Skip to content
Part 3 of 3 in the Series Kirkira by Bala Anas Babinlata

Rainon ƙirkira (Nuturing)

Dukkan ƙwararru a fagen ƙirƙira sun yarda cewa abu mafi muhimmanci ga ƙirƙira shi ne mutum ya kiyaye lafiyar jikinsa. Zai yi wuya a yi tunani mai kyau yayin da jiki yake a gajiye, hakan kan kawo cikas ga tunani mai kyau ya hana ƙirƙira gaba ɗaya.

Haka nan ya kamata hankalin mutum ma ya kasance lafiya. Ana cewa ma’abuta ƙirƙira na fama da mutanen ɓoye. An ce ma makarai ne ke basu gudunmawar yawancin ƙirƙire – ƙirƙiren nasu. Ba abin da nake nufi kenan da lafiyayyen hankali ba.

Lafiyayyen hankali ne ke iya samar da bayanan yau da kullum daga abubuwan da ke faruwa, ta hanyar karatu da tattaunawa.

Wanda ke haifar da kwararan tunani daga saƙe – saƙen zucin dake adane a cikin zuciya.
Sararawa wata hanya ce mai sanya nutsuwar hankalinka. Ta kan baiwa sabbin abin da zuciya ta samar damar cakuɗuwa da sauran bayanai. Yayin da mutum ke sararawa tunani kan zo masa kai tsaye. Mutane sukan sarara ta hanyoyi daban-daban: wasu ta hanyar wasannin motsa jiki, wasu yayin da suke yin wanka, wasu yayin tafiya mai tsawo, wasu yayin da suke tuƙin keke, wasu lokacin da suke yin zane – mutum zai iya zaɓar duk abin da yafi aiki a gare shi.

Sararawa na bayar da kyakkyawan sakamako wajen samar da nutsuwar hankali. Haka nan ƙwararru sun yi amanna cewa tana tallafawa fannin ƙirƙira.

Cafkar aidiya yayin da take ɓuɓɓuga

Lokacin da ake rainon abubuwan ƙirƙira, aidiyoyi na iya kwararowa ta kowane ɓangare. Yi shiri domin cafkar su a yayin da suka fara kwarara, ko kuma su ɓace har abada! Ma’abuta ƙirƙira kan yi yawo da kayan aiki iri daban-daban. Waɗanda suka haɗa da:

  • Ɗan littafin rubutu (notebook)
  • Ƙananan Kati (index cards)
  • Ƙaramar rikoda
  • Wayar hannu
  • “ Kashi Casa’in bisa ɗari na kowane abu Gurɓatacce ne.”

Theodore Sturgeon

Bitar musamman

Bitar musamman ta ƙunshi rarrabe wa tsakanin aidiyoyi masu kyau da marasa kyau. Kamar yadda maimai ke inganta shuka. Bitar musamman kan adana mafi kyawun aidiyoyin mutum kuma ta inganta su gaba ɗaya. Bitar musamman wani babban ɓangare ne mai zaman kansa a fagen ƙirƙira. Ba a yin bitar musamman sai bayan an kammala samar da Aidiyoyi (ko a ƙallla an haɓaka aidiyoyin zuwa wani mataki). Ba a yin bitar musamman a lokacin da ake zafafa tunani, wato brainstorming ko literal thinking domin yakan yanke kwararar aidiyoyi. Akan kira bitar musamman da “tacewa,” “daidaitawa,” ko “murzawa,” da dai sauransu, ya danganta da sana’ar mutum. Sai dai duk ma’anar su ɗaya ce.

Yawancin mutane bitar musamman kan wahalar da su, saboda suna shan wahala wajen watsar da wani abu da suka ƙirƙira. Wasunsu na ganin idan suka watsar da abin da suka ƙirƙira to tamkar fa sun ɓata lokacinsu ne a banza a wofi. Dukannin zaton biyu ba daidai ba ne kuma sun saba wa tsarin ƙirƙira.

Dokar Sturgeon

Abu na farko da ya kamata mutum ya yarda shi ne yawancin Aidiyoyi shiririta ne. Hatta shahararrun ma’abuta ƙirƙira sun yarda da haka.

