wanka ya sanya yadi mai kyau ruwan madara da hular zanna baka, sannan ne ya tasheta.

Ta tashi tana mika, har lokacin jikinta a mace yake murus. Sai da tayi wanka da ruwa mai dan zafi sannan ne taji karfin jikinta.

Su biyun suka rankaya zuwa bangarensu Anna. Ta durkusa har kasa tana gaidata, mace mai dattako da fara’a, koda yaushe zaka samu fuskarta cike da fara’a da murmushi. Ta amsa mata a tausashe.

Ranar kam kin hawa kan teburi tayi saboda cewa tayi takura mata yake yi, ta mike kafa anan tsakiyar falo tana cin gurasa wadda Anna din da kanta tayi, ga kuma hadadden bakin shayi da ya sha kayan kamshi, su kuma su Na’imah suna kan teburin.

Bayan sun gama cin abincin AbdulMalik ya fita, ita kuma suka zauna ita da su Na’imah suna ta hirarsu har su Lukman suka je, nan ta kara shantakewa suna shan hira.

Yini guda cur suna ta hirarsu abinsu, ko nan da can bata zuwa, ko abu zata bukata sai dai su ce ta fada su dauko mata. Haka suka yini suna ta yan ciye-ciyensu, da rana ma da aka gama abinci sai bata ci ba, sai sauran gurasar da aka yi da safe ta kara ci.

Sai dare aka je aka dauki su Lukman, har lokacin kuma AbdulMalik bai dawo ba.
Sai can wajen karfe tara na dare, lokacin su duka suna falo bayan sun gama cin abinci. Tana zaune a kasan kafet ta mike kafafunta, ta dora kanta a tsakanin kujerar da su Umaimah da Na’imah suke zaune. Kallo suke yi, amma ita rabi barci take yi rabi kallo.

Ya zauna a kujerar dake fuskantarsu yana cire hular kanshi ya ajiye akan hannun kujerar, idanunshi kur a kanta cike da alamun tambaya.

Yace, “baby girl ya dai, ko duk gajiyar ce har yanzu?”

Kai kawai ta iya kada mishi a kasalance. Yayinda Umaimah ta fara mishi tayin abinci, kai kawai ya girgiza, “a koshe nake sosai, naci abinci gidansu Jameel. Amma dai idan akwai yoghurt mai sanyi samo mana sai mu shiga dashi.”

Ta mike tsaye, “to watakila ko Anty Kauthar ta iya shan yoghurt din, don kuwa bata iya cin abinci da yawa ba yau.”

Jin abinda tace yasa ya kalleta fuska dauke da alamun tambaya, ita kam kai kawai ta girgiza mishi kamar taji tambayar ‘me yasa’ din da yake yi a cikin ranshi. Haka kawai sai taji gabadaya komi ma ya fita a kanta.

Sai da suka yiwa Anna sai da safe kafin suka wuce bangarensu.

Bayan sun gama shirin barci ya tsiyaya yoghurt a cikin kofi ya mika mata ganin tana shirin mikewa akan gado, kofin ta kalla tana dan girgiza kai, “a koshe nake fa!”
Yace, “me kika ci to? Umaimah fa tace baki ci komi ba.”

Tace, “fada kawai take yi, amma na sha kankana sosai da mangwaro. Kuma na sha sauran kulin da aka ci gurasa dashi dazu!”

Yace, “to kuma ce miki aka yi kankana da mangwaro abinci ne? Balle ma kuma kuli? Yaushe kika ma fara cin kuli ne?”

Ta daga kafada kawai. Samu yayi da kyar dai da lallashi ta sha yoghurt din sosai sannan suka kwanta.

Washegari ma haka ta tashi sam babu wani kuzari a jikinta ko kadan. Haka duk tarin abincin da aka hada musu na kari kasa ci tayi, sai masa data samu ta dangwale da kuli.

Sai ranar suka fita gari suka zagaya sosai. Ya kaita gidan abokanshi da ‘yan’uwanshi da yawa.

Sun je gidan wata cousin dinshi, matar abokinshi kuma, Hafiza, sun jima a gidan suna hira kuma hankalinta ya nutsa da halin Hafiza din sosai. Da zasu tafi haka ta cikata da tsarabar turaren kamshi da spices na girki.

Suna tafiya a mota inda zasu karasa gidansu Kauthar din, ya juya yana tambayarta, “kinga Hafiza dinnan?”

