Skip to content
Part 7 of 26 in the Series Kauthar by Jeeddah

“Na yarda, Aunty!”
Ita kanta a yadda maganar taje mata sai data sa ta dan yi dumm, tana jin kanta yana kara juyawa akan wadda yake yi a da. Tun daga lokacin data baro asibitinnan kwanaki uku da suka wuce, zuwa yanzu, kanta bai daina juyawa ba. Har ma ta fara tunanin watakila ya riga daya zame mata jiki.

Aunty Aisha ta daga kanta daga kan iPad din hannunta wadda take ta aikin lissafi da shigar da bayanai, tana jefawa Kauthar kallo mai cike da alamun neman karin bayani.

Idanu ta lumshe tana sosa saman goshinta,

“Ina nufin na amince da auren AbdulMalik, da sharadin bayan auren zaki taimaka min in samo mahaifiyata kamar yadda kika yi alkawari, kuma dukkan abinda zai biyo baya ba zaki sanya baki a ciki ba!”

Aunty Aisha wayar hannunta ta ajiye a gefenta, ta matsa inda Kauthar ke zaune ta kamo hannunta, fuskarta dauke da wani irin murmushi wanda ya bayyana zallan farinciki da murna da take a ciki, ta ce,

“In shaa Allah Kauthar, babu abinda zai biyo baya sai alkhairi. Na kuma yi miki alkawarin hakan! Sannan game da mahaifiyarki, ki kwantar da hankalinki, tuni na fara aiki akan haka nasan kuma nan da dan kankanin lokaci zamu ji labari mai dadi. Ke dai kawai ki kwantar da hankalinki, kiyi aiki mai kyau a jarabobin da suka rage miki. Auren AbdulMalik alkhairi ne in Allah Ya yarda!!”

Kai kawai ta girgiza mata, can kasan ranta kuwa tana fada tana nanata, ‘I doubt’, amma bata furta hakan a fili ba don bata so maganar tayi tsayi.
Ta lallaba ta tashi tsaye akan kafafunta da take jinsu kamar taliyar indomie data gama shan ruwa tayi laba-laba saboda sanyin da suka mata, ta fita daga dakin.
Tana fita Aunty Aisha ta janyo karamar wayarta ta dannawa Alhaji Abubakar Zannah waya ta sanar dashi halin da ake ciki, wanda a lokacin ma yana Algeria.

Mahmoud da Lukman suna falo suna kallon Teenage Mutants a tashar mbc 2, duk da son film din da take yi hakan bai sanyata kara kallon inda plasma din ma take ba saboda ji take yi komi ma ya fita a kanta.

Washegari Laraba zata zana last jarabawarta, amma koda ta baza tarin text books da handouts a gabanta, kasa fahimtar komi tayi. Ta zube a tsakiyar gadonta tayi dai-daya cikin pyjamas dinta na Mickie Mouse, ranar barci sai dai barawo.

Anty Aisha ta tasheta a barci washegari. Ta bude idanu da suka yi mata nauyi cikin magagin barci tana kallon Anty Aisha din. A shirye take tsaf cikin shirin fita kamar ba yanzu garin ya waye ba, karfe takwas da rabi lokacin.

Anty Aisha ta kalleta ta cikin farin gilashin fuskarta, “karfe nawa zaku gama exams dinku yau?”

Kauthar bata da tabbacin a inda tasan tana da jarabawa yau, amma tasan zata iya yiwuwa kawai hasashene irin nata.
Tayi yar mika, “Karfe biyu da rabi.”
Ta gyada kai, “good! Zan yiwa Abdul waya zai je ya daukoki idan kun gama, zai kaiki wajen awon kaya.”

Wani abu mai kama da zare taji yana mata yawo da filfilwa a ciki, duk sai taji ta rasa duk wani kuzari daya rage a jikinta. Kai kawai ta iya gyadawa.
Itama bata kara cewa komi ba ta juya ta bar dakin, ta bar Kauthar na shakar turarenta mai kamshi na Victoria Secret. Ranta cike da taraddadi da dana sani. Dama ta kame bakinta bata amincewa wannan aure ba!

*****

Abdul ya dauketa daga makaranta zuwa wani shagon dinki na zamani, bata zuwa wajen ba. Kodayake dama ina ta sani? Yawancin dinkunanta sai dai a kai mata su a dinkensu, dama can dinkin ba burgeta yake yi ba, ta fi ta’ammali da ready made din kaya da jallabiya.