Akwai wata sananniyar magana da Theodore Sturgeon, marubucin littattafan kimiyya na Almara ya yi, in da yake cewa, “Kashi casa’in bisa ɗari na labaran almarar kimiyya gurɓatattu ne. Me ya sa? Saboda kashi casa’in bisa dari na kowane aikin ƙirƙira Gurɓatacce ne. Wanda daga bisani ake kiransa da Dokar Sturgeon. Har yanzu ana ƙaddarawa, “Kashi casa’in bisa dari na kowane abu, gurɓatacce ne.”

Akwai sahihanci sosai game da wannan Dokar ta Sturgeon. Wasu ma na ganin kamar kashi casa’in bisa dari babu makawa shi ne ma’aunin.

Tun da yawancin aidiyoyi ba su da inganci ballantana a haɓaka su, don haka ya zama babu makawa kenan ko dai a yi watsi da su ko kuma a sauya musu fasali.

Ba abin kunya ba ne don an soki aikin mutum. Abubuwa da dama kan iya canzawa, daga ƙarshe ka ga an fitar da ingantaccen aiki mai nagarta daga ainihin aikin da mutum ya fara ƙirƙira.

Matakan bitar musamman

Akwai matakai uku na Bitar Musamman. Mataki na farko ya haɗa da gama-garin gyare-gyare kamar gyaran kurakurai na bayyane, misali gyaran ka’idodin rubutu. Da daidaitawa da shigar da muhimman bayanai da aka manta yayin rubutu.

Mataki na biyu ya ƙunshi watsar da abubuwan da ba su da amfani ko abin da Sturgeon ya kira gurɓatattu, abin da wasu suka kira cikin hikima “tarkace”

Sai mataki na uku wanda yake mafi rikitarwa shi ne haɗa aidiyoyi biyu marasa amfani domin ƙirƙirar Aidiya ɗaya ƙwaƙƙwara.
A nan ne ainihin abin al’ajabin ke faruwa. Masu amfani da ɓangaren kwakwalwar dama kan yi wannan cikin sauƙi, saboda yanayin tunaninsu na gaba-gaɗi.

Masu tunani da ɓangaren hagu na ƙwaƙwalwarsu kuwa sukan samu matsala sosai saboda tsayawa da suke yi neman wasu rubutattun ka’idoji da zasu bi. Wanda hakan ke wahalar dasu wajen sarrafa gurɓatattun aidiyoyi domin samar da wani abin kirki daga jikin su.

Satar amsa

Zan baku ‘yar wata satar amsa a nan:

Akwai wata Tsohuwar magana da masu hikima suka jima suna faɗi, “idan kana shakka akan kowane abu, jefar ka huta,” a nan za a ce hakan gaskiya ne. Domin zai sanya aikinka ya zamo mai tsabta da ƙarancin kurakurai muddin ka yasar da duk abin da kake da kokwanto a kansa.

Waɗannan fasahohin zasu taimaka maka:
1. Kasancewa Mai Tsage Gaskiya – Mutum ba zai taɓa yin nasara ba sai ya zama mai tsage gaskiya a kan aikinsa da ya yi da hannunsa. Sai dai kuma Kash! Yana da wuya matuƙa mu kawar da girman kai, mu amince mu watsar da abin da muka ƙirƙira a cikin ruwan sanyi. Sai mutum ya yi namijin ƙoƙari yake iya koyon daina dagiya da kariya ga duk abin da ya ƙirƙira.

2. Nisanta Kanka Daga Ayyukanka – Sau tari duba aikin wani yafi sauƙi akan ka duba aikinka da kanka. Aikin ka ma zaka iya yi masa haka, ta hanyar bayar da tazara tsakanin lokacin da ka ƙirƙiri aikin da kuma lokacin da zaka yi bitar aikin naka. Misali bayan ka gama rubutun ka sai ka ajiye shi zuwa mako ɗaya zuwa wata ɗaya ko ma fiye kafin ka sake duba aikin. Hakan yakan mayar da aikin baƙo a gare ka, ya baka damar yin gyara ba tare da ji a ranka cewa aikinka kake rusawa ba.