Ta gyada kai tana kallonshi, yace, “to ita ce wadda kike zargina da ita.”

Ta yamutse fuska cikin rashin fahimtar inda zancen nashi yasa gaba, “ban gane ba?”
Yace, “itace wadda kika ganni rungume da ita a makarantarku shekarun baya da suka wuce, kike zargin ko ina bibiyar mata ne!”

Sai tayi kasa da kanta cike da kunya da tozarcin abinda ta mishi. Shi kuwa yayi dan murmushi, “idan ban manta ba a lokacin, na isar mata da sakone mai karya zuciya sosai, ita cousin dina ce, kuma budurwar abokina sosai wanda yake soja ne. An aikasu wani aiki aka harbeshi wanda kuma a lokacin ma anyi zaton babu shi ya rasu, cikin rashin sa’a kafin wani a gida yayi tunanin ta yadda zai sanar da ita har an samu wasu daga cikin abokanshi sun sanar da ita. Ta kirani tana kuka, don haka naje na sameta. I was just offering comfort to her a lokacin, wanda nasan cewa ba abinda ya kamata ba kenan. Amma abinda ya wuce ya riga daya wuce, babu zancen dawowa baya.”

Bata iya cewa komi ba sai juya mishi kai da tayi har a lokacin cike da kunyarshi. Duk da cewa dai ko babu komi taji dadin bayanin daya mata, don kuwa har a lokacin zuciyarta bata daina tunanin wannan din ko wacece ba? Amma bada wata manufa ba sai ta son sani kawai, don kuwa ta yarda da mijinta dari bisa dari.

Ya kalleta fuskarshi dauke da murmushin tsokana, “su yar ware masu kishin son mutum amma kuma ana kin nuna mishi saboda tsabar jindadi!

Ai ban san son nawa da kike yi ya kai har haka ba. Wannan ai shine ana so ana kaiwa kasuwa din!”

Ta jefa mishi harara cikin wasa tana turo baki, “ni a ina nace maka wai ina kishinka?”

Yayi dariya sosai har yana dukan sitiyari, “ko da baki fada ba ai na ga hakan zane baro-baro a cikin kwayar idanunki. Kuma ai kinji dai hausawa cewa suka yi wai labarin zuciya a tambayi fuska!”

Tace, “uhmm! Kai dai kawai kace duk abinda kake son fada kawai, amma nasan ba haka bane!”

Hannunta ya kama ya jimke a cikin nashi, “to idan hakan ne ma sai ya? Don kinyi kishin mijinki wa ya isa yace miki kin aikata ba daidai ba? Sai dai ma in kara da fada miki ki kwantar da hankalinki kawai, In Allah Ya so, AbdulMalik dai na Kauthar ne. Ni da ke ai mutu ka raba ne, ko ban fada miki ba dama can Allah Ya kadartomu a matsayin ma’aurata bane? And it’s forever in shaa Allah!”

Ya kai hannunta saitin bakinshi yana sumbata, “ba zan taba iya imagining kasancewa a ko’ina in ba anan ba, tare da ke Kauthar!”

Har suka karasa gida jikinta a mace yake da jin kalamanshi.

*****

Satinsu daya cur a Abuja kafin suka koma Lagos. Kafin su tafi take neman shawarar Anty Aisha akan abinda ya kamata tayi da dukiyarta. Tace mata ita kam me zata ce mata? Amma idan tana ganin zata iya irin kasuwancinsu taje suyi, kai tsaye ma ce mata tayi a’ah. Saboda ita dai zaman auren take so tayi gabadayanshi, bata son abinda zai dinga nesantata da mijinta da iyalanta. Don haka sai ta bata shawarar zata iya bude mall nata na kanta, in yaso ta samu wanda zai dinga managing yana kula mata da komi. Da wannan shawarar suka rabu.

Shiri ya fara musu ba tare da saninta ba na zuwa yawon zaga kasashen duniya bude ido kafin daga karshe su dira a garin Makkah.

Sai kuma in between ga kyautar da basu taba tsammani ba daga Azzah wa Jal.
Rana guda ta tashi da zazzabi da amai daya jigatar da ita sosai. Awon farko ma likita cikin wata biyu ya gani.

Wayyo, zo kaga murna da doki wajen AbdulMalik. Ya rasa inda zai tsomata a cikin ranshi yaji sauki.