Duk wani size dinta sai da aka auna, hakan yasa ta fara tunanin ko wani event na daban suke so suyi.
Ranta cike da wadannan tambayoyi suka juya gida.
Kai tsaye kuwa dakin Anty Aisha ta wuce, ko cikakkiyar sallama da Abdul bata samu sunyi ba. Tayi sa’a Anty Aisha din tana nan.

Cikin natsuwa da calmness ta mayar mata da amsar tambayarta, “babu wani event da za ayi Kauthar sai walima kawai, awon da aka yi miki duka na kayan da zaki sanya ne a gidan aurenki.”

Ta turo baki gaba, “Yo zaman yin kwalliya da gayu zan je inyi a gidan ko zaman aure?”
Anty Aisha dan murmushi kawai tayi tana girgiza kai, “Duka Kauthar!”

Ta daga baki zata sake watsa mata wata tambayar, tayi gaggawar katse ta, “Ina ce dai event ne baki so ayi saboda kada ku hadu da AbdulMalik? To kada ki damu, baya ma garin za ayi komi sai mun kaiki can gidanki sannan zaku hadu, don haka ki daina damun kanki. Kije ki samu ki huta don daga ganinki kin kwaso gajiya sosai!”

Bata iya cewa komi ba sai juyawa da tayi, a ranta tana fadin wani irin hutu kuma? Tana tunanin kila ita da samun hutu kam sun riga da sun raba gari tuni.

*****

Sauran kwanaki da suka biyo baya ta kasance kamar wata mutum-mutumi, Anty Aisha take ta shigi-da-fici game da bikin ita da sauran abokanta. Kauthar kam tana gefe sai dai a ce mata anyi kaza ko za ayi kaza, ita dai ido ne nata.

Tun washegarin ranar data gama jarabawa aka fara mata shiri irin na amare, korafinta a kullum shine, ‘meye ma na wani shiri ita da ba auren soyayya bane?’
Wata kawar Anty Aisha da suke cewa Sister Hadiza, ita take zama tayi ta kokarin fahimtar da ita muhimmancin aure irin wanda zata yi da muhimmancin gyaran jikin, wadanda duk kunnen shegu take yi dasu, Anty Aisha kam ko kokarin yin bayanin ma ta daina.

Kafin kuwa kace me! Tuni ta fara canza kamanni, idan ka kalleta sau daya ba zaka so ka dauke idanu daga kanta ba. Fatar nan tata tayi wani irin fresh da kyau, yanayin kalar fatarta ruwan cakuleti har wani sheki take yi da daukar idanu. Wai ma don tunani da taraddadi sun hanata tsayar da ranta a waje daya balle har tayi kyawun yadda yakamata.

Ranar Assabar ya zamana saura kwanaki shida daurin aure, aka kai mata tarin invitation cards. Lokacin da Mahmoud ya kai mata su, ta duba taga sun kai guda dari biyu, wani lalataccen murmushine ya subuce mata a fuska kawai, a ranta kuwa cewa take yi ina abokan da zata gayyata suke? Ko a yan makarantarsu wadanda suka san da zancen auren nata kalilan ne. Balle ma sun riga da sun rabu kowa ya nufi hanyar da tafi mishi.
Ta daga bedside drawer ta watsasu a ciki ta rufe, bata kara bi ta kansu ba.

Washegari suna zaune a falo da misalin karfe tara na safe ita da su Mahmoud suna karin safe saboda suma yaran sun samu hutun makaranta, taji wayarta tayi kara.

Bata yi mamakin ganin sunan Anty Aisha ba, don kuwa a yan kwanakin waya suke yi fiye da a kirga a rana.
Sai da kiran ya kusa katsewa sannan ta daga, Anty Aisha bata bari tayi sallama ba ta tare numfashinta,
Cewa tayi, “Kauthar, don Allah ki shiga dakin Daddy ki duba cikin lockers din office dinshi zaki ga wani purple din file, ki dauka ki kaiwa direbanshi yana waje yana jiranki!”

Kafin ma Kauthar din ta amsa mata da ‘to,’ ta katse wayar.
Wayar tabi da kallo tana kwafa tare da harararta kamar itace tayi mata laifin.

Sai data gama shan kamshinta sannan ta tashi tayi dakin Daddy. Dama can baya rufe dakinshi sam, don haka kai tsaye ta bude ta shiga dakin daya ware a matsayin study room inda yake gudanar da harkokin kasuwancinshi.
Kai tsaye ta hau dage-dage lokas tana dubawa har Allah Ya bata damar cin karo da abinda taje nema.