3. Saurarar “Kokwanto” – A duk lokacin da mutum ya ji zuciyarsa na raya masa wani abu game da aikinsa, to yana da muhimmanci mutum ya zauna ya yi nazari na musamman a kan abin da yake kokwanto ɗin. Waɗannan irin tunanin, ko kokwanton, zuciyar ka ce ke raya maka cewar lallai fa akwai matsala a wani sashe na aikin ka. Yawanci wannan kokwanton manuniya ce dake tabbatar maka akwai matsala ta gaske a aikinka.

4. Kalli komai da zuciya ɗaya – Yi ƙoƙarin kallon abubuwa ba tare da nifaƙa ko tunani irin na al’ada ba. Kaucewa duk wata Aidiya da ta yi gangan da yawa, musamman wadda almarar dake cikin ta har ta shallake hankali.

Habɓaka aidiyoyi

Bayan samar da aidiyoyi ta hanyar zafafa tunani wato (brainstorm) da kuma yin amfani da tunani a Kaikaice wato (Literal thinking) daga nan sai ƙoƙarin haɓaka aidiyoyin don ƙirƙirar aikin da ake shirin samarwa. Kowace sana’a suna da hanyar da suke bi wajen samar da aiyukansu: Mai sana’ar sassaƙa yakan fiƙe ko ya wasa kayan aikinsa; mai bincike zai yi gwaji irin na (experiment) domin ya tabbatar da bincikensa (theories); mai daukar hoto ya tanadi abubuwan ɗaukar hoto mafi dacewa da fitilu da sauran kayan sarrafa haske don samar da ingantaccen hoto.

Duk da kowace sana’a na amfani da kayan aiki mabanbanta, amma tsarin haɓaka aidiyoyi duk salon iri ɗaya ne. Ƙirƙira na taka muhimmiyar rawa saboda haka za a yi ta cin karo da matsalolin da ke buƙatar dabaru na musamman.

Akwai dabaru biyu masu ƙarfi da ake amfani dasu don haɓaka aidiyoyi: dabarun su ne Pre-visualizing da gestation. Ayyana wa a zuci da kuma ƙyanƙyashe wa:

Ayyanawa a zuci (Pre-visualisations)

Pre-visualizing shi ne tunanin aiki tun kafin a yi aikin azahiri. Misali, idan kai mai daukar hoto ne, za ka yi ta gwada yadda hasken wajen zai kasance a ƙwaƙwalwarka, shin waɗanne irin fitilu da kayan aiki zaka yi amfani da su don samar da abin da kake nema. Haka nan idan kai marubuci ne, za ka yi nazari ne ta hanyar wasa ƙwaƙwalwa tun kafin ka ɗora biro a takarda.

Mazanin Gini, Frank Lloyd Wright yana cewa yayin da ya zauna zai yi aiki, kai tsaye yana zama ne don ya yi zane, ba wai zama tunanin yadda zai ƙirƙiri zane ba. Me ya sa? Saboda tuni ya gama ayyana me zai zana a ƙwaƙwalwarsa tun kafin ya zauna zaman zanen duk gidan da zai zana.

Alfred Hitchcock, Shahararren Daraktan Fim na Hollywood, shi ma ya bayyana irin wannan ra’ayin lokacin da ya ce: ɗaukar fim abu ne mai cin rai, saboda tuni ya riga ya gama ƙuƙƙulla fim din a cikin kwanyarsa. Waɗannan Jagororin suna bayyana mahimmancin sas-saƙa abu da ayyana shi a cikin ƙwaƙwalwa tun kafin lokacin yinsa na da matuƙar amfani a tsarin ƙirƙira.

Pre-visualization yana ba ka damar ka ƙirƙiri aiki cikin sauri da inganci.

Kamar wata hanya ce ta horar da kai, ta yadda mutum zai kammala aikin tun kafin zuwan ranar yin aikin.

Ba lallai ne ku fahimta ba, amma gwada yin abu ta hanyar ayyana shi a zuci, ya fi sauƙi a kan gwada shi da jiki, wato a zahiri, fiye da yadda kuke zato. Sakamakon zai ba ka mamaki.

Ba a yin (pre-visualizing) daf da lokacin da za a fara yin aikin, ana yin sa ne wasu ‘yan sa’o’I ko kwanaki kafin yin aikin. Idan so samu ne ma a ɗan maimaita shi da yawa kafin lokacin fara aikin.