Tattali na duniya dai babu wanda bata gani ba, kuma Alhamdulillah cikin yaje mata da sauki sosai, babu laulayi da tsarabe-tsarabe irin na masu ciki. Sai ciwon mara kadan-kadan wanda likitan yace hakan ba komi bane, kuma zai daina a hankali.

Su biyun sun raini cikinsu cikin tsananin tattali da kulawa.

Tana shiga watan haihuwa kuwa Anty Aisha da kanta taje ta dauketa zuwa gida. Inda taje ta samu Hajiya Hadiza itama taje. Nan suka cigaba da kulawa da ita, ga Anna itama kusan kodayaushe tana tafe ko kuma aiken tuwonta wanda Kauthar din take ci da gurasa, suna tafe.

Ranar litinin da dare har sun kwanta ita da Hajiya Hadiza da yake bangarenta ta koma da zama, nakuda ta tashi kamar gaske, suka kwasa suka yi asibiti a sukwane.

Abu kamar wasa nakuda ta ki ci ta ki cinyewa, sai ta taso gadan-gadan sai ta koma. Haka har gari ya waye, uban gayyar yazo aka dora dashi.

Ana shawarar ko ayi aiki wajen karfe goma na safe dai Allah Ya saukaka, ta haifi lafiyayyar diyarta mace tubarkallah da ita.

Sai da likita ya basu awa suka kara hutawa saboda wahalar da ta sha kafin ya bada umarnin wadanda suka yi dandazo a kofar dakin su shiga.

Wajenta ya nufa kai tsaye, ya cukuikuyeta da yar diyar dake gefenta su duka yana sa musu albarka kamar bakinshi zai tsinke.

Bayan likita ya gama tabbatar da su dukansu ita da baby lafiya lau, ya sallamesu suka koma gida.

Bayan an gama shirya musu inda zasu zauna, sun nutsu ita da baby. Yana like dasu ya ki matsawa ko nan da can, dashi aka yi komi. Lokacin duk an fita an barsu su kara hutawa, ita tana kwance akan gado, shi kuwa yana gefen gadon rungume da baby a kirjinshi, ya kasa rabuwa da ita ko nan da can.

Ya kalleta a tausashe, wani so da kaunarta da girmanta ne yake karuwa a cikin ranshi sosai da sosai, yace, “wane suna kika bawa baby ne?”

Ta kalleshi da idanu kasa-kasa, “Anty Ummy ce!”

Sai yayi dan murmushi, ya kara bakinshi a kunnenta ya fara yi mata huduba.

Lokacin daya daga idanu fuskarshi dauke da wani irin murmushi, idanunshi suna sheki ne na hawaye, sai taji itama zuciyarta tana kokarin karyewa.

Murya a tausashe yake kallon jaririyar yana mata magana, “Allah Ya rayaki Fahima! Allah Ya baki ikon dauko halayen mai sunanki. Allah Ya hadamu daku, da ita, da iyayenmu, da al’ummar musulmi a gidan AljannarShi Madaukakiya!!”

Kauthar tace, “ameen ameen.”

Anty Aisha ta shigo dakin, Hajiya Babba mahaifiyarta na tafe a bayanta, hannu riki-riki da manyan ledoji masu dauke da tambarin wani shahararren shagon sayar da kayan jarirai.

Ta zauna tana jerawa Kauthar ruwan sannu, wadda haka kawai sai taji wata irin kwalla tana kwararar mata a cikin idanu.

AbdulMalik ya tashi tsaye tare da mika mata yarinyar, ya kalli Anty Aisha yana dan murmushi a kunyace, har lokacin kallon suruka yake yi mata, yace, “Anty, ga Fahima!”
Baiwar Allah ta rasa me zata yi, sai suka hade kai ita da Hajiya Babba suka hau kukan farinciki. Kauthar ya kalla da itama take kokarin dargwajewa da kukan, yana girgiza mata kai alamun a’ah. Shigar Hajiya Hadiza dakin dauke da kofin kunun tsamiya da aka damawa maijegon yasa ya sudada ya fita daga dakin. Don ita dai ba waigi gareta ba, korarshi zata yi bayan ta kare mishi tatas.

Ita ta samu ta rarrashi su Anty Aisha din. Bayan sun nutsa, ta zubawa Kauthar kunun ta mika mata ta shanye. Tana gamawa ta koma tayi kwanciyarta ta hau barci.

Adidat da yan uwanta tun a washegari suka dira, aka ware musu bangare guda inda suka cigaba da kulawa da maijego da jinjirarta har zuwa ranar da aka yi suna.