Caraf idanunta suka kai kan wata yar karamar jaka baka daga can karshen loka din, da alama ma an manta da wanzuwarta.
Bata sani ba ko instinct ne? Ta kai hannu ta dauko jakar, ta zuge.

Kakkausan gashin girarta da yake a cike da gashi da tsari kamar mutum ne yayi gyaran bayan kuma halittarsu ce a haka, suka daga cike da mamaki har suna kokarin hadewa da juna ganin tsohon SIM card irin tsohon yayi tun na farkon zamani, da wayar salula itama tsohuwa. Data kara bincikawa sai ta tsinto memory card da hoto da takardu a cukurkude da sauran kananun tarkace.
Kafin ta canza shawara ta maida jakar ta zuge ta sanyata cikin aljihun rigar jikinta. Jiki na rawa kafafu na hardewa, ta fita daga dakin.

Direba yana bakin kofa yana jiranta, tana bashi takardun ta juya da sauri. Bata kara komawa kan abincin ba, tunda dama ba wani ci take yi ba, ta haye sama zuwa dakinta da sauri ta maida kofa ta rufe harda murza makulli a jiki.

Ta sake janyo yar jakar ta bude ta bubbude abubuwan ciki. Sim Card din dai babu yadda za ayi ya hau kan waya dole sai an kara yankeshi, don haka ta ajiyeshi a gefe. Sauran tarkacen kuwa takardune, tana tunanin wasikune amma saboda tsakar ajiya kalmomin jiki basa rubutu sai yan tsilli-tsillin kalmomi da take tsinta wadanda basu kareta da komi ba sai kara cakuda mata kwanya, suma tayi gefe dasu.

Hoton kuma mutane uku ne ta gani da alamu abokan junane saboda yanayin yadda ta fahimci yadda suka dauki hoton, cikinsu kuma Daddynta kadai ta iya ganewa sauran bata sansu ba.
Ta zaro memory din ta sanya shi a card reader ta jona jikin laptop, babu jimawa ya hau kai ya fara loading. Cikin memory din folder daya ce kawai, ta hotuna.

Ta shiga ciki tana bi daya bayan daya tana dubawa, yawamcinsu wadannan mutanen uku ne, wasu lokacin taga mutum biyu; Daddy da daya daga cikinsu, ko duka ukun tare da karin wasu mutanen. Tana kokarin zare memory din a tunaninta ko ajiyar Daddy ce ta tsofin abokinshi, tayi saurin kara zooming hoton da take gani tana raba idanu tsakanin mutanen dake jikin hoton da sauri. Tabbas ta gane fuskar Mahaifiyarta, ta yaya zata iya mantata? Sai dai ba wannan bane abinda yafi daure mata kai, Da Daddy da Mommynta, da Anty Aisha da daya daga cikin abokan Daddy na hoton wannan, dogo, fari, mai dan kakkarfan jiki, shine abinda ya bata mamaki. Me yake faruwa ne? And why does the man look eerily familiar?

*****

Saura kwanaki uku da daurin aure Hajiya Hadiza ta karaso Najeriya daga Saudiyyah. Duk da cewa ba wani shiri suka cika yi ba, amma Kauthar taji tana kewar matar, ta kuma kasance cike da dokin son sake ganinta.
Wannan dalilin yasa tun da safe data tashi bata koma barci ba saboda karfe goma na safe jirginta zai sauka.

Misalin karfe takwas da kwata na safen ta sauka falon kasa, a shiryenta tsaf cikin pencil skirt maroon da farar shirt, sai ta dora kimono fara da ratsin maroon a kan kayan, da hula da flat din takalma suma maroon.

Su Mahmoud suna kan dinning shi da Lukman suna karin safe, taja kujera ta kusa da Mahmoud ta zauna, hannunta daya yana shafa sumar kan Lukman.

Duka yaran suka daga kai suna kallonta, a lokaci guda kuma suna gaishe da ita, “Adda ina kwana?”

Dan murmushi ya subuce mata, “lafiya lau my babies, ina sauran mutan gidan?”

Mahmoud yace, “Ammie yanzu ta shiga daki, Daddy kuma wai yaje Kaduna kila ma sai gobe zai dawo!”

Bata tsaya tambayar dalilin tafiyar tashi ba sai kai data jijjiga, ta hau bude warmers na musamman da tasan don ita aka tanada. Tuni aka cireta daga cikin layin abincin gidan, nasu ake yi musu daban, itama ayi mata nata daban.