Hakan zai baiwa ƙwaƙwalwa damar ta haddace matakan, ta ma iya faɗaɗa aidiyoyin. Haka nan ta iya hango matsaloli da hanyoyin da zata samar da mafita ga matsalolin.

Yawa-yawan ma’abuta kirkira suna yin Pre-visualizing ba tare da sun san shi suke yi ba. Pre-visualizing na tafiya ne hannu da hannu tare da Ƙyanƙyasar Aidiyoyi. Wato (Gestation).

Gestation yana warware matsaloli ne ta hanyar amfani da sabkwanshos. A yayin Gestation, keɓantattun aidiyoyi na haɗuwa da wasu aidiyoyin domin haifar da sabbin aidiyoyi.

Ita ce hanyar da masu ƙarancin shekaru ke amfani da ita wajen koyo. Hatta manya suna amfani da Gestation wajen warware matsalolinsu. Ko da yake ba lallai ne su gane Gestation suke yi ba, saboda Gestation salo ne mai sauƙin sajewa.

Hanyar da ake yin Gestation ita ce: mutum zai tattauna aidiya ko wata matsala dake damunsa a zuciyarsa, daga nan sai ya bari sai bayan kwana ɗaya ko fiye. Lokacin da mutum ya waiwayi abin zai tarar kusan komai ya warware ba tare da wani takura kai ba.

Wani lokaci abin yakan zo wa mutum da ilhami ta yadda zai ji shauƙin aiki ma ya zo masa.

Sirrin Gestation shi ne bai son gaggawa. Babu aibu idan mutum ya ƙaddara a ransa cewa ina yin aiki a kan wannan matsalar, amma dai kada a takurawa kai ko a sanya damuwa a kan abin, sanya damuwa kan kore Gestation.

Bayan ka zayyana matsala, zaka iya taimakawa Gestation ta hanyar kaɗaita kanka wajen yin wani abun dabam ko sararawa. Kamar mutum ya yi wata ‘yar doguwar tafiya a ƙafa ko tuƙa keke ko wanka da ruwa mai ɗan ɗumi, ko ƙailula—mutum na da damar ya zaɓi abin da ya fi so. Shakatawa na sanya ruhi nutsuwa har mutum ya ji yana sha’awar ya cigaba da aiki.

Gestation tsari ne mai ƙarfi, amma fa sai mutum ya yi amanna da tsarin kafin ya ga tasirinsa.

Zafafa Tunani (brainstorming) ko Gestation?
Zafafa Tunani (Brainstorming) da gestation Dukansu sukan shiga sabkwanshos, amma fa sukan yi hakan ta hanyoyi dabam – dabam.
Zafafa Tunani (brainstorming) ya kan afku ne cikin sauri tamkar walƙiya, yayin da gestation ke ɗaukar lokaci kafin a samu sakamako. Ana amfani da hanyoyi biyu a bisa dalilai mabanbanta.

Ana amfani da Zafafa Tunani (brainstorming) don samar da sababbin Aidiyoyi, yayin da ake amfani da gestation don faɗaɗa aidiyoyin da warware matsalolin dake tare da Aidiyoyin.

Sharhin manazarta

Sharnin manazarta ya kan taimaka wajen inganta aiki ta hanyar baiwa aikin wasu mahangai da hankalin mutum bai taɓa kai kan su ba.

Shawarwarin mutane zai nusar da kai ƙarin wasu gyaran, ya bayyana maka abubuwan da ka manta ya kuma nuna maka kurakuran da hankalinka bai kai kansu ba.

Yana da muhimmanci gyara ya fito daga mutanen da za su iya tantance aikinka bil haƙƙi, da gaskiya, misali, takwarorinka a rubutu.

Nau’o’in manazarta

Nau’o’in Manazarta uku ne:

  1. Akwai waɗanda ke iya gano matsala game da aikinka, amma ba za su iya faɗar ainihin mece ce matsalar ba.

2. Sannan sai waɗanda ke kallon aikinka daga mahangarsu maimakon su kalla daga mahangarka.

3. Sai kuma waɗanda ke iya gano matsalolin aikinka kai tsaye ta mahangarka. Wato waɗanda sun gane in da ka dosa da aikinka, kuma ta wannan fuskar suke bayar da tsokaci ga aikin.