Bayan dangi na nesa dana kusa sun tafi, nan suka fara ainihin wankan jego na gargajiya, Hajiya Hadiza ce tsaye a kanta kyam don haka duk da yadda bata son wankan tawul, sai ta takurata tayi.

Ta kan ce mata, ‘gata ne nake miki wallahi, ba kuma zaki san da hakan ba sai kinyi haihuwa uku ko hudu kin dinga jinki dakau kamar wata yar budurwa sannan. Wannan wankan ai shine martabarki’

Anty Aisha kuma ita ce gyaran ciki da waje. Shi yasa kafin suyi arba’in, sunyi wani irin fari da kyau ita da babyn, jikinsu ya murmure sosai da sosai. In ka gansu kamar ka daukesu ka gudu.

Suna yin arba’in Anty Aisha da Hajiya Hadiza suka mayar da ita gidanta, mijinta ya amshesu da hannu biyu cike kuma da doki.

Bata tunanin akwai wata ‘ya mace data taba ganin tattali da tsantsar so da kulawa daga wani d’a namiji kamar yadda AbdulMalik yake nuna mata a wannan lokacin ita da d’iyarta. Wane lokacin da suke ganiyar cin amaryacinsu? Wannan ai ya ninkashi ya kara.

Of course, akwai ups and downs na rayuwa, wadda dama ita ta gaji haka, kuma wani matakine ma na kara fahimtar juna da son juna. To dukansu sun fahimci junansu, da suka yi hakan kuma sai suke kiyaye bacin ran junansu, da haka sai komi yake zuwar musu a saukake.

A wani lokaci can bayan yan shekaru, jin kunnenta daya ya dauke gabadaya, ko da hearing aids dinta baya aiki, sai guda yake functioning. Hakan bai daga mata hankali ba kamar yadda tayi tunanin zai yi a baya. Domin kuwa tana tare da mutanen da suma hakan bai damesu ba. Kuma a garesu hakan ba tawaya bace face kaddara, wadda ta kara shaping dinta zuwa more matured mutum, wadda tasan mutuncin kanta dana ahalinta. Kuma tana da tabbacin koda nan gaba jin nata ya dauke gabadaya, babu abinda zai ragu na kulawar da suke mata sai dai ma ya karu.

Rayuwa tayi mata wani irin juyi wanda bata taba tsammani ba, amma fa juyi na alkhairi.

Ta samu kaunar uwa a wajen matar data tsana a da, ta kuma samu kaunar mahaifiyar data haifeta.

Ta samu miji na kerewa sa’a, wanda yake bata duk wani abu da mata take bukata a wajen mijinta har ma ya kara akan wasu. Ta samu sukuni da salama na zuciya wanda bata taba tunanin zata samu a tattare dashi ba.

Rayuwar na tafiya cike da kalubale, wata rana farinciki wata rana kuma akasinsa. Sai aka wayi gari sun kasance kammalallun iyalai a waje guda. Bayan Fahima ta sake haihuwar Aisha, ta haifi Naseer, sai kuma Tameem da yake bibiyarta.
Wannan shekarar data raka maigidan nata kasar California inda suke kokarin bude kamfanin hadin gwiwa shi da wani abokinshi, ita kuma tana da kaso mai yawa na hannun jari, suka koma gida da tsarabar wani cikin.

Idan ta juya ta kalli rayuwarta ta baya, sau tari sai tayi murmushi tana girgiza kai kawai. Domin kuwa bata taba tunanin rayuwar tata haka zata kasance mata ba.

Idan ta tuno ranar da tayi niyar barin gida saboda zancen aurenta da AbdulMalik, da abinda ya wakana bayan nan. Sai ta samu kanta da godewa Allah da bai bata damar tafiya ba, ta kuma kara gode miShi da bai bata damar bijirewa umarnin iyaye ba, ta kuma sake godewa Anty Aisha da tayi dalilin da yasa ta koma gida a lokacin. Tunda duka da ba don su ba, da ba zata taba dandanar irin rayuwar da take yi a yanzu ba. Rayuwa tare da mijinta da iyalansu mai kyau da tsafta, wadda suke fatan dorewarta har gaban abada!!

‘Alhamdulillah! La Haula Wa La Quwwata Illa Billah!!’

<< Kauthar 25<< Kauthar 24

4 thoughts on “Kauthar 26”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×