Ajiyar zuciya ta dan saki a hankali ganin farfesun kayan ciki da wani lemun dabino da kwakwa da ake yi mata. Allah Ya gani har ta fara gajiyawa da cin kaza, don dai babu yadda zata yi ne da zubar dasu zata dinga yi.

Ta zuba farfesun a cikin bowl, wayar hannunta ta bude tana yan dube-dube tana cin abincin a nutse. Bata san lokacin da Lukman ya matsa inda take ba, sai ganinshi tayi yana kai lomar farfesu baki.
Ta janye da sauri tana dan harararshi, “Wai ba Anty tayi muku fadan taba mun abinci ba? Yanzu fa ka gama cin naka shine zaka dawo ta nan kawai cinye mun nawa?”

Yace, “Allah Adda naki yafi dadi sosai, kuma Mommy hanamu take yi mu ci!”

Murmushin mugunta ta sakar mishi, ta sanya cokali ta debo sauran daya rage, tayi kamar zata bashi a baki. Sai daya hangame bakin sannan ta juyar da cokalin zuwa bakinta ta taune tana mishi dariya.
Ya hau dira kafa, “Adda wannan ai mugunta ce kike yi mun!”.

Ita kuwa aikin dariya kawai take mishi, “Me na fada maka ranar nan? Dama ai sai da nace maka sai na rama,” ta karasa fada tana mishi gwalo. Kawai sai yaro ya bare baki ya hau surfa mata kuka.
Tun tana dariya tana tunanin tsokana ce, har dai taga abin da gaske yake. Sannan ne ta hau bashi hakuri dan shafa kanshi cikin lallashi. Jakarta ta zuge ta ciro cakuletin Alpenluebe ta bashi, Mahmoud ya mika hannu shima ta bashi, itama ta bare guda ta jefa a baki.

Kayan abincin ta ture gefe guda, ta ci gaba da scrolling a wayarta. Tayi mamakin adadin mutanen da suka dinga yi mata magana da korafin wai bata gayyacesu bikinta ba. Ta rasa ta ina suka san da zancen auren.
Yawanci kawai ce musu take yi suyi hakuri abin ne yaje mata kai tsaye shi yasa.

Tana nan zaune har Anty Aisha ta fito cikin wata koriyar atamfar super wax, ta dora gyale ruwan madara da wani takalmi mai dan tudu a kafarta shima ruwan madara.
Tana mamakin ta yadda aka yi matar tasan ainihin gayu da iya gyaran jiki. Idan wani ya ganta a yadda take dinnan zai iya rantsewa da Allah kan cewa ba ita ta haifi su Mahmoud ba.

Tayi nisa a cikin tunaninta da zancen zuci duk akan matar da take ki take kuma girmamawa a lokaci guda, har bata san lokacin da duk suka tashi ba.
Sai da suka kai bakin kofa sannan Anty Aisha ta juya tana watsa mata kallon tambaya, “Ba zaki je bane?!”

Sannan ta zabura da sauri ta tashi ta bi bayansu.
Anty Aisha din ce take tukin da kanta, Kauthar na gefenta su kuma su Lukman suna baya, ba wata hira suka dinga yi ba sai yan labarai jifa-jifa da sauraren radio har suka karasa airport din.
Babu jimawa suka tari Hajiya Hadiza, duk suka rungumeta cikin murna da farinciki da jin dadi. Bayan an gama gaisawa dai daga karshe suka dunguma zuwa gida.

Ita kuma. tsarabar kayan turaruka kawai ta yiwa Kauthar, masu kyau da kamshi da kama jiki. Tun ma a ranar aka fara yi mata turaren jiki dasu.
Shi yasa kafin zuwan ranar daurin aure tuni sun kama jikinta da kayanta. Ya zamana duk inda ta nufa sai ta bar kamshi, kafin kuma ka rasa inda take kamshin ne zai yi mata maraba tun daga nesa.

Abin kamar kiftawar ido, sai ga shi har ranar daurin auren tazo. Ranar juma’ah aka daura bayan an taso daga masallaci. Da tun a ranar ma za a tafi da ita amma aka bari sai washegari Assabar.

Asubahi ta gari! Matar Abdulmalik

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 2.9 / 5. Rating: 12

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kauthar 6Kauthar 8 >>

7 thoughts on “Kauthar 7”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×