Wannan nau’in na ƙarshe su ne KADARA, haka nan suna da wuyar samu.

Tsokaci abu ne mai ƙona rai, zai ma iya sage maka guiwa saboda yawancin mutane ba su iya bayar da shi ba.

Yawancin shawarwarin idan aka tattara su zaka same su basu da wata cikakkiyar alƙibla. Sai dai duk da haka, ba za a rasa ɗan inganci game da wasu maganganun ba, musamman idan ka san yadda ake rarrabe bayanai.

Tattara tsokaci (Gleaning criticism)

Yawancin manazarta, kyakkyawan nazari ko mummuna, mutane ne masu ƙoƙarin fadar gaskiya. Idan ka ji manazarci ya ambaci matsala to tabbas ya lura ne an rasa wani abu muhimmi a aikin. Aikinka shi ne ka gano wanne abu ne manazarcin ke magana a kai. Wannan takan faru har ga sukan rashin adalci. Ga wasu daga cikin manuniyar hakan:

1. Gano Alamomi – wannan hanyar na ɗaya daga cikin dabarun da ake bi don ragewa aiki rauni. Wato ƙoƙarin gano alamomi da kamanceceniya a shawarwarin da manazarta dabam dabam suka gabatar. Wannan yana buƙatar nutsuwa saboda manazartan zasu iya bayar da shawara a kan matsala iri ɗaya amma ta fuskoki dabam dabam.

2. Yawaita tambaya – Yawancin manazarta kwararru ne wajen gano matsala, amma sukan kasa yin cikakken bayanin da zaka iya fahimta. Saboda haka ka yi musu tambayoyi masu yawa domin gano ainihin mece ce matsalar. Ka ƙaddara a ranka kai ne ƙwararre akan aikinka, ba manazarci ba.

3. Kada ka ɗauki tsokaci a matsayin ƙiyayya – Hanya ɗaya da zaka inganta aikinka ita ce ka yiwa aikin adalci ta hanyar karɓar gyararrrakin da aka yi maka. Kamar yadda muka tattauna a baya, yana da muhimmanci ka nisanta kanka daga aikinka ta hanyar bayar da ɗan lokaci tsakanin ƙirƙirar aikin da nazarin aikin.

4. Kada ka dage wajen kare Aikinka – saboda dagiyar kare aiki alama ce ta rashin ƙwarewa, haka nan ita ke kassara manufar bayar da tsokaci. Ta kan sage gwiwar manazarta wajen fito da gaskiyar lamari, ɗari bisa ɗari. Lokacin kaɗai da ya kamata ka yi bayani shi ne idan ka lura manazarci ya kasa fahimtar aikin sosai. Duk da haka, in da hali yana da muhimmanci a guji bayyana komai.

Bita (Revision)

Bayan an gama gyara akwai buƙatar sake bibiyar aikin.

A fagen rubutu ana kiransa Bita, manufar ta shafi dukkan wani yunƙuri na ƙirƙira.
Bita na afkuwa lokacin da gyararrraki suka rage ƙimar aikin. Saboda haka akwai buƙatar sake gina aikin.

Duk da yawan gyare-gyaren yana iya zama maras amfani, amma a zahiri yakan haifar da ingantaccen aiki.

Ƙananan gutsire-gutsire, da jirkice-jirkice, da goge-goge, da ragi da ƙari yakan inganta aikin, daga ƙarshe ya haifar da aikin da ya sha bambam da na farko a kyau da inganci. Sau da yawa, Bita kan buƙaci ƙarin zafafa tunani, da gestation, da sake zama don haɓaka aidiyoyi. Ba lallai ne a bi tsarin daki-daki ba. Yana da kyau ka bi wuraren da aka bayar da gyararrraki a jere ka gyara su. Bita ta ƙare idan babu sauran wani abu da za a ƙara taɓawa ko gyarawa a cikin gundarin aikin.
Wannan matakin na nazari shi ne mataki mafi girma da ke taimakon aikin ƙirƙira, amma rashin fahimta ya sanya yawa yawan mutane ba sa maraba da shi. Yawancin ma’abuta ƙirƙira musamman marubuta suna kuskuren kallon manazarci a matsayin abokin adawar aikinsu. A zahirin gaskiya idan babu manazarta rubutu baya samun balagar da ya kamata ya samu.

Toshewar basira

Dukkan ma’abuta kirkira kan fuskanci toshewar basira ta hanyoyi dabam dabam. Wannan ya haɗa da ƙananan matsaloli irin gaza yin tunani na wucingadi har ya zuwa babbar toshewar basira, wato mutum ya gaza samar da tubalan ƙirƙira:

Watsarwa yayin da aiki ya dauki zafi

Wasu mutanen na da dabi’ar watsar da aikinsu yayin da aikin ya kai wata ƙololuwa.
Alamar irin wannan matsalar ita ce a ko da yaushe mutum ya ƙare cikin yin ‘yan guntayen aiyuka. Ko da yake irin waɗannan mutanen kan gamsu da yanayin aikin nasu a matakin Sabkwanshos, amma ganewa ne kawai basu yi ba, suna fargabar rashin sanin yadda zasu iya haɓaka aikin nasu ne. Ta wani ƙaulin ma za a iya cewa suna gujewa aikin nasu ne da rana tsaka. Wannan gurguwar dabara ce, saboda alamu na nuna har yanzu suna da abin rubutawa in da zasu mayar da hankali su cigaba da aikin.

Tamkar mutum ya gudu daga aiki ne da rana tsaka. A tsohon tsarin wasan dambe mai zagaye goma sha biyar, zagaye na 13 zuwa ƙarshe shi ake kira “zagayen zakaru.” A wannan gaɓar ce ake gane ɗan dambe na ƙwarai, ‘yan dambe masu juriya kaɗai ke iya kai labari. A duk lokacin da kake ganiyar ƙirƙira ka ji zuciyarka na raya maka cewa ka tsaya, to kamar kana zagaye na 13 ne irin na ‘yan dambe, ka ci karo da bangon jimiri a fagen ƙirƙira, wato yanzu kana cikin zagayen zakaru. Dole ka tilasta kanka ka ci gaba har sai ka iya kaiwa ƙarshe. Domin mafi kyawun aidiyoyin ka ma basu ma fara ɓuɓɓugowa ba!

Gaza rike wuta

Wasu mutanen kan gaza ɗorawa daga in da suka tsaya a aikinsu na baya.

To, akwai dabarun da ake amfani da su don warware irin waɗannan matsalolin:
Ɗabi’ar Barin Saura – Tabbatar a ko da yaushe kana barin giɓi a ƙarshen aikinka, wato ka rinƙa ƙarewa da wani abu da za a rinƙa biyo ka bashi. Alabasshi sai sabon babi ko sabon scene ya fara daga in da aka biyo ka bashin. Misali wasu marubutan sukan ƙare suna tsaka da rubutu, wato ba sai sun kai ƙarshen jimla ba.

Jera “Abubuwan Yi” – rubuta bayanan abubuwan da kake so ka yi a gaba ta hanyar tambayar kanka ko gayawa kanka abubuwan da kake so ka yi idan ka dawo zaka cigaba da rubutu. Yin haka zai riƙe maka karsashin aikinka duk lokacin da ka dawo zaka cigaba. Kada ka cunkusa abubuwa da yawa. Idan suka yi yawa zasu iya sanya ka ganda!

Ƙirƙiri Jadawali – Yi aiki da jadawali don sanin iya me zaka yi a duk zama. Yin hakan zai ɗora mutum a kan tsari, sai dai ya kamata a kiyaye, a yi aikin cikin ‘yanci kada ya zama ci-da-ƙarfi. Don gudun kada aikin ya zama kamar an bi shi daki – daki, mutum zai iya jujjuya jadawalin ya maida shi Kwan-gaba Kwan-baya. Jadawalin tamkar jagora ne, a ko da yaushe mutum zai iya komawa gare shi idan buƙatar hakan ta taso.

Snags

Mafita ita ce mutum ya jingine aikin ya huta kawai, ko ta hanyar sararawa ko mutum ya fita ya yi ‘yar doguwar tafiya a ƙasa. Idan ɗan gajeren hutu ya gaza wadatarwa, to lallai akwai buƙatar dogon hutu. Zai fi kyau mutum ya haƙura ya jingine aikin, alabasshi ya cigaba a lokacin da ya samu nutsuwa.

Lokacin da mutum ya dawo zai ci gaba da aikin, zai ga komai ya zo masa cikin sauƙi. Haka tsarin ƙirƙira yake. Kuskuren da mutum zai yi shi ne ya tilasta kansa dole sai ya yi aiki a lokacin da babu shauƙin aikin a ransa. Wanda a ƙarshe mutum ya yi aikin babu inganci ta yadda dole daga bisani sai ya dawo ya warware lokacin da hankalinsa ya dawo jikinsa.

Blocks

Yayin da snags suke ‘yan ƙananan alhaki a cikin matsaloli, matsalar blocks ta fi girma ainun. Toshewar basirar da ake kira Creative Block na faruwa ne yayin da sha’awar ƙirƙirar sababbi da ƙayatattun aidiyoyi ta gushe daga ran mutum.

Toshewar basira, kan faru a kowane fage na ƙirƙira kuma ga kowace irin sana’a. Akwai abubuwan la’akari guda biyu lokacin da ake fuskantar toshewar basira.

Na farko, zai iya kasancewa sakamakon azabtar da kai da yawan aiki ko sanya damuwa a rai; na biyu, zai iya zama wani abu na wucingadi, wato (temporary).

Yana da mahimmanci mutum ya cire damuwa a ransa, domin damuwa na sanya al’amura su taɓarɓare ne.

A gaskiya ma, damuwa a kan ƙaramar toshewar basira na iya haifar da babbar toshewar basira, zata iya karyawa mutum zuciya har ya soma ji a ransa babu wata hanya da zai iya warware kowace irin matsala da ta taso masa.

Akwai hanyoyi da dama da mutum zai iya bi don warware matsalar toshewar basira.
Na farko, dole ne ka guji takurawa kanka. Idan hakan na nufin tsawaita hutun aiki, to babu makawa abin da ya dace kawai ka yi ɗin kenan.

Abu na gaba kuma, Sai ka bincika don gano mene ne tushen matsalar sannan ka ɗauki matakan gyara. Misali, idan kana yin aikin da ya wuce kima ne, to sai ka gyara jadawalin aikinka yadda zaka samu sassauci. Idan kuma ka galabaita ne gaba ɗaya, to Hutu zai iya zama mafitar da zata iya warware matsalar ka. Wasu na ganin sauya wa zuwa wani matakin kan iya warware matsalar. Misali idan kana matakin rubutu sai basirar ka ta toshe, to kawai ka ƙyale rubutun ka tsallaka ya zuwa bita ta iya aikin da ka riga ka kammala. Wataƙila sabon matakin ya sanya ka hango matsalar da ta sa ka kasa cigaba da aikin.

Sai abu na ƙarshe, amincewa cewa tsarin ƙirƙira – yana aiki!

Kammalawa

Wannan littafi an tanade shi ne domin ya zaburar da mutum a yunƙurinsa na ƙirƙira. Wato an ƙirƙiri littafin ne don ya farfaɗo da ƙirƙirar duk mutumin dake da burin ya farfaɗo da ƙirƙirarsa. Tsarin na iya zama kamar mai wuya da farko. Yana da wahala mutum ya bar daɗaɗɗiyar ɗabi’arsa, musamman ta ɗanfarewa tunanin hagu ko dama na ƙwaƙwalwa. Muddin ka amince da tsarin! To, aidiyoyi za su rinƙa zuwar maka cikin sauƙi, za kuma ka san abin da ya dace ka yi da Aidiyoyin a duk lokacin da suka zo. Yawaita amfani da waɗannan ƙa’idodin zai sanya ƙirƙirar ka ta faɗaɗa cikin ƙanƙanin lokaci.

Wannan shi ne ƙarshen wannan ɗan littafi mai suna Ƙirƙira. Da fatan kun amfana da abin da ya ƙunsa nake ce muku Assalamu alaikum.

Bala Anas Babinlata

<< Kirkira 2

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.